Shugaban jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, jiya ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da abin da ya kira farfaganda da ake yaɗawa game da rajistar jam’iyyar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta yi masu.
Tsohon gwamnan na Jihar Bayelsa ya kare sahihancin rajistar jam’iyyar, yayin da ya yi watsi da zarge-zargen rashin bin ƙa’ida da ake masu, tare da jaddada cewa an bi duk matakan da doka ta tanada.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a wani saƙo da ya wallafa a dandalin X, sanatan mai wakiltar Bayelsa ta Yamma ya ce kafa NDC ta samo asali ne tun daga shekarar 2017, saɓanin iƙirarin cewa an yi rajistar ta ne kwanan nan ba tare da cika sharuɗɗan doka ba.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da wani jagora a jam’iyyar All Democratic Alliance (ADA), Dakta Umar Arɗo, ya yi barazanar ƙalubalantar rajistar NDC ɗin a kotu bisa zargin karya ƙa’idoji.
Wannan ya faru ne a ranar da jam’iyyar ta bayyana cewa ta yi rajistar mambobi miliyan 10 cikin ƙasa da awa 48 bayan tsohon gwamnan Jihar Anambra, Mista Peter Obi; tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Musa Kwankwaso, da wasu jigajigan jam’iyyar ADC sun sauya sheƙa zuwa cikin ta a daren Lahadi.
NDC ta gudanar da tarukan jihohi (state congresses) jiya Litinin inda ta zaɓi kwamitocin zartarwa na jihohi, yayin da ADC da ɓangaren tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, suka musanta tattaunawar ƙawance da ita.
Dickson ya dage cewa bayyanar NDC sakamakon dogon tsari ne da aka shafe lokaci ana yi, yana mai cewa akwai takardu da ke tabbatar da hakan.
Ya ce: “Domin a fayyace, takardun mu sun nuna cewa mun fara neman rajistar NDC tun a 2017, kuma INEC ta amince a wancan lokacin kafin a dakatar da aikin. Lokacin da aka sake buɗe rajistar jam’iyyu bara, mun sabunta buƙatar da muka gabatar tun farko.”
Ya ƙara da cewa an ƙirƙiri jam’iyyar ne a matsayin dandali na aƙida wanda zai ɗore fiye da waɗanda suka kafa ta, tare da ba da gudunmawa ga cigaban kasa.
“Burin mu a NDC shi ne gina jam’iyyar siyasa mai aƙida wadda za ta ɗore har bayan waɗanda suka kafa ta zuwa shekaru masu zuwa,” inji Dickson.
Tsohon gwamnan ya kuma ce jam’iyyar tana ba matasa da mata muhimmanci sosai, yana bayyana ta a matsayin dandali mai haɗa kowa da kowa, koyarwa da hidima.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar tana ci gaba da samun goyon baya a faɗin ƙasar nan, sakamakon haɗuwar gogaggun ‘yan siyasa kuma masu tasiri a matakin ƙasa.
Ya ce: “Abin da muke gani a yanzu wata babbar haɗuwa ce… shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasa suna gangami a ƙarƙashin dandali guda.”
Yayin da ya amince cewa irin wannan babban shiri na siyasa yakan jawo suka, Dickson ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalin su, kada su bari a ruɗe su.
Ya ce: “Da gogewar da nake da ita a siyasa, na san cewa irin wannan aiki mai girma zai jawo hatsaniya—ji-ta-ji-ta, gulma, farfaganda har ma da ɓata suna. Don haka ina kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da irin waɗannan abubuwa.”
Ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su shiga jam’iyyar, su yi rajista tare da shiga harkokin siyasa.
Barazanar Arɗo
Sai dai kuma, Dakta Umar Arɗo ya sake bayyana damuwa kan abin da ya kira rashin bin ƙa’ida a rajistar NDC, har ya yi alƙawarin kai maganar kotu.
ADA tana daga cikin ƙungiyoyin siyasa 171 da suka nemi rajista a wurin INEC domin zama jam’iyyu.
A wani taron tuntuɓa da shugabannin jam’iyyu a Abuja a watan Fabrairu, shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa ƙungiyar Democratic Leadership Alliance (DLA) ce kaɗai aka yi wa rajista daga cikin ƙungiyoyi 171, yayin da aka yi rajistar NDC bisa umurnin kotu.
Ya ce an tantance ƙungiyoyin ne bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (da aka gyara), da Dokar Zaɓe ta 2022, da kuma dokoki da ƙa’idojin INEC na 2022.
Sai dai yayin wata hira da Trust TV, Arɗo ya zargi INEC da kauce wa ƙa’idojin ta ta hanyar yin rajistar wata jam’iyya wadda ba ta bi duk matakan tantancewa ba.
Amma a wata sanarwa, NDC, ta bakin sakataren ta na ƙasa, Ikenna Enekweizu, ta bayyana zargin Arɗo a matsayin na yaudara da ruɗani.
A ranar Lahadi dai, Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso sun shiga NDC bayan ficewa daga ADC, inda aka ba su katunan zama mambobi a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
A wata hira da DCL Hausa, Arɗo ya dage cewa rajistar NDC tana cike da kurakurai, yana mai cewa zai ɗaukaka ƙara.
Ya ce NDC ta samu rajista ba tare da bin ƙa’ida ba. Ya ce ba ta cika sharuɗɗan doka ba, kundin tsarin mulki ko ƙa’idojin INEC.
Ya ce ban da ADC ɗin, idan akwai wata jam’iyyar wadda aka yi wa rajista ba tare da cika sharuɗɗan ba, zai ƙalubalance ta a kotu.
A cewar sa, su a ADA sun cika dukkan sharuɗɗa, sun bi doka, amma aka ƙi yi masu rajista, don haka suka kai ƙara kotu.
Ya ce a Fabrairu 2026, INEC ta ce ta yi rajistar jam’iyyu biyu—ɗaya bisa tsarin ta, ɗaya kuma bisa umurnin kotu.
Ya ce baya ga wasiƙar niyya, NDC ba ta gabatar da cikakkiyar buƙatar rajista ba, ba a tantance ta ba, ba ta yi amfani da gidan yanar rajista na INEC ba, kuma ba ta gabatar da muhimman takardu kamar kundin tsarin mulki, manufofi ko jerin shugabanni ba, amma duk da haka kotu ta umurci a yi mata rajista.
Arɗo ya ƙara da cewa za su nemi haƙƙin su a kotu har sai an warware lamarin.
ADC da ɓangaren Atiku sun musanta tattaunawar sauya sheƙa
A gefe guda, jam’iyyar ADC da magoya bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar sun musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa suna tattaunawa kan sauya sheƙa zuwa NDC.
Mai ba Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya ce babu irin wannan tattaunawar.
“Idan akwai haka, ni ne zan fara sani. Ba na ganin akwai irin wannan magana,” inji shi.
Jami’an jam’iyyar ma sun ce babu wata tattaunawa da ke alaƙanta manyan ‘yan siyasar ADC da NDC, suna mai cewa rahotannin ba su da tushe.
Sakataren yaɗa labarai na ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce: “Ƙarya ce ɗari bisa ɗari.”
Duk da haka, rahotanni sun nuna ana zargin akwai tuntuɓa tsakanin manyan ‘yan siyasa a ADC da shugabannin NDC, tare da hasashen cewa za a iya ba da sanarwar wani mataki a tsakiyar wannan mako.
Bayan sauya sheƙar Peter Obi da Kwankwaso, ana kallon NDC a fagen siyasa a matsayin wata sabuwar mafaka ga masu neman sabon tsari a siyasar Nijeriya.






