• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Bankwana da 2025: Shekarar da farashin kayan abinci ya yi ragaraga da manoman Arewa

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
December 24, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Bankwana da 2025: Shekarar da farashin kayan abinci ya yi ragaraga da manoman Arewa
Manomi

Manomi

Maganar dai ɗaya ce tun daga kasuwar Pataskum har ta Bakori. Daga kasuwar Ɗandume har ta Shuwarin. Tun daga kasuwar hatsi ta Giwa har ta Sabuwa, Charanci, Badume, Maigatari da duk wata kasuwar da ake kai amfanin gona a sayar. Ba ka jin ana labarin darajar farashin amfanin gona, sai dai faɗuwar sa ragaraga.

Gero, dawa, wake, masara, gyaɗa, rogo, barkono, riɗi, albasa, shinkafa duk farashin su sai ƙara yin ƙasa yake yi a kullum.

Lamarin ya zama fuska biyu: A fuska ɗaya talakawan da ba noma suke yi ba, sai dai idan manoma sun noma su je su saya, murna suke ta yi da addu’a, Allah ya ƙara karya farashin kayan abinci. A ɗaya gefen kuma manoma sai kuka suke yi, saboda ganin cewa kashi 90 bisa 100 na manoman Arewa da suka yi noma a daminar bana, sun ɗibga gagarumar asara.

Wannan ce ta sa har a cikin makon da ya gabata, Majalisar Dattawa ta zartar da riƙon Shugaba Bola Tinubu ya dubi mummunan halin da manoma suka shiga, ya tallafa masu da ɗan abin da za su goge hawayen kukan da suke ci gaba da yi tun cikin damina, har yanzu bayan kaka ba su daina ba.

Wannan matsala da manoma suka afka, ta samo asali ne daga tsadar da amfanin gona ya yi a 2023 da kuma 2024. Ganin haka, sai Gwamnatin Tarayya ta cire waigin harajin kayan abincin da ake shigowa da shi daga waje. Hakan ya sa aka riƙa shigo da kayan abinci masu yawan da suka cika kasuwanni. Wannan ya tilasta saukar farashin kayan abinci sosai, har ta kai malejin tsadar rayuwa da malejin hauhawar farashi sun sauka ƙasa sosai, daidai aljihun talaka, a cikin 2025.

Manoman asali da manoman neman riba sun yi tunanin cewa kayan abinci zai sake tsada, kamar yadda ya yi a shekaru biyu da suka gabata. Sai kowa ya koma noma. Ko dai don ya noma wanda za a ci a gida, ya huta da saye, ko kuma domin ya sayar idan kayan gona sun yi tsada.

Sai dai abin bai zo wa manoma yadda suke so a 2025 ba. Domin tun a farkon damina suka fara ganin ba daidai ba. Sai da ta kai buhun takin zamani ya kai har kusan naira 60,000.

“To yanzu fa idan za ka sayi buhun takin zamani, sai ka kusan sayar da buhun masara uku. Har naira 21,000 ana sayar da buhun masara a cikin Disamba ɗin nan.” Inji Imamu Nuhu, wani manomin da bai ji daɗin daminar bana ba, saboda asarar da ya ce ya ɗibga.

Shi kuwa Junaidu Murnai ƙara nitso ya yi wajen yi wa wakilin mu bayanin wannan asara da manoma suka yi. Cewa ya yi, “kana ganin ana sayar da buhun masara naira 20,000 ko? To ina tabbatar maka, baya ga asarar kuɗin noma da na huɗa da na taki, duk buhun masara ɗaya kafin a kai shi kasuwa sai manomi ya yi masa wahalar naira 6,000 zuwa 7,000. Ka ga dai za a cire nasarar, ta tara wuri ɗaya, a cashe ta. A sayi buhuna a zuba. Duk ba kyauta leburori za su yi wa manomi ba.

“Daga nan za ka nemi mota ta ɗauko maka zuwa gida, ko a kai maka kasuwa. To a wannan ranar za ka san fetur ya yi tsada. Idan direba ya yanka maka kuɗin da za ka biya, sai ka ji kamar ka bar amfanin gonar a daji kawai, saboda baƙin ciki.”

Wata matsala da manoman ke fuskanta a yanzu ita ce, faɗuwar farashin kayan abinci ya sa ko sun kai kasuwa sun sayar, ba su iya biyan buƙatu na dole da na yau da kullum ɗin da suke son su biya. “Babu abin takaici kamar yadda wai sai ka sayar da tiya uku ta dawa za ka iya sayen tiyar garin kwaki ɗaya da kuɗin. Gaskiya da sakel.” Inji wani manomi a Garki, Jihar Jigawa.

A halin yanzu masu sayen abinci suna kimshewa sai ya yi tsada su sayar, su ma sun shiga taitayin su. Domin daminar bana an yi noma sosai, kuma a kullum sai fitar da shi a kasuwa ake yi. Babu wanda ya san yadda kasuwar hatsi za ta kasance nan da watanni bakwai da za a fuskanta. Tabbas idan ma ya nemi ya sake tsada, to gwamnati na iya karyar da shi, kamar yadda ta yi a 2025.

Saura abin da za a zura ido a gani, shin ko gwamnatin za ta dubi irin asarar da manoma suka yi har ta tallafa masu kamar yadda Majalisar Dattawa ta nemi ta yi?

Sai dai kuma da dama daga waɗanda suka maida noma kasuwanci, musamman masu karɓar hayar gonaki, ba za su sake gangancin yin noma a daminar 2026 ba. To akwai tsoron kada hakan ya haifar da ƙarancin abinci, nan da watanni goma masu zuwa.

Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta taya ’yan Nijeriya murnar Kirsimeti, ta yi kira a yi haɗin kai da tausayi

Next Post

Yadda fashewar bam ta kashe masallata a masallaci a Maiduguri – ‘Yan sanda

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Yadda fashewar bam ta kashe masallata a masallaci a Maiduguri – ‘Yan sanda

Yadda fashewar bam ta kashe masallata a masallaci a Maiduguri – ‘Yan sanda

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!