• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta taya ’yan Nijeriya murnar Kirsimeti, ta yi kira a yi haɗin kai da tausayi

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
December 24, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta taya ’yan Nijeriya murnar Kirsimeti, ta yi kira a yi haɗin kai da tausayi
Murnar Kirsimeti da Sabuwar Shekara

Murnar Kirsimeti da Sabuwar Shekara

Murnar Kirsimeti da Sabuwar Shekara

Gwamnatin Tarayya ta taya jama’ar ƙasar nan, musamman mabiya addinin Kirista, murnar bikin Kirsimeti, inda ta bayyana lokacin a matsayin na ƙauna, sadaukarwa da kyakkyawar fata, tare da kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da nuna haɗin kai da tausayi duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya fitar a ranar Laraba.

A cewar Ministan, darussan da bikin Kirsimeti ke koyarwa suna tunatar da ’yan Nijeriya muhimmancin kula da juna, zama tsintsiya-maɗaurin-ki-ɗaya, da kuma ci gaba da yarda da makomar ƙasar nan, ko da a lokutan wahala.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana daraja juriya da jajircewar ’yan Nijeriya, tare da jaddada cewa ba za a raina haƙurin da suka yi ko wahalhalun da suka sha ba.

“Haƙuri da juriya da ’yan Nijeriya suka nuna ba za a ɗauke su da wasa ba, haka kuma zufa da gumin su ba zai tafi a banza ba,” inji sanarwar.

Ministan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ci gaba da maida hankali wajen gina Nijeriya mai tsaro, ƙarfi da wadata, wadda za ta amfani kowa da kowa.

Ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen tunawa da waɗanda suke fuskantar matsaloli a sassa daban-daban na ƙasar nan, tare da yin addu’a ga iyalan da hare-haren ta’addanci suka shafa.

Haka kuma, Idris ya buƙaci jama’a da su saka jami’an tsaro a addu’oin su, yana mai yaba wa jajircewar su wajen kare rayuka, dukiyoyi da ƙasar daga barazana iri-iri.

“Yayin da muke murnar wannan lokaci, mu tuna da waɗanda ke cikin ƙalubale, mu yi addu’a ga iyalan da hare-haren ta’addanci ya shafa, sannan mu riƙa tunawa da jami’an tsaron mu waɗanda ke ci gaba da kare rayukan mu, dukiyoyin mu da ƙasar mu daga kowace irin barazana,” inji shi.

Gwamnatin Tarayya ta kuma ƙarfafa ’yan Nijeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙara haɓaka zaman lafiya, tausayi, da haɗin kai a cikin gidajen su da al’ummomin su, tana mai cewa haɗin kan ƙasa muhimmin ginshiƙi ne na ci gaba da ɗorewar zaman lafiya.

Ya ce: “Mu yi amfani da wannan lokaci wajen inganta zaman lafiya, kyautatawa da haɗin kai a cikin gidajen mu da al’ummomin mu.”

Ya kammala da yi wa ’yan Nijeriya fatan murnar Kirsimeti cikin annashuwa da kuma sabuwar shekara mai albarka, tare da yin addu’ar Allah Ya albarkaci Nijeriya.

“Barka da Kirsimeti da kuma sabuwar shekara mai albarka. Allah Ya albarkace ku baki ɗaya. Allah Ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya,” inji sanarwar.

Tags: Bola Ahmed TinubuKirsimetiMohammedIdrisSabuwar Shekara
Previous Post

Bankwana da 2025: Shekarar da Harry Kane ya ci ƙwallaye 60 a Bayern, Mbappe ya ci 59 a Madrid

Next Post

Bankwana da 2025: Shekarar da farashin kayan abinci ya yi ragaraga da manoman Arewa

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Bankwana da 2025: Shekarar da farashin kayan abinci ya yi ragaraga da manoman Arewa

Bankwana da 2025: Shekarar da farashin kayan abinci ya yi ragaraga da manoman Arewa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!