• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Ƙasashen Duniya

Matar Firayim Ministan Faransa, Brigitte Macron, za ta kai hujja kotu cewar ita ba ɗa namiji ba ce

ALI KANO by ALI KANO
September 19, 2025
in Ƙasashen Duniya
A A
0
Matar Firayim Ministan Faransa, Brigitte Macron, za ta kai hujja kotu cewar ita ba ɗa namiji ba ce
Emmanuel da Brigitte Macron a wajen babban taron ƙasashen G7 da aka yi a garin Cornwall na ƙasar Ingila, cikin Yuni 2021. (Hoto: Jack Hill/AFP via Getty)

Emmanuel da Brigitte Macron a wajen babban taron ƙasashen G7 da aka yi a garin Cornwall na ƙasar Ingila, cikin Yuni 2021. (Hoto: Jack Hill/AFP via Getty)

Uwargidan Firayim Ministan ƙasar Faransa, Brigitte Macron, ta bayyana ƙudirin ta na kai hujja kotu mai tabbatar da cewa ita mace ce, ba ɗa namiji ba.

Hujjojin sun haɗa da hotuna da shaidun kimiyya.

Haka kuma ita da mijin ta sun shigar da ƙara a kotu a kan wata ‘yar taratsin soshiyal midiya mai suna Candace Owens bisa zargin ta da zaƙewa kan yayata wannan iƙirarin wanda ya yaɗu a duniya kamar wutar bazara.

Suka ce wannan wani kamfen ne da ake yin sa don a tsinka su a idon duniya.

Ita dai Candace Owens, mai shekaru 36, ta fi kowa yaɗa wannan magana cewa wai an haifi Brigitte ne a matsayin ɗa namiji, sai ta saci suna da bayanan wata mace domin ta yaudari jama’a tun daga lokacin.

Ta ce sunan namijin Jean-Michel Trogneux, to amma masu binciken lamarin sun gano cewa ai wannan ɗan’uwan Bridgette ɗin ne ciki ɗaya.

A watan Maris 2024, Owens ta rantse a manhajar X cewa ta amince da zubewar dukkan mutuncin ta idan an tabbatar da cewa Brigitte Macron ba namiji ba ce tun asali.

Ita ma ta yi ƙarar su Macron ɗin domin a yi watsi da ƙarar da suka kai ta.

Lauyan su Macron, Tom Clare, ya faɗa wa BBC kwanan nan cewa wannan ji-ta-ji-tar ta taɓa mutuncin Firayim Minista Emmanuel ɗan shekara 47, da matar sa Brigitte ‘yar shekara 72, kuma ma’auratan sun sha alwashin wanke kan su a kan wannan ƙage da aka yi masu

Ya ce: “A gaskiya abin damuwa ne matuƙa a ce sai mutum ya yi irin wannan abin, ya kawo irin wannan hujjar… Abu ne wanda tilas ta yi shi a bainar jama’a. Amma a shirye take ta yi hakan. Ta shirya tsaf domin ta yi abin da ya dace saboda ta kawar da duk wani shakku.”

Wata majiya ta ce daga cikin hujjojin da Bridgette za ta bayar a kotu har da hotunan da aka ɗauke ta tana da cikin ‘ya’yan ta da ta haifa.

Tags: Bridgette MacronCandace OwensEmmanuel Macronlabaran ƙaryasoshiyal midiyatakaddama
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta yi jimamin rasuwar mutane a gobarar Benen Afriland a Legas

Next Post

Gwamnan CBN ya gargaɗi masu wulaƙanta takardar Naira

Related Posts

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce
Ƙasashen Duniya

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

April 24, 2026
Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

April 20, 2026
Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa
Ƙasashen Duniya

Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa

April 20, 2026
Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran
Ƙasashen Duniya

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

April 18, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Ƙasashen Duniya

CBN na shirin kafa kwamitin sulhu don warware rikice-rikicen masu taurin bashi

April 17, 2026
Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta
Ƙasashen Duniya

Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta

April 3, 2026
Next Post
Gwamnan CBN ya gargaɗi masu wulaƙanta takardar Naira

Gwamnan CBN ya gargaɗi masu wulaƙanta takardar Naira

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!