Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure, Fatima Abubakar, da ’ya’yan ta shida a unguwar Chiranci da ke Jihar Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci da abin Allah-wadai.
A wata sanarwa da Fadar Shugaban Kasa ta fitar a ranar Lahadi, Shugaban ya yaba wa rundunar ’yan sanda bisa gaggawar cafke manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin, tare da bayar da umurnin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da su gaban kotu ba tare da jinkiri ba.
Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga iyalan da abin ya shafa, yana mai addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan.

A cikin wannan sanarwar, Tinubu ya kuma bayyana alhinin rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma jagoran al’ummar ’yan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji (Dakta) Bature Abdul’aziz, wanda ya rasu a ƙarshen makon da ya gabata.
Shugaban ya ce rasuwar marigayin babbar asara ce, ba ga ’yan kasuwar Kano kadai ba, har ma ga kasa baki ɗayan, duba da irin tasirin da ya yi a harkokin kasuwanci da ƙungiyoyin ’yan kasuwa.
Marigayi Dakta Bature Abdul’aziz ya kasance shugaban ƙungiyar Harmonised Traders Association of Nigeria, tare da taka rawa a wasu ƙungiyoyin kasuwanci na ƙasa.
Tinubu ya kuma tuna irin gudunmawar da marigayin ya bayar a yaƙin neman zaɓen shekarar 2023, da kuma jajircewar sa wajen inganta haɗin kan ƙasa da kishin ƙasa ta hanyar Patriotic Elders Network for Peace (PENP) da ya assasa.
Shugaban Ƙasa ya miƙa saƙo ta’aziyyar sa ga ’yan kasuwa a Kano, da jama’ar jihar baki ɗaya, da kuma gwamnatin Jihar Kano, bisa wannan rashi.







