• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, May 15, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Rahoton Musamman

Matsalar Tsaro A Katsina: Rayuwar Mazauna Yankunan Karkara Ƙarƙashin Yarjejeniyar Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA by Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA
May 19, 2025
in Rahoton Musamman
A A
0
Matsalar Tsaro A Katsina: Rayuwar Mazauna Yankunan Karkara Ƙarƙashin Yarjejeniyar Sulhu Da ‘Yan Bindiga
Jana'izar mutum 18 da 'yan bindiga suka kashe a ƙauyen Tsauwa da ke Ƙaramar Hukumar Batsari, Jihar Katsina, a cikin 2021

Jana'izar mutum 18 da 'yan bindiga suka kashe a ƙauyen Tsauwa da ke Ƙaramar Hukumar Batsari, Jihar Katsina, a cikin 2021

A daidai lokacin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara Jihar Katsina a ranar 2 ga Mayu, 2025, a daidai lokacin kuma dandazon matasan ƙauyukan yamma da garin Batsari na can suna yi wa ‘yan bindiga aikin ‘leburanci’ a cikin dajin ƙauyen Nahuta, wanda ke tazarar kilomita 13 daga Batsarin.

An gano ɗimbin albarkatun ma’adinai a ƙarƙashin ƙasa shimfiɗe a dajin Nahuta, wanda ke cikin Jihar Katsina, tazarar kilomita 15 zuwa kan iyakar Katsina da Jihar Zamfara. Dajin, wanda a halin yanzu yake ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga, ya zama wurin dabdalar haƙar ma’adinai ga dandazon matasa.

To sai dai waɗannan matasa waɗanda ke zuwa aikin leburancin haƙar ma’adinai, ‘yan bindiga suke wa aiki.

Wannan hada-hada ta buɗe ne sanadiyyar wata yarjejeniyar sulhu da jaridar New Citizen Hausa ta tabbatar an cimma da ‘yan bindiga, a ƙarƙashin babban gogarman su, wani hatsabibi kuma fitinanne wai shi Abu Raɗe, wanda a bisa kuskure wasu ke kiran sa da Usman Raɗɗa.

Tabbatattun majiyoyi ba ɗaya ba a garin Batsari, sun shaida wa New Citizen Hausa cewa, “Gwamnatin Jihar Katsina ba ta shiga cikin yarjejeniyar sulhun ba. Amma dai cikin waɗanda suka halarci zaman akwai Shugaban Ƙaramar Hukumar Batsari, Alhaji Yusuf Mamman Ifo, da Sarkin Ruma Tukur Mu’azu da kuma Difi’on ‘yan sanda na Ƙaramar Hukumar Batsari.

Nahuta, Zangon Haƙar Ma’adinai A Katsina:

Tun a farkon 2025 hada-hadar ma’adinai ta buɗe a Nahuta, ƙauyen da bai wuce kilomita 13 daga Batsari ba, kuma 60 da kaɗan tsakanin sa da Katsina. Yayin da New Citizen Hausa ba ta gano adadin abin da ‘yan bindigar ke sallamar leburori a kowace rana ba, amma dai ta gano cewa ana sayen lemun roba kala-kala daga Batsari ana kaiwa cikin ƙauyen Nahuta. “Daga can ne kuma ‘yan bindiga ke zuwa su riƙa jida kan babura suna kaiwa sansanin haƙar ma’adinai,” inji wani ɗan cikin garin Batsari da ya yi zancen da wakilin mu. Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar ba su shiga cikin Nahuta da makamai idan sun je ɗaukar lemun.

Haka nan kuma ya tabbatar wa da wakilin mu cewa yanzu haka hada-hada ta buɗe a Nahuta, domin ta kai har wasu ma sun kai rumbunan yin ƙanƙara a garin, wato ‘cold room.’

