• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, October 1, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnan CBN ya gargaɗi masu wulaƙanta takardar Naira

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
September 19, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnan CBN ya gargaɗi masu wulaƙanta takardar Naira
Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso, ya yi kakkausan gargaɗi ga masu watsa takardar Naira yayin bukukuwa, da masu duƙunƙune takardun kuɗaɗe, da masu hadahadar sababbin kuɗi da kuma masu buga kuɗaɗen jabu.

Wannan gargaɗin ya fito ne daga Kakakin Yaɗa Labarai ta CBN, Hakama Sidi Ali, wadda ta wakilci Cardoso a wani taron wayar da kan jama’a da bankin ya shirya a ranar Alhamis, a Kaduna.

Ya ce dukkan waɗannan laifuffuka ne masu nuna rashin kishin ƙasa, kasancewa wulaƙanta Naira tamkar wulaƙanta ƙasa ne ɗungurugum.

Taron, wanda CBN ya raɗa wa suna, “Samar da Hanyoyin Hada-hadar Kuɗaɗe a Matsayin Dabarun Bunƙasa Tattalin Arziki,” an shirya shi ne kacokan domin ƙarfafa wa jama’a yadda za su gane tare da fahimtar tsare-tsaren Babban Bankin Nijeriya, sai kuma rawar da al’umma za su taka wajen samar wa tattalin arziki nagartattun ƙafafun da iya tsayuwa a kai.

Cardoso ya ce an bijiro da wannan shiri domin fito da kusantakar da ke tsakanin muhimmancin amfani da asusun banki da kuma bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEs), waɗanda ke da muhimmin tasiri wajen saisaita daidaiton farashi da kuma inganta tattalin arziki.

Ya ce: “Ina gargaɗin kowa cewa ya riƙa riƙe Naira da daraja sosai, ya daina sa mata datti. A guji watsa takardun Naira yayin tarukan bukukuwa da shagulgula. A daina hada-hadar sabbin nairori, a daina duƙunƙune Naira, kuma a daina buga jabun kuɗaɗe. Saboda Naira ita ce alamar ƙima da darajar Nijeriya.”

Gwamnan ya ce taron yana daga shirin da bankin ya bijiro da shi domin ci gaba da bayyana wa jama’a irin tasirin da yake sanarwa wajen inganta rayuwar su, bunƙasa tattalin arziki da ciyar da harkokin kasuwancin su gaba.

Ya ci gaba da cewa an fara ganin alfanun sababbin tsare-tsaren da CBN ya fito da su, kamar samun ƙarin masu zuba jari a Nijeriya, cinikayya mai riba ba mai giɓin hada-hadar kuɗaɗe ba, sai kuma ƙarin masu amfani da asusun banki wurin hada-hadar su.

Cardoso ya lissafa manyan nasarorin da CBN ya samar, waɗanda ya ce sun haɗa samar farashin musayar Naira da kuɗaɗen waje na bai-ɗaya, kawar da matsalar musayar kuɗaɗen waje na Dala biliyan 7, bayan an tantance, sai kuma ci gaba da ake kan yi wajen ƙarfafa jarin bankuna, da nufin cimma ƙudirin ganin darajar tattalin arzikin cikin gida na Najeriya ya kai Dala tiriliyan ɗaya.

Tags: bukukuwaCBNNairaOlayemi Cardoso
Previous Post

Matar Firayim Ministan Faransa, Brigitte Macron, za ta kai hujja kotu cewar ita ba ɗa namiji ba ce

Next Post

“Hasken rayuwa ta”: Tinubu ya taya matar sa Oluremi murnar cika shekaru 65 da kalmomi masu daɗi

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
“Hasken rayuwa ta”: Tinubu ya taya matar sa Oluremi murnar cika shekaru 65 da kalmomi masu daɗi

"Hasken rayuwa ta": Tinubu ya taya matar sa Oluremi murnar cika shekaru 65 da kalmomi masu daɗi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!