Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ta tsananta kai samame kan maɓoyar ‘yan bindiga a Jihar Bauchi, inda ta yi nasarar fatattakar sansanonin su, ta kamo iyalan su, kuma ta da lalata kayayyakin aikin su a dajin Madam.
Wani rahoton fafatawa da aka fitar a yau Laraba a Abuja ya bayyana cewa dakarun Birged ta 33 tare da haɗin gwiwar jami’ai daga Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro (ONSA) ne suka gudanar da wannan gagarumin aiki.
Sojoji sun share shahararrun sansanonin ‘yan bindigar da suka haɗa da sansanin Azuge da Hari, waɗanda ke zama matattarar ayyukan masha’a a cikin dajin.
An kashe ‘yan bindiga da dama yayin musayar wuta, yayin da sauran suka raba ƙafa sakamakon luguden wutar da aka yi masu.
Jami’an tsaron sun yi ram da mutum 19 da ake kyautata zaton iyalai ne ga ‘yan ta’addan, waɗanda suka haɗa da mata shida da yara 13.
Dakarun sun gano abubuwa da dama da suka haɗa da albarusan bindigar AK-47, ƙwayoyin Tramadol, kayan sarki da suka haɗa da kakin ‘yan sanda da na sojoji (na bogi), da dawakai biyu.
Bugu da ƙari, sojojin sun cinna wa baburan da ‘yan bindigar suke amfani da su wuta domin daƙile hanzarin su da rage masu ƙarfin gudanar da hare-hare.

Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa an kai wani samamen na daban a yankin Mainamaji bayan hare-haren jiragen yaƙi da aka kai a baya-bayan nan. Ko da yake ba a haɗu da kowa ba, hakan ya nuna cewa ‘yan bindigar sun tsere sakamakon matsin lambar da suke fuskanta.
A halin yanzu, dakarun sojin sun mamaye dajin domin tabbatar da cewa ‘yan bindigar ba su sake komawa ba.
Rundunar ta sake jaddada kudirin ta na ci gaba da matsa lamba har sai an samu cikakken zaman lafiya, kuma ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba su haɗin kai da bayanan sirri a kan lokaci.






