• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kotu a Amurka ta ɗaure farfesa ‘yar Nijeriya watanni 70 kan satar dala miliyan 1.4

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
May 14, 2026
in Labarai
A A
0
Kotu a Amurka ta ɗaure farfesa ‘yar Nijeriya watanni 70 kan satar dala miliyan 1.4
Farfesa Nkechy Ezeh

Farfesa Nkechy Ezeh

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wata farfesa ‘yar asalin Nijeriya mai suna Nkechy Ezeh hukuncin ɗaurin watanni 70 a gidan yari bisa laifin damfarar kuɗi har dala miliyan 1.4.

Kotun gundumar da ke Jihar Michigan ta ce Farfesa Ezeh, wadda ita ce tsohuwar babbar daraktar gudanarwa ta ƙungiyar Early Learning Neighbourhood Collaborative (ELNC), ta aikata laifin “shirya wata damfara da ta wawure dala miliyan 1.4 na kuɗin masu biyan haraji da na masu bayar da tallafi, waɗanda aka ware domin taimaka wa ƙananan yara masu rauni da ke makarantar gaba da firamare.”

Alƙalin kotun, Hala Jarbou, ta bayyana Ezeh a matsayin “’yar damfara kuma ɓarauniya” wadda ta aiwatar da wata “bayyananniya kuma babbar” maƙarƙashiyar satar kuɗaɗen da aka tanada domin “yaran da suka fi kowa rauni” a yankin Yammacin Michigan.

Ezeh, wadda farfesa ce mai koyar da ilimi, ita ce ta kafa ELNC, wata ƙungiya mai zaman kan ta wadda Ma’aikatar Lafiya ta Amurka, Ma’aikatar Ilimi, da masu bayar da tallafi masu zaman kan su suke ɗaukar nauyin ta domin samar da abinci, sufuri, tallafi, kare haƙƙi, da sauran ayyuka ga yara a al’ummomin da ba su da isassun ayyukan jinƙai.

A cewar wata sanarwa da gwamnatin Amurka ta fitar, alƙalin ta umurci Ezeh da ta biya dala miliyan 1.4 a matsayin diyyar mayar da asarar da waɗanda aka damfara suka yi, sannan ta biya dala 390,174 ga Hukumar Harajin Cikin Gida ta Amurka (IRS).

Har ila yau, alƙalin ta yanke mata hukuncin ɗaurin watanni 60, wanda za ta yi lokaci guda, saboda kauce wa biyan harajin kuɗin shiga.

A watan Disambar 2025, farfesar ta amsa laifukan damfarar hanyar sadarwa, haɗin baki wajen aikata laifi, da kauce wa biyan haraji.

Bisa ga yarjejeniyar amsa laifi, Ezeh ta amince cewa “tun daga aƙalla 2017 zuwa 2023, ta haɗa baki da Sharon Killebrew da wasu domin shirya wata maƙarƙashiyar damfarar ELNC da karɓar dala 1,400,000.”

Gwamnatin Amurka ta ce an rufe ELNC a 2023 sakamakon wannan damfara, lamarin da ya sa makarantu da dama na gaba da firamare a Yammacin Michigan suka rasa tallafi, yayin da yara mabuƙata suka rasa muhimman kayayyakin tallafi.

Ƙungiyar mai zaman kan ta ta kuma sallami ma’aikatan ta 35 ba tare da sanarwa ba.

Ita ma Sharon Killebrew, tsohuwar mai kula da lissafin ELNC kuma abokiyar aikata laifin Ezeh, an yanke mata hukuncin ɗaurin watanni 54 a gidan yari na tarayya a watan Nuwamban 2025 saboda rawar da ta taka a wannan maƙarƙashiya.

Da yake tsokaci kan hukuncin, Timothy VerHey, lauyan gwamnatin Amurka na yankin yammacin Michigan, ya ce Ezeh ta kashe kuɗaɗen tallafin da aka ware domin yara a kan ta maimakon taimaka musu.

“Kwaɗayin Nkechy Ezeh abin ƙyama ne matuƙa,” inji VerHey.

“Ta sace kuɗaɗen masu biyan haraji da na masu bayar da tallafi masu zaman kan su da aka ware domin yara marasa galihu a al’ummar mu. Maimakon taimaka wa yara, ta kashe kuɗin a kan ta.

“Da wannan kuɗin da aka sace, da an taimaka wa ɗaruruwan yara a Yammacin Michigan tare da iyalan su.

“Hukuncin da Alƙali Jarbou ta yanke ya dace ƙwarai.”

Tags: AmurkadamfaraEarly Learning Neighbourhood Collaborative (ELNC)Hala JarboukotuMichiganNkechy Ezehɗauri
Previous Post

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

Next Post

Nagartattun sauye-sauyen CBN kan manufofin tattalin arziki sun haddasa ambaliyar masu sha’awar zuba jari daga ƙasashen waje

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa

Nagartattun sauye-sauyen CBN kan manufofin tattalin arziki sun haddasa ambaliyar masu sha'awar zuba jari daga ƙasashen waje

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!