Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta zaɓi Farfesa Chris Piwuna na Jami’ar Jos a matsayin sabon Shugaban ta.
Piwuna dai shi ne Shugaban Tsangayar Al’amurran Ɗalibai na Jami’ar Jos kuma babban likita ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos.
An gudanar da zaɓen a wajen babban taron ƙasa na 23 na ƙungiyar a ranar Lahadi a Jami’ar Benin da ke Birnin Benin, Jihar Edo.
Farfesa Piwuna ya karɓi ragamar ƙungiyar daga hannun Shugaba mai barin gado, wato Farfesa Emmanuel Osodeke na Jami’ar Aikin Gona ta Michael Okpara da ke Umudike wanda ya gama wa’adin sa na shekara huɗu.
A zaɓen, ya kayar da Farfesa Adamu Babayo na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), Bauchi.
Sauran waɗanda aka zaɓa su ne Austen Sado (Mataimakin Shugaba); Happiness Uduk (sakatariyar kuɗi); Peter Adamu (ma’aji); Celestine Aguoru (sakataren zuba jari); Aisha Bawa (jami’ar walwala), da Ƙassim Umar (oditan cikin gida).
Ɗimbin malaman jami’a daga faɗin ƙasar nan suka halarci taron domin tattaunawa kan matsalolin da suka addabi harkar Ilimin jami’a a Nijeriya tare da zaɓen sababbin shugabannin ƙungiyar.
Zaɓen Piwuna ya zo a daidai lokacin da jami’o’i suke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi, musamman ma batutuwan ɗaukar nauyin su, biyan alawus-alawus ɗin malamai, hijirar malamai daga jami’o’i zuwa wasu ɓangarorin ko ma ƙasar waje, ‘yancin gudanarwa, da inganta rayuwar malamai.
A jawabin sa na karɓar jagoranci, Farfesa Piwuna ya sha alwashin zai tunkari manyan matsalolin da ke addabar jami’o’i, sannan ya roƙi abokan aikin sa da su ba shi haɗin kai don a taru a fidda jaki daga duma.