‘In ba ka yi ba ni wuri“ a wani ƙauye a Jihar Katsina wanda ‘yan ta’adda suka kai wa hari

Wane Ne Gogarma Abu Raɗe?:

Abu Raɗe Bafulatanin ƙauyen Baranda ne, yamma da Tashar Modibbo, cikin Ƙaramar Hukumar Batsari. Baranda asalin wani wuri ne da Gwamnatin Tarayya ta gina Ma’aikatar Kula da Lafiya da Bunƙasa Kiwon Dabbobi, wato Livestock Improvement Breeding Centre (LIBC) tun cikin 1978, a tsakiyar Dajin Rugu, zamanin mulkin soja na Olusegun Obasanjo.

Abu Raɗe ya fatattaki mazauna yankin, inda ya mayar da wannan ma’aikata tamkar sansanin sa, kamar yadda New Citizen Hausa ta samu labari.

Haka kuma wakilin mu ya tattauna da mutane daban-daban, waɗanda suka tabbatar masa da cewa ana kai wa ‘yan bindiga da leburorin su ruwa daga cikin garin Katsina, har cikin Nahuta. “Akwai wata mota ƙirar J5 da ke yawan wucewa daga Katsina tana kai lodin fiyawata har cikin Nahuta.

New Citizen Hausa ta gano cewa kafin a ƙulla sulhu da gogarma Abu Raɗe, shi da yaran sa sun tarwatsa ƙauyukan da ke yamma da Batsari, haka mazauna ƙauyukan duk sun tarwatse, kusan tsawon shekaru biyar ba su noma.

Wani da ba ya so a ambaci sunan sa a garin Batsari ya shaida wa wakilin mu cewa, “Garuruwa irin su Ɗangeza, Shingi, Ɗankwadatso, Madogara, Zamfarar Madogara, Ɗantsuntsu, Ƙasai, Salihawar Madogara, Garin Yara, Sabon Garin Dumburawa, ‘Yarlarba, Kurawa, Dankar, ‘Yandaka, Ruma da ma wasu, duk sun zama kufai, domin mazauna garin sun tsere daga farkon zangon mulkin Buhari na biyu, wato 2019, har zuwa ƙarshen 2024.

“Amma yanzu dalilin sulhun da aka yi, mutane sun fara komawa ƙauyukan su. Ko a ranar yau, 3 ga Yuni, 2025 an yi sallar Juma’a a Ɗangeza. Da kuwa an shafe shekaru ba mutane a garin.”

Wakilin mu ya gano cewa su ma Fulanin cikin jejin yamma da Batsari lamarin ya shafe su, sun shafe shekaru cikin ƙunci a takure. Dalilin sulhun da aka yi, masu yawa sai ficewa suke yi tare da dabbobin su suna nausawa gabas.

“Ya kamata ka gane cewa mu dai nan cikin garin Batsari a gaskiya ba mu yarda da wannan sulhu ba,” cewar majiyar mu.

Sulhun Batsari: Tallafin Kayan Abinci Da Shanun Noma Daga ‘Yan Bindiga:

Binciken New Citizen Hausa ya gano cewa tuni wasu mazauna yankunan yammacin Batsari suka samu tallafin buhunan gero da dawa daga ‘yan bindiga, bayan komawar su gida, sakamakon sulhun da aka yi. Haka kuma da dama a cikin garin Batsari sun shaida wa wakilin mu cewa ɗan bindiga Abu Raɗe ya yi wa manoma alƙawarin tallafa masu da shanun huɗa idan damina ta sauka. Sai dai wakilin mu bai tabbatar da shin kyauta zai taimaka masu da shanun noman ko kuwa aro zai bai wa manoman ba.

Sannan kuma Raɗe ya yi alƙawarin ba da gudunmawa wajen farfaɗo da karatun Islamiyya, ta hanyar ɗaukar nauyi ko tallafa wa malaman da za su riƙa koyar da yara. Wannan jarida ta ji haka daga bakin mutanen Batsari daban-daban, waɗanda ta tattauna da su ta wayar tarho.

