• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Gwamnan Filato, Mutfwang, ya koma APC daga PDP

ALI KANO by ALI KANO
December 19, 2025
in Siyasa
A A
0
Gwamnan Filato, Mutfwang, ya koma APC daga PDP
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin ƙasar nan ta bada sanarwar cewa Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya yi sauyin sheƙa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Shugaban APC na Ƙasa, Nentawe Yelwata, wanda shi ma ɗan Jihar Filato ne, shi ne ya bayyana sauyin sheƙar gwamnan a taron ƙolin jam’iyyar na ƙasa karo na 14 wanda aka gudanar a Zauren Taron Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Yelwata ya ce da sauyin sheƙar Gwamna Mutfwang, yanzu dukkan yankin Arewa ta Tsakiya yana ƙarƙashin mulkin APC.

An zaɓi gwamnan a ƙarƙashin PDP a babban zaɓen 2023, kuma ya zama sabon ɗan siyasar da ya shahara da ya fice daga babbar jam’iyyar adawa.

A wajen taron, shugaban APC ya bayar da wa’adin ranar 30 ga Janairu, 2026, ga dukkan membobin jam’iyyar domin su kammala rajistar zama memba ta hanyar intanet.

Ya ce fara aiki da tsarin rajistar intanet, wanda tuni aka soma, zai ƙara tsare gaskiya, ingancin bayanai da dimokiraɗiyyar cikin gida a jam’iyyar.

Ya ce: “Mun yi horo a matakin jiha, mun yi a matakin shiyya, mun kuma yi a ƙananan hukumomi a yawancin jihohi. Kuma ina kira ga masu ruwa da tsaki da su goyi bayan ƙaddamar da wannan muhimmin aiki a faɗin ƙasar nan.

“Mu yi amfani da wannan dama wajen tabbatar wa sababbin membobi cewa suna da dukkan haƙƙoƙi da gata a cikin jam’iyyar, mu kuma ƙarfafa masu gwiwa su yi amfani da rajistar membobi ta ƙasa domin su yi wa magoya bayan su rajista. Don haka tsofaffi da sababbin membobi su shiga shafin rajista su yi wa dukkan membobin su rajista.

“Muna sa ran a kammala wannan aiki daga yanzu zuwa ƙarshen Janairu, wato ranar 30 ga Janairu. Dole ne dukkan membobi su yi rajista tare da shirye-shiryen tunkarar tarukan jam’iyya (congresses) da ke tafe.”

Taron ya samu halartar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, manyan shugabannin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo.

Haka kuma, gwamnonin APC da suka halarta sun haɗa da Peter Mbah na Inugu, Douye Diri na Bayelsa, Agbu Kefas na Taraba, da Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, wanda kwanan nan ya koma APC, tare da tsofaffin gwamnonin jihohi, shugabannin jam’iyya na ƙasa, da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Tags: APCCaleb MutfwangFilatoNentawe YelwataPDP
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai don farfaɗo da Maɗaba’ar Gwamnati da aka yi watsi da ita, bayan shekaru ana tafka asara

Next Post

Kasafin 2026: Tinubu ya ba sha’anin tsaro, kiwon lafiya, noma, ilimi da ababen more rayuwa muhimmanci na musamman

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Kasafin 2026: Tinubu ya ba sha’anin tsaro, kiwon lafiya, noma, ilimi da ababen more rayuwa muhimmanci na musamman

Kasafin 2026: Tinubu ya ba sha'anin tsaro, kiwon lafiya, noma, ilimi da ababen more rayuwa muhimmanci na musamman

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!