• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Nijeriya ta nemi haɗin gwiwa da sauran ƙasashe don ƙaryata labaran ƙarya

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
October 25, 2025
in Labarai
A A
0
Nijeriya ta nemi haɗin gwiwa da sauran ƙasashe don ƙaryata labaran ƙarya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa hulɗa da abokan ta na ƙasashen duniya domin yaƙar labaran ƙarya da ake yaɗawa don ɓata sunan Nijeriya.

Idris ya bayyana hakan ne a birnin London, ƙasar Birtaniya, a yau Asabar, a taron yankin Birtaniya na ‘Renewed Hope Global Dialogue’ mai taken, “Ƙarfafa Hulɗa da Duniya Don Sabunta Tattalin Arziki da Kyautata Martabar Ƙasa a Ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata,” inda ya jaddada cewa haɗin gwiwa shi ne mabuɗin sake fasalta yadda ake kallon Nijeriya a idon duniya.

Ministan ya nuna yadda Nijeriya take fuskantar barazanar labaran ƙarya da ake yaɗawa game da ita na cewar wai gwamnati tana kai hari ga mabiya wasu addinai a ƙasar.

Ya ce: “Mun mayar da martani sosai, mun bayyana a sarari cewa waɗannan labaran ƙarya ne daga waɗanda ba su da masaniya kan Nijeriya. Muna buƙatar abokan mu na ƙasashen duniya da suka fahimci ƙasar mu su taimaka wajen yaɗa batutuwan gaskiya game da Nijeriya.”

Ya bayyana cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), ta ƙaddamar da Ƙungiyar Kula da Martabar Nijeriya (NRMG) don inganta alfahari na ƙasa da kyakkyawan suna a duniya.

NRMG ta ƙaddamar da Aikin Kula da Martabar Nijeriya a Duniya, wanda ƙwararrun masu tsara suna ke jagoranta, inda ƙarin bayani zai biyo baya a watanni masu zuwa.

Ministan ya ce a ranar 15 ga Oktoba za a ɗauke ta a matsayin Ranar Martabar Nijeriya domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin martabar ƙasa.

Ya jaddada cigaban da Nijeriya take samu a fagen diflomasiyya, inda ya ce ƙasar za ta gudanar da taron Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a ta Afrika (APRA) 2026 da kuma Taron Duniya na Hulɗa da Jama’a (WPRF 2026) a Abuja — ita ce ƙasar Afrika ta farko da za gudanar da duka tarukan na duniya guda biyu a shekara guda.

Idris ya bayyana cewa manufofin diflomasiyyar Nijeriya, ƙarƙashin ƙa’idar Tinubu ta Dimokiraɗiyya, Cigaban Ƙasa, Yawan Jama’a, da ‘Yan Ƙasar Waje (4Ds), suna haifar da sakamako mai ma’ana.

Daga cikin su akwai shigar Nijeriya a matsayin ƙasar haɗin gwiwa ta BRICS, zaɓen ɗan Nijeriya a matsayin Sakatare-Janar na Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Gas (GECF), da cire Nijeriya daga FATF Grey List, wanda ke nuna nasarorin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.

A fannin cikin gida, Idris ya bayyana hoɓɓasan gwamnatin na kawo sauye-sauye, ya nuna cewa a yanzu Nijeriya tana aiwatar da tsarin haɗaɗɗen canjin kuɗi, da shirin lamuni da ya amfani ɗalibai fiye da rabin miliyan, da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, da sabon tsarin lamunin sayen kayan masarufi, da shirin shugaban ƙasa na iskar gas, da sababbin dokokin haraji guda huɗu, da Hukumomin Raya Yankuna guda biyar, da kuma ƙirƙiro Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi ta Tarayya.

Ya jaddada cewa waɗannan shirye-shirye ne da ke inganta burin ƙasar na zama mai ƙarfi ta fuskar tattalin arziki a duniya.

Ya ƙara da cewa Nijeriya tana dawo da martabar ta a gida da waje ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada cewa za ta ci gaba da ƙarfafa hulɗa da abokan haɗin gwiwa domin tabbatar da cigaban da ake samu.

“Mu gwamnati ce mai sauraren jama’a da kuma aiki tare, muna gayyatar ku da ku nemi ƙarin bayani game da abubuwan ban-sha’awa da ke faruwa a Nijeriya kuma ku duba hanyoyin haɗin gwiwa da mu don ɗaga sauye-sauyen da ake yi a Nijeriya zuwa mataki na gaba,” inji Idris.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi kan yaƙar labaran ƙarya game da Nijeriya… a yau a London

Tags: labaran ƙaryaLondonMohammed IdrisNIPRRenewed Hope AgendaShirin Sabunta Fata
Previous Post

Tinubu ya sauya Hafsan Hafsoshin Tsaro, ya naɗa Janar Oluyede a muƙamin 

Next Post

Ƙungiyar NFTD ta jinjina wa Yakubu, Babban Daraktan Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Ƙungiyar NFTD ta jinjina wa Yakubu, Babban Daraktan Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya

Ƙungiyar NFTD ta jinjina wa Yakubu, Babban Daraktan Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!