Manoman da suka fara komawa ƙauyukan su dai akwai jan aiki a gaban su. Na farko dai a tsawon shekarun da suka yi na gudun hijira, yawanci zuwa cikin garin Batsari, ‘yan bindiga sun ɓaɓɓalle kwanon rufin gidajen su, sun sace wayoyin lantarki da tiransifomi masu ba da hasken wutar lantarki a yankunan.

Ba a yankin Batsari kaɗai aka yi sulhu da ‘yan bindiga a Jihar Katsina ba. Watannin baya an yi a Jibiya, tare da gogarman ‘yan bindigar da ya fitini yankin, mai suna Audu Lanƙai. Bisa dukkan alamu mazauna yankin na Jibiya sun fara samun kwanciyar hankali, domin motoci na zirga-zirga tsakanin Jibiya zuwa Batsari, sannan kuma yanzu ana cin kasuwar Jibiya. Kuma an amince Fulani su shiga su yi hada-hadar su, su koma cikin daji.

Majiya ta tabbatar wa da wakilin mu cewa, “Yanzu Audu Lanƙai ya hana a kai hare-hare, kuma duk inda ya samu labarin wasu sun kai hari, to zai sa a kamo wanda ya kai harin ya kashe shi.

Sai dai kuma wasu na ganin wannan sulhu ba zai ɗore ba, domin babu ɗan bindigar da ya ajiye makaman sa a yankunan biyu, wato Batsari da Jibiya.

Bambancin Sulhun Mazauna Gabacin Faskari:

Yankin Faskari yana daga cikin ƙananan hukumomin da ‘yan bindiga suka yi wa mummunar illa a Jihar Katsina. Haka su ma ƙananan hukumomin Safana, Sabuwa, Kurfi, Dutsin-ma ma, da sauran su. Yawancin su a ƙaramar hukuma za ka fahimci cewa kusan babu ƙauyen da ‘yan bindiga ba su shiga ba. Ɗaruruwan ƙauyuka duk sun zama kufai, babu kowa, sai daga baya-bayan nan wasu ke ƙarfin halin komawa.

A yankin Faskari, gabacin garin Sheme, ƙauyuka irin su Ruwan Godiya, Kwai, Gidan Kare, Ɗanba’u, Fulanin Ɗanba’u, Ligel, Kwakware ‘A’ da Kwakware ‘B’, da suka gaji da kisan da ake yi masu da asarar ɗimbin dukiya, sai suka yi sulhu da ‘yan bindiga.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar wa wakilin mu cewa, “Wannan sulhu ya sa mun samu damar kwashe amfanin gonar mu a ƙarshen 2024. Ba mu da yadda za mu yi sai dai mu yi sulhu da su kawai, domin lamari ne ya zama mabugi kusa, maceci nesa.”

Ya ci gaba da cewa, “Yaushe don za mu yi sulhu da macutan mu sai mun tsaya yin shawara da waɗanda suka kasa kare mu?”

Sannan kuma ya ce daga kashe-kashen da aka yi na ɗimbin mutanen da ya sani, shi dai a yankin su ba a taɓa kai masu tallafi ko na bargo ba a gidajen da aka yi garkuwa da wasu ko wani, ko inda aka yi kisa.

Ya ce: “Amma dai muna ganin irin yadda ake kai tallafi kuma shugaban ƙaramar hukuma da hakimi da DPO na can suna zuwa jaje, kuma mun ga inda aka kai masu tallafin kuɗaɗe idan irin haka ya faru a maƙwabtan mu da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bakori.”

A tattaunawar da wakilin mu ya yi da wani mazaunin yankin a ranar 19 ga Mayu, 2025, ya tabbatar masa cewa, “Tun bayan da muka yi sulhu ba a ƙara shigowa ƙauyukan mu ba. Amma har yanzu suna kai hare-hare a yankunan da ba a yi sulhu da su ba. Ko kuma su tare hanya kawai, wanda ya je wucewa su ƙwace abin da ke hannun sa, su bar shi ya yi gaba.”

