• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tasiri da alfanun umurnin CBN kan adana bayanan hadahadar kuɗi a cikin ƙasa

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
July 13, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

Makonnin baya ne dai Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umurci dukkan bankuna, kamfanonin fasahar kuɗi (fintechs) da sauran kamfanonin biyan kuɗi cewa su mayar da dukkan bayanan mu’amalolin su, wato ‘data’ daga cibiyoyin adana bayanai na ƙasashen waje zuwa cibiyoyin da ke cikin Nijeriya kafin nan zuwa ranar 1 ga Janairu 2027.

Wannan mataki yana nufin ƙarfafa ikon ƙasa kan bayanan ta, sauƙaƙa binciken hukumomi, rage dogaro da ƙasashen waje da kuma tabbatar da cewa kuɗaɗen da ake kashewa wajen amfani da sabis na girgije, wanda a Turance ake kira ‘cloud services’ sun ci gaba da zagayawa cikin tattalin arzikin Nijeriya.

Wannan umarni ya zo ne a lokacin da harkokin biyan kuɗi ta hanyar dijital suka zama ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar.

Bayanai daga Tsarin Hadahada Tsakanin Bankunan Nijeriya (NIBSS) sun nuna cewa darajar mu’amalolin kuɗi dijital ta kai sama da Naira Kwadriliyan 1.07 a shekarar 2024, tare da gudanar da fiye da mu’amaloli biliyan 11.2. Wannan yana nuna muhimmancin samun ingantattun cibiyoyin adana bayanai da za su iya ɗaukar wannan nauyin cikin ƙasa.

A halin yanzu, yawancin bankuna da kamfanonin ‘fintech’ suna amfani da manyan dandamalin girgije na ƙasashen waje kamar Amazon Web Service (AWS), Microsoft Azure, Google Cloud da IBM Cloud. Duk da haka, bankunan Nijeriya sun ci gaba da ƙara saka hannun jari a fasahar zamani, inda manyan bankuna goma suka kashe kusan biliyan naira biliyan 177.91 wajen inganta tsarin fasahar sadarwa, amfani da basirar ƙirƙira ta wucin gadi (AI), tsaro ta yanar gizo da kuma tsarin girgije a farkon watanni uku na shekarar 2026.

Masana masana’antar sun bayyana cewa umarnin CBN zai ƙarfafa ikon Nijeriya kan bayanan kuɗi, ya inganta tsaro, ya sauƙaƙa aikin hukumomin bincike da kuma jawo sabbin jarin gina cibiyoyin adana bayanai da sauran kayayyakin fasahar dijital.

Tuni dai a bayanan da muka buga a baya muka bayyana yadda masu gudanar da cibiyoyin adana bayanai suka ce sun shirya karɓar wannan nauyi da ƙalubale.

Shugaban kamfanin Open Access Data Centres (OADC), Ayotunde Coker, ya bayyana cewa shekaru da dama suna zuba jari wajen gina cibiyoyi masu inganci da za su iya karɓar bayanan bankuna da sauran manyan kamfanoni cikin ƙasa. Ya ce cibiyoyin da ake ginawa a yau suna da inganci iri ɗaya da na ƙasashen da suka ci gaba.

A yau, Nijeriya na da kusan cibiyoyin adana bayanai guda 26, ciki har da cibiyoyi 18 na kasuwanci da sauran cibiyoyi masu zaman kan su. Mafi yawan su suna Legas, yayin da wasu suke Abuja, Kano, Enugu da Fatakwal. Ƙarfin cibiyoyin kasuwancin da ake da shi yanzu yana tsakanin megawat 50 zuwa 56, kuma idan aka haɗa da waɗanda ake faɗaɗawa zai kai kusan megawat 124. Wannan ya sanya Nijeriya ta zama ta biyu mafi girman kasuwar cibiyoyin adana bayanai a Afrika, bayan Afrika ta Kudu.

Ana sa ran buƙatar irin waɗannan cibiyoyi za ta ci gaba da ƙaruwa sakamakon bunƙasar amfani da fasahar girgije, wato ‘cloud’, basirar wucingadi da kuma sabbin dokokin ajiye bayanai cikin ƙasa.

Masana sun yi hasashen cewa ƙarfin cibiyoyin na Nijeriya zai iya kai tsakanin megawat 210 zuwa 300 nan da shekarar 2030.

