• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, May 15, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

NDLEA ta damƙe mutum shida masu harƙallar cushen lodin muggan ƙwayoyi cikin kayan matafiya Saudiyya

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
August 25, 2025
in Labarai
A A
0
NDLEA ta damƙe mutum shida masu harƙallar cushen lodin muggan ƙwayoyi cikin kayan matafiya Saudiyya
Waɗanda ake zargi

Waɗanda ake zargi

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta ce ta samu gagarumar nasara kama wani Mohammed Ali Abubakar da aka fi sani da Bello Karama, wanda ake zargin babban mai safarar ƙwayoyi ne, tare da wasu mutane biyar masu aiki a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) da ake zargi da yi wa mahajjata cushen ƙwayoyi a cikin kayan su, yayin tafiya Saudiyya.

Cikin sanarwar da Kakakin Hukumar, Femi Babafemi, ya fitar bayan taron manema labarai a hedikwatar NDLEA ta ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin, ya bayyana cewa binciken NDLEA ya gano cewa mutanen sun shirya lodin jakunkuna shida a jirgin Ethiopian Airline daga Kano zuwa Jeddah, a ranar 6 ga Agusta, 2025.

Ya ce uku daga cikin jakunkunan na ɗauke da ƙwayoyi, aka cusa cikin kayan waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, labarin da ya jefa su hannun jami’an tsaro a Saudiyya, inda a yanzu haka suna can a tsare.

Waɗanda abin ya ritsa da su, su ne Maryam Hussain Abdullahi, Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddiq, waɗanda suka je aikin Umrah.

Sanarwar ta ce sun isa Saudiyya ne ba tare da sanin cewa an saka wa waɗannan jakunkuna da ƙwayoyi ba, abin da ya jawo aka tsare su a Jeddah.

NDLEA ta ce an gano Bello Karama shi ne ya kawo jakunkunan, inda daga baya ya bi jirgin Egypt Air zuwa Jeddah, yayin da ya bar jakunkunan da aka saka musu sunayen waɗannan matafiyan a Ethiopian Airline.

Babafemi ya ce an riga an kama mutane shida cikin waɗanda ake zargi da hannu, kuma sun amsa laifin su, tuni an gurfanar da huɗu a kotu.

Waɗanda aka gurfanar sun haɗa da Abubakar Abdulbasit, Murtala Akande, Olalekan da Yayock.

NDLEA ta tabbatar da cewa ma’aikatan filin jirgin saman na Kano masu hannu a harƙallar cushen ƙwayoyin sun amsa laifin su. Sun ce an biya kowanen su Naira 100,000, inda suka cusa ƙwayoyin a jakunkuna biyu kowanen su, tare da manna masu sunayen matafiyan waɗanda ba na su ba ne.

Waɗanda suka yi wannan harƙallar su ne Celestine Emmanuel Yayock da Jazuli Kabiru, waɗanda ma’aikatan Kamfanin Dakon Kaya na SAHCO ne da ke filin jirgin MAKIA.

Najeriya Za Ta Karɓo Waɗanda Aka Tsare A Saudiyya:

Babafemi ya bayyana cewa shi da kansa ya jagoranci tawagar jami’an NDLEA, inda suka je Jeddah, suka samu jami’an hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyin ƙasar, suka binciki jakunjunan.

Ya ce nan ba da daɗewa ba za a saki waɗanda aka tsare a Saudiyya, bayan an tabbatar da ba su ne suka aikata laifin shiga ƙasar da ƙwayoyin ba.

Previous Post

Kotunan Nijeriya sun zama cibiyoyin hada-hadar shari’u – Sarkin Musulmi

Next Post

Matar Tinubu ta ƙaddamar da masana’antar sarrafa fatun dabbobi, bayan an ruguje wa Hausawa kasuwar Alaba a Legas

Related Posts

Kotu a Amurka ta ɗaure farfesa ‘yar Nijeriya watanni 70 kan satar dala miliyan 1.4
Labarai

Kotu a Amurka ta ɗaure farfesa ‘yar Nijeriya watanni 70 kan satar dala miliyan 1.4

May 14, 2026
EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Next Post
Matar Tinubu ta ƙaddamar da masana’antar sarrafa fatun dabbobi, bayan an ruguje wa Hausawa kasuwar Alaba a Legas

Matar Tinubu ta ƙaddamar da masana'antar sarrafa fatun dabbobi, bayan an ruguje wa Hausawa kasuwar Alaba a Legas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!