• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama a Jilli, ta ba da umurnin bincike

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
April 14, 2026
in Tsaro
A A
0
Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama da Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta kai a ranar 11 ga Afrilu a yankin Jilli da ke Ƙaramar Hukumar Gubio a Jihar Borno, tana mai cewa an kai harin ne kan ’yan ta’adda bisa sahihan bayanan sirri.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Talata.

Ya bayyana cewa yankin Jilli, wanda aka daɗe ana danganta shi da ayyukan ’yan ta’adda, ya kasance wurin da ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP suke amfani da shi wajen tsara hare-hare da gudanar da harkokin su.

A cewar sa, an kai harin ne bayan an shafe makwanni ana sa ido da tattara bayanan sirri, wanda ya tabbatar da kasancewar ’yan ta’adda a yankin, domin daƙile ayyukan su.

Yayin da take kare harin, Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da bayyana asarar rayukan fararen hula a matsayin abin takaici.

Idris ya ce: “Kowace rayuwar ɗan Nijeriya mai daraja ce, kuma duk wata asarar rayuwar fararen hula abin takaici ne matuƙa”.

Ya ƙara da cewa an ba da umurnin gudanar da cikakken bincike domin duba yadda aka tattara bayanai da kuma yadda aka aiwatar da harin, tare da ɗaukar matakan da suka dace idan an samu kurakurai.

“Kare rayukan fararen hula babban abu ne da ya rataya a wuyan rundunonin tsaro,” inji shi.

Gwamnatin ta kuma ce tana aiki tare da hukumomin jihohi da na agajin gaggawa domin tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa, tare da ƙarfafa matakan kariya.

Ta buƙaci jama’a da su bi ƙa’idojin tsaro tare da guje wa wuraren da aka hana shiga saboda barazanar tsaro.

Gwamnatin ta sake jaddada aniyar ta ta ci gaba da yaƙi da ta’addanci tare da inganta yadda ake gudanar da ayyukan tsaro.

Tags: BornohariJilliMohammed Idrissojojita'addanci
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniyar ƙarafa ta dala biliyan 1 a Indiya, jarin waje ya kai dala biliyan 2.2 a ƙarƙashin Tinubu

Next Post

Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

Sojoji sun ragargaji maɓoyar 'yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!