Har zuwa ƙarshen Disamba 2024 dai babu mutane a garuruwa da dama, wasu kuma ‘yan ƙalilan ne suka koma a wurare. “Kamar Unguwar Boka, ba komai sai masallacin garin.”

Ƙauyuka irin su unguwar Dogo, Unguwar Ranɗama, Suntum, Dogon Dawa, Tsuru, Munhaye, Unguwar Rimi, Bangi, Zuru, Raɓa, Hurumin Ƙogo, Hayin Maikalwa da sauran su da dama duk sun fuskanci fitinar ‘yan bindigar da ta kassara su. Wasu garuruwan an sace komai, “hatta injin niƙa sai a yi masa filla-filla a cire shi.”

Marina: Garin Da Ake Cin Kasuwa Tilas Tare Da ‘Yan Bindiga A Safana:

Ƙaramar Hukumar Safana, wadda ita da Batsari Dajin Rugu ke cikin su, tana daga cikin ƙananan hukumomin da aka ƙirƙira daga cikin Dutsin-ma. Sauran sun ƙunshi Kurfi, Batsari da Ɗanmusa. Safana har yau tana tsakiyar fama da gaggan ‘yan bindiga garke-garke, ko a ce sansani-sansani, waɗanda ke jibge a cikin Dajin Rugu.

Akwai wani gari mai suna Marina, wanda ke daidai bakin Dajin Rugu, nisan kilomita 20 daga garin zuwa Batsari, amma kimanin kilomita 27 zuwa Safana. Kasuwar Marina tana ci a kowace Asabar. Wakilin mu ya samu tabbacin cewa a duk ranar kasuwar aƙalla ‘yan bindiga 100 sukan shiga kasuwar su yi harkokin su, amma fa kowane ɗauke da bindiga ƙirar AK-47.

Wani direba da ya ɗauki fasinjoji ya kai kuma ya maida su daga wajen Batsari, ya tabbatar da cewa, “Ko jiya Asabar (17 ga Mayu, 2025) na je kasuwar Marina. Kuma da ido na sai da na ga ‘yan bindiga sun fi ɗari, kowane ɗauke da AK-47. Babu ruwan su da kowa, idan sun gama cin kasuwa su koma cikin daji.”

Direban ya ci gaba da shaida wa wakilin mu cewa amma fa daga Madina babu mai iya keta dajin ya ƙarasa garin Runka.

Yankin Safana da Dutsin-ma har wani ɓangare na Kurfi ne suka yi fama da gogarma Usman Moɗi-moɗi wanda ya rasa ran sa a wani faɗan ‘yan bindiga su-ya-su, cikin 2024. Kuma shi ne ubangidan Jankare.

Previous Post

Idris Ya Ƙaryata Ji-ta-ji-tar An Mayar Da Taron Bayanin Ministoci Zuwa London

Next Post

Batutuwa 25 Dangane Da Manyan Attajirai 3,028 Na Duniya 

Related Posts

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi
Rahoton Musamman

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi

May 14, 2026
Kamfanonin ‘yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ya lashe lambar yabo ta Gwarzon Babban Bankin Shekara na Duniya

March 24, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya umurci bankuna su yi gwajin ƙarfin jure matsin tattalin arziki

March 8, 2026
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa

February 2, 2026
Rawar da Babban Bankin Nijeriya ke takawa a tallafin kuɗin noma
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rawar da Babban Bankin Nijeriya ke takawa a tallafin kuɗin noma

January 13, 2026
Ɗaiɗaicewa da ɓalɓalcewar matasan Arewa cikin duniya
Rahoton Musamman

Ɗaiɗaicewa da ɓalɓalcewar matasan Arewa cikin duniya

December 28, 2025
Next Post

Batutuwa 25 Dangane Da Manyan Attajirai 3,028 Na Duniya 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!