• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ribadu da Uba Sani sun jajanta wa El-Rufai kan rasuwar mahaifiyar sa

Fati Abdul by Fati Abdul
March 27, 2026
in Labarai
A A
0
Ribadu da Uba Sani sun jajanta wa El-Rufai kan rasuwar mahaifiyar sa
Marigayiya Hajiya Umma El-Rufai

Marigayiya Hajiya Umma El-Rufai

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jajanta wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, bisa rasuwar mahaifiyar sa, Hajiya Umma.

Ribaɗu ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Na yi matuƙar jimami da jin rasuwar Hajiya Umma El-Rufai, uwar iyalan El-Rufai. Ina da kyawawan tunani na lokutan da muka yi tare da ita da kuma kulawar ta irin ta uwa.

“A irin wannan lokaci, kalmomi ba sa iya bayar da cikakken ta’aziyya kan irin wannan babban rashi. Ina miƙa ta’aziyya ta har zuci ga Mallam Nasir El-Rufai da ɗaukacin iyalan sa. Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta mata kurakuran ta, ya ba ta hutu na har abada a Aljannar Firdausi, kuma ya ba iyalan ƙarfin jure wannan rashi.”

Shi ma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya aika da saƙon ta’aziyya ga iyalan El-Rufai.

Ya ce: “A madadin Gwamnati da al’ummar Jihar Kaduna, ina miƙa matuƙar ta’aziyya ta ga Mai Girma, Malam Nasir El-Rufai, da ɗaukacin iyalan El-Rufai kan rasuwar mahaifiyar su abar ƙauna, Hajiya Umma El-Rufai.

“Hajiya Umma El-Rufai ba kawai uwa mai sadaukarwa kuma shugabar iyali ba ce, har ila yau mace ce mai kyakkyawan hali na musamman, mai tsantsar gaskiya, da ƙarfi cikin natsuwa.

“Ta rayu rayuwa mai cike da jinƙai, tawali’u, da hidima mai ɗorewa, tana nuna jinƙai ga marasa ƙarfi tare da girmama duk wanda ya zo gare ta. A cikin al’ummar ta, ta kasance ginshiƙi na shawarwari da sulhu, tana ƙarfafa haɗin kai tare da zama abin koyi na ƙimomin imani, haƙuri, da karamci.

“A wannan lokaci na jimami, ina tare da iyalan El-Rufai cikin alhini, ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da ya gafarta mata kurakuran ta, ya karɓi ayyukan ta na alheri, ya kuma ba ta mafaka ta har abada a Aljannatul Firdausi.

“Allah ya sanyaya zuciyar waɗanda suka rasa ta, ya ba su juriyar jure wannan babban rashi. Amin.”

Tags: El-RufaiNuhuRibadurasuwata'aziyyaUba SaniUmma El-Rufai
Previous Post

An saki El-Rufai, ya koma gida domin jana’izar mahaifiyar sa

Next Post

Allah ya kyauta a ce wai Peter Obi ya zama Shugaban Nijeriya, inji Fani-Kayode

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Allah ya kyauta a ce wai Peter Obi ya zama Shugaban Nijeriya, inji Fani-Kayode

Allah ya kyauta a ce wai Peter Obi ya zama Shugaban Nijeriya, inji Fani-Kayode

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!