• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta nemi a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
November 20, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta nemi a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa
Nnamdi Kanu

Nnamdi Kanu

Bayan tabbatar da laifin da aka yi wa shugaban ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da ke tsare, Nnamdi Kanu, Gwamnatin Tarayya, a yau Alhamis, ta nemi kotu da ta yanke masa hukuncin kisa.

Babban lauyan gwamnati, Adegboyega Awomolo, SAN, shi ne ya yi wannan roƙo jim kaɗan bayan kotu ta samu Kanu da laifi a kan dukkan tuhumar ta’addanci guda bakwai da aka shigar a kan sa.

Masu gabatar da ƙara sun nace cewa yekuwar Kanu ta jawo mutuwar jami’an tsaro da dama da kuma lalata muhimman gine-ginen gwamnati, suna zargin cewa IPOB da ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Eastern Security Network (ESN), wanda ya bayyana a matsayin reshen yaƙi na ƙungiyar, sun ɗauki matakan da suka nufi tayar da hankalin ƙasa.

Ya ce wajabta hukuncin da ya fi tsanani shi ne kawai zai tabbatar da adalci ga waɗanda suka rasa rayuka da dukiyoyi sakamakon ayyukan ta’addancin Kanu.

A cewar sa, duk da cewa tuhuma ta 1, 2, 4, 5 da 6 suna ɗauke da hukuncin kisa, tuhuma ta 3 tana ɗauke da hukuncin shekaru 20 a gidan gyara hali, yayin da tuhuma ta 7 ke ɗauke da hukuncin shekaru biyar.

“Mai girma ya yi la’akari da irin nauyi da kuma tsananin laifukan ta’addancin da wanda aka yanke wa hukunci ya aikata a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da ke zama a Kudu-maso-gabas,” inji shi.

Bugu da ƙari, ya zargi Kanu da gaza nuna nadama ko tuba dangane da laifukan, yana mai cewa halayen sa a gaban kotu suna cike da girman kai.

Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta roƙi kotu da ta bayar da umurnin ƙwace dukkan kayan watsa shirye-shiryen da aka kama daga hannun Kanu, tare da hana shi samun damar amfani da na’urorin zamani ko intanet duk inda za a tsare shi don ya yi zaman hukunci.

Lauyan na gwamnati ya roƙi kotun cewa don kare lafiyar Kanu, kada a mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje a Abuja, wanda ya taɓa fuskantar fasa kurkuku a baya.

A halin da ake ciki, kafin kotu ta ɗage zaman zuwa ƙarfe 4:10 na yamma domin yanke hukunci, ta saurari roƙon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Ikwuano/Umuahia North and South, Hon. Obinna Aguocha, wanda ya roƙi kotu da ta sassauta hukunci.

Hukuncin kotun ya kawo ƙarshen shari’ar da aka yi wa Kanu tsawon fiye da shekaru 10.

Tags: Adegboyega AwomolohukunciIPOBkotuNnamdi Kanuta'addanci
Previous Post

Gargaɗi daga CBN: A guji yin hulɗa da Zuldal Microfinance Bank, ba shi da lasisi

Next Post

Babban Hafsan Sojoji ya je Borno, ya buƙaci dakaru da su ƙara jajircewa

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Babban Hafsan Sojoji ya je Borno, ya buƙaci dakaru da su ƙara jajircewa

Babban Hafsan Sojoji ya je Borno, ya buƙaci dakaru da su ƙara jajircewa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!