• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Shettima ya halarci ɗaurin aurarraki a Kaduna

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
January 31, 2026
in Labarai
A A
0
Shettima ya halarci ɗaurin aurarraki a Kaduna
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, tare da Gwamna Uba Sani da sauran mahalarta a wurin ɗaurin aurarrakin a Masallacin Sarkin Musulmi Bello, a Kaduna a yau

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, tare da Gwamna Uba Sani da sauran mahalarta a wurin ɗaurin aurarrakin a Masallacin Sarkin Musulmi Bello, a Kaduna a yau

A safiyar yau Asabar a Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya halarci ɗaurin auren Nadiya Abba Dasuƙi, ‘yar Abba Dasuƙi, Durɓin Sakkwato, da Baffa Salihi Abdullahi, wanda aka gudanar a tsohon Masallacin Juma’a na Sultan Bello.

Shettima ya tsaya a matsayin waliyyin amarya, inda ya ba da Nadiya auren ga iyalan ango.

Shi kuma Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Mohammed Ɗalhatu, shi ne wakilin ango.

Bikin ya samu halartar ‘yan’uwa da abokan arziki, malamai da manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Alhaji Kashim Shettima, Alhaji Uba Sani, da sauran manyan baƙi a wajen taron

Daga cikin mahalarta akwai Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani; tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Mohammed Namadi Sambo; Minista, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi; Sanata Bala Ibn Na’Allah; tsohon mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan tsaron ƙasa (NSA), Sambo Dasuki; Shugaban JIBWIS na ƙasa, Sheikh Bala Lau; Sheikh Ahmad Gumi, tare da sauran manyan jami’an gwamnati, dattawa masu daraja, masu riƙe da sarautun gargajiya, ‘yan kasuwa, da malaman addini.

A wannan wuri kuma, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya halarci wani ɗaurin auren na daban da ya shafi gidan Sanata Bala Ibn Na’Allah, inda aka ɗaura auren ɗan’uwan sa, Ishaq Sa’idu Wasagu, ɗan marigayi Sarkin Wasagu, Muhammad Tanko, da Habiba Aliyu Datsama (Ummi), ‘yar DCM Aliyu Bawa Datsama.

Shettima ya yi roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya albarkaci aurarrakin biyun, Ya ba ma’auratan zaman lafiya da fahimtar juna, kuma Ya sanya gidajen su su zama ginshiƙan kwanciyar hankali, dauwamammiyar albarka, da zaman lafiya.

Shettima yana addu’a ga ma’auratan
Tags: DasuƙiKashimShettimaɗaurinaure
Previous Post

Isar da saƙon gwamnati iri ɗaya shi ne ginshiƙin dawo da yarda daga jama’a — Minista

Next Post

Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe babban kwamandan ISWAP a Arewa-maso-gabas

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe babban kwamandan ISWAP a Arewa-maso-gabas

Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe babban kwamandan ISWAP a Arewa-maso-gabas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!