Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin duba tare da ƙara kuɗin rajistar jarabawar West African Senior School Certificate Examination (WASSCE) da kuma National Examinations Council (NECO) Senior School Certificate Examination (SSCE) na shekarar 2027.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar a ranar Litinin a Abuja.
A cewar ta, ma’aikatar ta janye wasiƙar da ta fitar ranar 18 ga Yuni, 2026, wadda ta bayyana shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar, domin ba da damar yin cikakken nazari tare da gudanar da faɗaɗɗiyar tuntuɓa da masu ruwa da tsaki kafin a yanke hukunci na ƙarshe.
Ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan damuwa da kuma shawarwari masu amfani da jama’a suka gabatar dangane da shirin ƙara kuɗin.
Ta ƙara da cewa shirin yin bitar kuɗin rajistar ya samo asali ne sakamakon matsin tattalin arzikin da ake ciki da kuma hauhawar kuɗaɗen gudanar da ingantattun jarabawar ƙasa.
Ta ce hauhawar kuɗin sufuri da jigilar kayayyaki, tsaro, buga takardun jarabawa, amfani da fasaha, tabbatar da inganci da sauran muhimman ayyuka ne suka sa aka gabatar da wannan shawara.
A cewar ta, Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya ba da umurnin dakatar da shirin, bisa manufar Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa duk wata manufa ta gwamnati ta kasance mai haɗa kowa da kowa, mai gaskiya kuma ta dogara da hujjoji.
Ta kuma ce ma’aikatar za ta gudanar da tuntuɓa da hukumomin shirya jarabawa, ma’aikatun ilimi na jihohi, masu makarantu da shugabannin su, ƙungiyoyin iyaye, ƙungiyoyin ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi a matsayin wani ɓangare na sabon tsarin bitar.
“Shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawa ba zai fara aiki ba kamar yadda aka sanar a baya, har sai an kammala wannan tsarin tuntuɓa,” inji ta.
Boriowo ta jaddada cewa jin daɗin ɗalibai, tabbatar da daidaiton damar samun ingantaccen ilimi da yanke shawara cikin gaskiya da adalci su ne ginshiƙan manufofin Gwamnatin Tarayya a fannin ilimi.
Ta gode wa ‘yan Nijeriya bisa fahimta, haƙuri da ci gaba da bayar da goyon baya, tana mai tabbatar da cewa za a ci gaba da sanar da jama’a yadda tattaunawar take gudana har zuwa kammaluwar ta.