Sai dai masana sun bayyana cewa babban ƙalubalen ba shi ne ƙarancin gine-ginen cibiyoyin adana bayanai ba, sai dai ƙarancin manyan sabis na girgije da ake samarwa a cikin Nijeriya. Shugaban kamfanin Kasi Cloud, Johnson Agogbua, ya ce akwai isassun wuraren adana bayanai, amma ana buƙatar ƙarin kamfanonin girgije masu ba da sabis irin na AWS, Microsoft Azure da Google Cloud su kafa cibiyoyin su a Nijeriya.

Haka shi ma shugaban kamfanin OnePipe, Ope Adeoye, ya ce hanya mafi sauƙi ita ce a samar da yanayin da zai sa manyan kamfanonin girgije na duniya su kafa cibiyoyi a Nijeriya maimakon tilasta wa bankuna canja tsarin da suke amfani da shi gaba ɗaya.

A cewar sa, sauya tsarin adana bayanan bankuna ba aiki ba ne mai sauƙi domin yana buƙatar sake tsara manhajoji, gwada inganci, tabbatar da bin ƙa’idoji da kuma kauce wa katsewar ayyukan kuɗi.

Duk da ci gaban da aka samu, har yanzu akwai ƙalubale kamar samar da ingantacciyar wutar lantarki, tsarin sanyaya na’urori, hanyoyin sadarwa masu sauri da kuma ƙwararrun ma’aikatan da za su kula da manyan cibiyoyin fasaha. Duk da haka, masana sun yi imanin cewa tsofaffin bankuna sun fi shirye-shiryen aiwatar da wannan sauyi saboda sun taɓa gudanar da nasu cibiyoyin bayanai tun kafin amfani da tsarin girgije ya zama ruwan dare.

Masu gudanar da cibiyoyin adana bayanai sun kuma nuna cewa ci gaban keburan wayoyin intanet da ke ratsawa ƙarƙashin teku, irin su MainOne, Glo-1, WACS, ACE, Equiano da 2Africa, ya inganta sadarwar intanet a Nijeriya sosai. Wannan ci gaba ya ƙarfafa matsayin ƙasar wajen jawo manyan kamfanonin fasahar girgije su zuba jari a cikin gida.

Masana sun yi imanin cewa idan aka aiwatar da wannan manufa yadda ya kamata, za ta taimaka wajen dawo da ayyukan sarrafa bayanai da ake yi a ƙasashen waje zuwa Nijeriya. Hakan zai samar da sabbin guraben aiki, ya ƙara saka hannun jari a fannin fasahar dijital, ya rage jinkirin gudanar da mu’amaloli ta hanyar rage nisan da bayanai ke bi, sannan ya amfanar da gwamnati, kamfanonin sadarwa, lafiya, ilimi da masana’antu baki ɗaya.

An kuma nuna damuwa cewa yawancin cibiyoyin adana bayanai suna Legas, lamarin da ka iya zama haɗari idan wata matsala ta afku a birnin. Sai dai masu ruwa da tsaki sun ce ana ci gaba da faɗaɗa cibiyoyi zuwa Abuja, Kano da Fatakwal, yayin da cibiyoyin da ake da su ke da hanyoyin kariya da madadin aiki da ke rage yiwuwar tangarda.

Masanin fasahar bayanai Olubayo Adekambi ya bayyana cewa bayanan mu’amalolin kuɗi yanzu sun zama wani muhimmin ɓangare na tsaron ƙasa saboda suna taimakawa wajen yaƙi da zamba, safarar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifukan kuɗi.

Ya ce duk da matsalolin wutar lantarki da faɗaɗa intanet, bai kamata hakan ya hana Nijeriya ƙarfafa ikon ta kan muhimman bayanan kuɗin ta ba.

A ƙarshe, masana sun bada shawarar cewa wasu na ganin lokacin da CBN ya bayar ba shi i da yawa, domin cibiyoyin kuɗi na da kusan watanni shida kacal su kammala ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen fasaha da aka taɓa yi a tarihin tsarin kuɗin Nijeriya. Duk da haka, sun ce cibiyoyin da suka fara shirye-shirye tun yanzu za su iya cika wa’adin cikin sauƙi, yayin da waɗanda suka yi jinkiri za su fuskanci ƙalubale wajen bin umarnin kafin ranar 1 ga Janairu 2027.

Tags: bankunaCBN
Previous Post

Yadda Shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ ya Sauya Zancen Ayyukan Gwamnatin Tarayya a Arewa

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ƙulla yarjejeniya ta farko a tarihi domin kawo ƙarshen yawan yajin aiki a jami’o’i

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!