Jaridar New York Times ƙasar Amurka ta bayyana cewa Shugaba Donald Trump ya dogara kacokam ne da wasu bayanai da rahotannin wani ɗan Nijeriya mai suna Mista Emeka Umeagbalasi, wanda ɗan kasuwa ne mai sayar da sukundireba a garin Anacha, Jihar Anambra, wajen kai hare-hare ta sama a Nijeriya.
Idan kun tuna, a watan Oktoba ne Trump ya sake ayyana Nijeriya a matsayin “ƙasa mai matuƙar ba da damuwa ta musamman” bisa zargin ana aiwatar da kisan kiyashi ga Kiristoci a ƙasar. Ya ce: “Kiristanci yana fuskantar barazana ga wanzuwar sa a Nijeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
Trump ya ɗora laifin “kisan gillar tarin jama’ar” kan masu tsattsauran ra’ayin Islama.
Wata ɗaya bayan ya faɗi hakan, sai ya yi barazanar cewa Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka za ta mamaye Nijeriya “da bindigogi masu amon wuta” domin kawar da ‘yan ta’addar Islama gaba ɗaya idan har gwamnatin Nijeriya ba ta yi wani abu don daƙile zargin kisan ƙare dangin ba.
Ilai kuwa, a ranar 26 ga Disamba, Amurka ta kai hare-haren sama kan ‘yan ta’addar ISIS a Jihar Sakkwato “bisa roƙon hukumomin Nijeriya”.
Rahoton da New York Times ta buga ya bayyana cewa Mista Umeagbalasi, wanda ya kafa ƙungiyar International Society for Civil Liberties and Rule of Law (Intersociety), shi ne “tushen binciken ba-zata wanda ‘yan majalisar jam’iyyar Republican na Amurka suka yi amfani da shi wajen yaɗa ra’ayin ƙarya cewa wai ana ware Kiristoci ne kawai domin a kashe su” a Nijeriya.
Mista Umeagbalasi tare da matar sa suna gudanar da wannan ƙungiyar sa-kai su biyu kacal daga cikin gidan su.
Rahoton ya ce wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka biyu, wato Riley Moore da Ted Cruz, waɗanda Shugaba Trump ya umurce su da su binciki zargin kisan kiyashin Kiristoci a Nijeriya, tare da ɗan majalisa Chris Smith na jihar New Jersey, “duk sun ambaci aikin sa”.
A hirar sa da jaridar, Mista Umeagbalasi ya ce ya lissafa kisan Kiristoci mutum 125,000 a Nijeriya tun daga 2009 ne bisa binciken da ya gudanar a manhajar Google, da rahotannin kafafen watsa labarai na Nijeriya, da wasu bayanan a gefe, da ƙungiyoyin fafutika irin su Open Doors, wadda ƙungiyar Kiristoci ce da Trump ya taɓa ambaton bayanan ta.
Ɗan kasuwar ya shaida wa New York Times cewa ba kasafai yake tabbatar da sahihancin bayanan sa ba.
Ya kuma ce bai cika zuwa yankunan da hare-haren suka faru ba, kuma yawanci yana alaƙanta addinin waɗanda aka kashe ne da wurin da lamarin ya faru.
“Idan satar mutane ko kisan gilla ya faru a wani yanki da yake ganin Kiristoci da yawa suke zaune cikin sa, sai ya ɗauka cewa Kiristoci ne aka kashe,” inji rahoton.
A wata hira da ya yi da jaridar The Sun, lokacin da aka tambaye shi inda yake samo bayanan sa, Mista Umeagbalasi ya nuna “wuri da sararin da abin ya faru ko wurin aikata laifi” kuma ya bayyana hanyar sa a matsayin “ɗaya daga cikin tsofaffin hanyoyin da ake gudanar da bincike da su a duniya”.
Wannan ɗan tireda dai ya ce yana da digiri a fannin ilimin tsaro, zaman lafiya da warware rikice-rikice (Peace and Conflict Resolution) da ya samu daga Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN), kuma ya bayyana kan sa a matsayin mai bincike mai “ƙarfi sosai” kuma mutum mai “ɗimbin ilimi”.
Bugu da ƙari, Mista Umeagbalasi, wanda ya kira kan sa masanin ilimin laifuffuka (criminologist), an bayyana shi a matsayin ƙwararre a cikin rahoton, inda ya yi iƙirarin cewa akwai “dabarar da aka kitsa ta shafe dukkan Kiristoci tare da Musuluntar da Nijeriya”.
Ya yi iƙirarin cewa akwai coci-coci 100,000 a Nijeriya, kuma kusan 20,000 daga cikin su an ragargaza su cikin shekaru 16 da suka gabata.
Da aka tambaye shi inda ya samo wannan bayanin, kawai sai ya ce: “A Google na gani.”







