Babban Hafsan Sojojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ja kunnen dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK) da su ci gaba da kasancewa cikin shiri, su guji sakaci, kuma su ci gaba da ɗaukar matsayi mai ƙarfi a cikin hare-haren da ake gudanarwa kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa-maso-gabas.
Shaibu ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya kai ziyara ta tantance ayyukan soji a Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa-maso-gabas (JTF NE OPHK) da ke Maiduguri.
Wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar ta bayyana cewa nufin ziyarar shi ne tantance yanayin tsaro, ƙimanta yadda ake gudanar da ayyuka, ƙarfafa daidaiton dabaru, da kuma ƙara haɗin kai da masu ruwa da tsaki domin tunkarar barazanar tsaro da ke ci gaba da addabar yankin.
Yayin da yake magana da dakarun, COAS ya yaba da jarumtaka da jajircewar su wajen fuskantar ‘yan ta’adda, yana mai kira gare su da su kasance masu himma, su ci gaba da zama cikin shiri, tare da kula da duk wani motsi don hana sababbin barazanar tasowa.
Ya jaddada buƙatar ci gaba da matsa ƙaimi a fagen aiki domin hana ‘yan ta’adda damar yin abin da suke so a ko’ina cikin yankin.

Shaibu ya kuma gana da manyan hafsoshin da ke cikin rundunar, inda ya jaddada muhimmancin sa ido mai ƙarfi, kyakkyawan tsare-tsare, samun sahihan bayanan leƙen asiri, da inganta yanayin gudanar da aiki domin ci gaba da samun nasarori a Operation Haɗin Kai.
Tun farko, kwamandan rundunar JTF NE OPHK, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya yi wa COAS bayani kan ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu, nasarorin da aka samu, da ƙalubalen da ake fuskanta a cikin yankin.
A wani ɓangare na ziyarar, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai ziyarar ban-girma ga COAS.
Gwamna Zulum ya taya Shaibu murna kan naɗin sa a matsayin Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na 25, yana mai cewa lallai ya cancanci wannan muƙami.
Ya nuna cewa Shaibu, wanda ya riƙe manyan muƙaman kwamandoji a wannan yankin, ya taka muhimmiyar rawa wajen rage matsalolin ta’addanci a yankin.

Zulum ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa COAS zai ci gaba da ɗorawa kan nasarorin da ake samu wajen kawar da ragowar ‘yan ta’adda domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a Jihar Borno da Arewa-maso-gabas baki ɗaya.
Ya tabbatar da aniyar gwamnati da mutanen Jihar Borno wajen ci gaba da haɗin kai da Sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro domin cigaban jihar, yankin da kuma ƙasa baki ɗaya.
Yayin da yake yaba wa gagarumin cigaban da dakarun OPHK suka samu, gwamnan ya buƙace su da kada su yi ƙasa a gwiwa saboda wasu matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu sassan jihar, sai dai su ci gaba da jajircewa da mayar da hankali.
A cikin martanin sa, COAS ya gode wa gwamnan saboda ziyarar, ya kuma yaba da haɗin kai mai ɗorewa da ke akwai tsakanin gwamnati da rundunar OPHK.
Ya tabbatar wa gwamnan da cewa Sojojin Nijeriya za su ci gaba da ƙara ƙaimi wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Borno da dukkan Arewa-maso-gabas.
Shaibu ya samu rakiyar manyan jami’an hafsoshin soji daga Hedikwatar Sojojin Ƙasa a wannan ziyarar tantance aiki.







