An saki tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, daga tsare shi da aka yi kuma ya koma gida domin halartar jana’izar mahaifiyar sa marigayiya, Hajiya Umma El-Rufai, wadda Allah ya yi wa rasuwa a yau.
Wata majiya a hukumar ICPC ta bayyana cewa an saki El-Rufai ne da misalin ƙarfe 8 na dare a yau Juma’a, inda jami’an tsaro suka raka shi zuwa gidan sa.
A cewar majiyar, “Akwai umarnin Shugaban Ƙasa na a saki El-Rufai nan take, wanda ICPC da jami’an tsaro suka bi ba tare da ɓata lokaci ba.
“Haka kuma wasu jami’an tsaro za su kasance a wurin jana’izar mahaifiyar tasa, duk da cewa babu tabbataccen bayani kan lokacin da zai koma wajen tsarewar. Wataƙila kotu za ta ba shi beli a ranar 31 ga Maris lokacin da zai koma kotu.”
Tabbacin sakin sa ya fito ne daga ɗan sa, Bashir El-Rufai, wanda ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a X (tsohon Twitter).
A cikin saƙon, Bashir ya bayyana tsare mahaifin sa a matsayin abin da aka yi “ba bisa ƙa’ida ba kuma haramtacce,” yana mai sukar hukuma da ya zarga da rashin gaskiya.
“Mun gode da dukkan goyon bayan da kuka nuna. Iyalin mu ba za su taɓa mantawa da wannan lokaci ba. Mun shawo kan lamarin, kamar yadda iyalan El-Rufai ke yi ko yaushe,” inji shi, yana nuna godiya ga masu goyon baya.
Sakin El-Rufai ya zo ne a wani lokaci mai cike da jimami ga iyalin sa, bayan rasuwar mahaifiyar sa wadda aka ruwaito ta rasu a birnin Alƙahira na ƙasar Masar bayan gajeriyar rashin lafiya.
Komawar sa gida domin halartar jana’izar ya jawo tausayin abokan siyasa, abokan hulɗa da kuma jama’a, inda da dama suka yi ta miƙa ta’aziyya a shafukan sada zumunta.
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shi ma ya miƙa ta’aziyyar sa ga El-Rufai da iyalin sa kan wannan rashi.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaban ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kyawawan halaye wadda ta tarbiyyantar da ’ya’ya da jikoki masu bayar da gudunmawa ga cigaban ƙasa.
“Nasir, don Allah ka karɓi ta’aziyya ta ta zuciya kan rasuwar mahaifiyar ka abar ƙauna…
“Rashin uwa ciwo ne da ba ya misaltuwa. Ina addu’ar Allah ya sa tunanin ƙauna, hikima da shawarwarin ta su zama abin sanyaya zuciyar ka a kwanaki masu zuwa.”
Shugaban Ƙasar ya kuma yi addu’ar Allah Ya jiƙan ta da rahama, ya kuma ba ta Aljannatul Firdaus.
Duk da cewa El-Rufai bai fito fili ya yi bayani kan sakin nasa ko rasuwar mahaifiyar sa ba, iyalin sa na ci gaba da nuna godiya kan irin goyon bayan da ’yan Nijeriya suka nuna.







