Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya (Chief of Defence Staff, CDS), inda ya tsige Janar Christopher Gwabin Musa daga muƙamin, ya maye gurbin sa da Janar Olufemi Oluyede.
Haka kuma ya yi sauyi a wasu muƙaman kamar haka:
- Chief of Army Staff, Major-General W. Shaibu;
- Air Vice Marshall S.K. Aneke, Chief of Air Staff;
- Rear Admiral I. Abbas, Chief of Naval Staff;
- Major-General E.A.P Undiendeye, Chief of Defence Intelligence (ba a sauya shi ba).
A cikin wata sanarwa da Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai, Sunday Dare ya fitar a yau, gwamnati ta ce sauye-sauyen sun fara aiki nan take.
Ta ce ta yi hakan ne domin ta “ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa tare da yin ƙarin hoɓɓasa kan matsalolin rashin tsaro da suke ƙara kunno kai a sassa daban-daban na ƙasar nan.”
Kafin naɗin nasa, Janar Oluyede ya riƙe muƙamin Hafsan Hafsoshin Sojoji (Chief of Army Staff).
Ya karɓi ragamar daga Janar Musa, wanda aka naɗa CDS a watan Yuni 2023.
Sanarwa ta ce, “Shugaban Ƙasa ya gode wa Hafsan Hafsoshin mai barin gado saboda sadaukarwar sa da ayyukan sa ga ƙasa, kuma ya yi kira ga sabon CDS da aka naɗa da ya nuna kyakkyawan shugabanci, ƙwarewa, da ƙaunar ƙasa a sabon muƙamin nasa.”
Kwanan nan ne dai labari ya cika ƙasa dangane da yunƙurin juyin mulki da aka ce an so yi wa gwamnatin Tinubu.







