• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai don farfaɗo da Maɗaba’ar Gwamnati da aka yi watsi da ita, bayan shekaru ana tafka asara

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
December 18, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai don farfaɗo da Maɗaba’ar Gwamnati da aka yi watsi da ita, bayan shekaru ana tafka asara
Hagu zuwa dama: Babban Sakatare na Dindindin, Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, Ogbodo Chinasa Nnam; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Darakta, Maɗaba’ar Gwamnati ta Tarayya, Hajiya Ahmed Hajarat Mustapha, yayin ziyarar duba aikin Maɗaba’ar Gwamnati (Federal Government Printer) a Asokoro, Abuja, a yau

Hagu zuwa dama: Babban Sakatare na Dindindin, Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, Ogbodo Chinasa Nnam; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Darakta, Maɗaba’ar Gwamnati ta Tarayya, Hajiya Ahmed Hajarat Mustapha, yayin ziyarar duba aikin Maɗaba’ar Gwamnati (Federal Government Printer) a Asokoro, Abuja, a yau

Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki tsauraran matakai domin kawo ƙarshen shekaru na asara da sakaci bayan Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, ya kai ziyarar duba Maɗaba’ar Gwamnati da aka daɗe da yin watsi da ita a Abuja, a yau Alhamis.

A yayin ziyarar, Ministan ya bayyana matuƙar damuwa game da halin da wurin yake ciki.

Ya bayyana cewa watsi da kamfanin ya jawo asarar biliyoyin naira, wanda abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma ya saɓa wa sabon mayar da hankali da Gwamnatin Tarayya ke yi kan tanadi, ɗaukar mataki da kuma amfani da dukiyoyin jama’a yadda ya dace, a ƙarƙashin Manufar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ministan ya tuna cewa an aza tubalin ginin cibiyar tun a shekarar 2001 a zamanin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo, inda ya bayyana cewa aikin ya kai kusan kashi 70 cikin 100 na kammalawa, tare da samar da manyan na’urorin ɗab’i tun a shekarar 2007.

Abin mamaki kuma, yawancin injinan da aka shigo da su daga ƙasashe irin su Jamus da Indiya har yanzu ba a buɗe su daga akwatunan su na asali ba fiye da shekara goma, inda wasu daga cikin fasahohin su ma suka zama tsofaffi sakamakon dogon sakaci.

Ya ce: “Abu ne mai taɓa zuciya ganin irin wannan asara a tsakiyar Abuja,” inji Ministan, yana mai cewa, “A daidai lokacin da gwamnati take ƙoƙarin tanadin albarkatu da dogaro da kai, abin ba zai yiwu ba a bar irin wannan babban jari ya lalace shekara da shekaru.”

Maɗaba’ar Gwamnati, wadda ke aikin bugun takardun Gwamnatin Tarayya, ita ce ke da alhakin gurza muhimman takardun ƙasa, ciki har da Jaridar Gwamnatin Tarayya (Federal Government Gazette) da sauran muhimman wallafe-wallafen Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.

Ministan ya ce tsawon lokacin da maɗaba’ar ta tsaya ba tare da aiki ba ya tilasta gwamnati ta riƙa fitar da ayyukan ɗab’i zuwa waje, alhali ya kamata a yi su a cikin gida, lamarin da ke rage inganci da ƙarfin ƙasa.

Binciken ya kuma nuna cewa muhimman kayayyakin more rayuwa a wurin, ciki har da sabon janareta mai ƙarfin 2000 KVA da aka girka tun a shekarar 2011, bai taɓa aiki ba, wanda ke nuna yadda aka bar dukiyoyin jama’a ba a amfani da su.

Ministan ya samu rakiyar Babban Sakatare na Dindindin, Daraktan Riƙo da ke kula da sashen, da sauran manyan jami’an ma’aikatar.

Ministan ya bayyana cewa sun yi ziyarar ne domin shugabanni su ga halin da ake ciki da idon su, su yi cikakken nazari, sannan su yanke sahihan shawarwarin gudanarwa.

Ya ce: “Mun zo ne domin mu gani da idon mu. Za mu koma mu gabatar da shawarwari masu ma’ana ga Mai Girma Shugaban Ƙasa da Majalisar Zartarwa ta Tarayya kan mafi kyawun hanyoyin farfaɗo da wannan Maɗaba’ar Gwamnati tare da amfani da ita domin amfanin ‘yan Nijeriya.”

Ministan ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta ci gaba da yin shiru kan lalacewar dukiyoyin ƙasa ba, inda ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakai masu ƙarfi domin dawo da darajar jarin da aka riga aka zuba da kuma hana ƙarin asara.

Ya kuma sake jaddada ƙudirin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na gaskiya, kyakkyawan shugabanci da ingantaccen sarrafa albarkatun jama’a, bisa ga umurnin Shugaba Tinubu na cewa duk nairar da aka kashe dole ne ta haifar da wani amfani ga ‘yan Nijeriya.

Tags: Federal Government PrinterMadaba'ar Gwamnatin TarayyaMohammed Idrisziyara
Previous Post

Kotu ta sake hana ’yan sanda aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu

Next Post

Gwamnan Filato, Mutfwang, ya koma APC daga PDP

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Gwamnan Filato, Mutfwang, ya koma APC daga PDP

Gwamnan Filato, Mutfwang, ya koma APC daga PDP

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!