• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Idris Ya Ƙaryata Ji-ta-ji-tar An Mayar Da Taron Bayanin Ministoci Zuwa London

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
May 16, 2025
in Labarai
A A
0
Idris Ya Ƙaryata Ji-ta-ji-tar An Mayar Da Taron Bayanin Ministoci Zuwa London
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa wai an mayar da Jerin Taron Bayanin Ministoci Ga ‘Yan Jarida daga Abuja zuwa London.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a lokacin buɗe jerin taron na takwas da aka gudanar a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa da ke Abuja.

Ya ce: “Ga amsar ku ga ji-ta-ji-tar cewa wai za a mayar da taron ‘yan jarida zuwa ƙetare. Muna da nauyin da ya rataya a wuyan mu na farko ga Nijeriya, shi ya sa muke gayyatar ministoci su zo nan su yi wa ‘yan Nijeriya da ma waɗanda ke waje jawabi kai-tsaye daga nan Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa da ke Abuja.

“Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne.

“Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.”

Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi.

Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba ne.

Idris ya kuma taɓo batun tattalin arzikin ƙasa, inda ya yi nuni da Rahoton Nuna Canjin Farashin Kayayyaki (CPI) na watan Afrilu 2025 da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta fitar.

Ya ce: “Yau, ina farin cikin bayyana wani labari mai daɗi daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, wadda ta fitar da Rahoton Nuna Canjin Farashin Kayayyaki (CPI) na watan Afrilu 2025, jiya. Bisa ga rahoton, adadin hauhawar farashin kayayyaki na watan Afrilu ya tsaya a kashi 23.71, wanda ke nuna ragin kashi 0.52 daga 24.23 da aka rubuta a watan Maris 2025.

“Haka kuma, idan aka kwatanta wata da wata, hauhawar farashin ya ragu sosai da kashi 2.04, daga 3.90 a Maris zuwa 1.86 a Afrilu.

“Wannan ba ya faruwa haka ziƙau. Tsare-tsaren Shugaban Ƙasa da aka mayar da hankali a kai su ne suke haifar da ɗa mai ido. Fa’idar gyare-gyaren da ake yi, ko da yake a hankali suke zuwa, tabbatattu ne kuma mutum zai iya auna su.”

Ministoci a wurin taron

 

Ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyakin abinci – wanda ke ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa hauhawar farashi – ya fara raguwa sakamakon tsare-tsaren Shugaban Ƙasa Tinubu.

Ya ce: “Ɗaya daga cikin manyan alamu na sauƙin da ake samu shi ne ƙimar hauhawar farashin abinci. Duk da cewa farashin abinci har yanzu yana damun mutane da dama a Nijeriya, hauhawar farashin abinci daga shekara zuwa shekara ya ragu zuwa kashi 21.26 a watan Afrilu.

“Idan aka duba wata zuwa wata kuwa, ya ragu zuwa kashi 2.06, daga kashi 2.18 da aka samu a Maris. Wannan cigaba mai kyau ya samo asali ne daga ragin farashin muhimman kayan abinci irin su garin masara, hatsi, garin doya, kuɓewa, gyaɗa, shinkafa, da wake.

“Jama’a, mun san cewa har yanzu ba mu kai inda muke fatar kaiwa ba. Amma waɗannan alƙaluman da aka samu kwanan nan suna ba mu cikakken dalili na yin fatan alheri. Suna nuna cewa matakan da muka ɗauka masu wahala sun fara haifar da kyakkyawan sakamako. Kuma yayin da farashi yake sauka, muna sa ran ganin sauƙi a ƙarfin sayen kayan masarufi da kuma rayuwar jama’a gaba ɗaya.”

Ministan ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa Gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da ɗaukar matakan da ke mayar da hankali kan rayuwar jama’a don kawo sauƙi, da dawo da daidaiton tattalin arziki, da inganta walwala ga kowa da kowa.

Ya kuma roƙi kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da ba da labarin irin wannan cigaban cikin gaskiya, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da zama mai gabatar da komai a bayyane kuma amintacciya ga ‘yan ƙasa.

Previous Post

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta zaɓi Farfesa Piwuna a matsayin Shugaba

Next Post

Matsalar Tsaro A Katsina: Rayuwar Mazauna Yankunan Karkara Ƙarƙashin Yarjejeniyar Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Matsalar Tsaro A Katsina: Rayuwar Mazauna Yankunan Karkara Ƙarƙashin Yarjejeniyar Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Matsalar Tsaro A Katsina: Rayuwar Mazauna Yankunan Karkara Ƙarƙashin Yarjejeniyar Sulhu Da 'Yan Bindiga

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!