Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa yana daga cikin manyan jami’an da aka sanya a gaba domin a kai musu hari a wani shirin juyin mulki da aka yi yunƙurin aiwatarwa kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ya ce masu shirya shirin sun ƙudiri aniyar kama shi tare da harbe shi idan ya yi wata turjiya.
Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin “Sunday Politics” na gidan talbijin na Channels, kwanaki kaɗan bayan sojoji sun tabbatar da cewa wasu daga cikin jami’ai 16 da aka kama a watan Oktoba 2025 za a gurfanar da su bisa zargin shirya kifar da Gwamnatin Tarayya.
Ministan Tsaron, wanda shi ne tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa (CDS), ya ce masu shirin juyin mulkin sun ayyana wasu manyan jami’an gwamnati domin a kawar da su, ciki har da shi kan sa.
“Ni ma an sanya ni a gaba, ina da tabbacin kun sani,” inji Musa a hirar. “An shirya a kama ni, kuma idan na ƙi, an shirya a harbe ni.”
A Oktoba 2025 ne dai hukumar sojoji ta ba da sanarwar an kama jami’ai 16, inda suka bayyana zargin da ake yi musu a matsayin rashin ɗa’a da kuma karya ƙa’idojin aikin soja. A wancan lokaci, Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa ta musanta rahotannin da ke danganta kamen da shirin juyin mulki, tana mai cewa binciken cikin gida ne na ladabtarwa.
Sai dai a makon da ya gabata, hukumar ta janye matsayin ta na farko.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Sama’ila Uba, ya fitar, Rundunar Sojin ta tabbatar da cewa bincike ya gano shaidu da ke nuna cewa wasu daga cikin jami’an da aka tsare suna da hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu.
“Abubuwan da aka gano sun nuna cewa akwai jami’ai da ake zargi da shirya kifar da gwamnati, abin da ya saɓa wa ɗabi’u, ƙimomi da ƙa’idojin ƙwarewa da ake buƙata daga membobin Rundunar Sojin Nijeriya,” inji Uba.
Ya ƙara da cewa jami’an da aka tabbatar suna da amsar tuhuma za a gurfanar da su a gaban kotunan soja da suka dace, bisa tanadin Dokar Rundunar Sojin Ƙasa da sauran ƙa’idojin aiki.
A cewar majiyoyin tsaro, an rubuta sunayen wasu manyan jami’an gwamnati da fitattun ‘yan ƙasa domin kama su ko kawar da su a matsayin wani ɓangare na shirin juyin mulkin.
Rahotanni sun kuma alaƙanta yunƙurin juyin mulkin da soke bikin zagayowar Ranar ‘Yancin Kai ta 65, wani mataki da ba a saba gani ba wanda ya janyo hasashe a tsakanin jama’a a wancan lokaci.
Tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, shi ma ya shiga cikin ce-ce-ku-ce bayan jami’an tsaro sun kai samame gidan sa da ke Abuja dangane da zargin shirin. Sylva ya musanta duk wani hannu da aka ce yana da shi a shirin.
Da yake ci gaba da magana, Janar Musa ya soki masu shirin juyin mulkin, yana kiran su da marasa hankali, kuma masu buri marasa tushe.
“Ina ganin waɗannan mutane wasu ne marasa muhimmanci,” inji shi. “Idan ka duba irin mutanen da ke ciki, ban san abin da ya shiga kawunan su ba har suka yi tunanin za su iya ƙalubalantar Rundunar Sojin Ƙasa ta haka.”
Ministan ya jaddada cewa al’ummar Nijeriya da kan su sun ƙi duk wani yunƙuri na kifar da gwamnati ta dimokiraɗiyya.
“Ko ‘yan Nijeriya da kan su da sun yaƙe su,” inji Musa. “Nijeriya ta daɗe tana gwagwarmaya da mulkin soja. Shugaban Ƙasa kan sa yana cikin wannan gwagwarmayar.
“Duk wanda ya farka wata safiya ya yi tunanin zai iya yin irin wannan abu a Nijeriya, to lallai yana buƙatar ya sake daidaita tunanin sa.”
Nijeriya dai tana da dogon tarihi na juyin mulkin soja, musamman tsakanin shekarun 1966 zuwa 1993, wanda lokaci ne da ya kasance cike da tsoma bakin sojoji cikin harkokin mulki.
Ƙasar nan ta koma mulkin farar hula a shekarar 1999, kuma tun daga lokacin take ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya ba tare da yankewa ba.







