Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wasu sababbin taraktocin noma guda 2,000 domin bunƙasa aikin noma na zamani a fadin kasar nan, tare da manufar noma sama da hekta miliyan 1.5 a duk shekara.
Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, shi ne ya bayyana hakan yayin bikin ƙaddamar da shirin a ranar Litinin a Abuja, inda ya ce wannan mataki wani gagarumin sauyi ne a ɓangaren noma ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cewar sa, an ƙaddamar da shirin ne a ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya na Renewed Hope National Agricultural Mechanisation Programme, wanda zai samar da taraktoci masu ƙarfin aiki tare da na’urorin noma sama da 9,000 domin inganta yawan amfanin gona.
Ya bayyana cewa za a fara da tura taraktoci 600 a mataki na farko, sannan a biyo da wasu 750 da kuma 650 a matakai na gaba har a kai ga cika adadin 2,000 a fadin ƙasar nan baki ɗaya.
Ministan ya ƙara da cewa ba za a bai wa mutane taraktocin a matsayin mallaka kai tsaye ba, sai dai za a mika su ga masu samar da ayyukan injinan noma (Mechanisation Service Providers), inda kowace na’ura za ta iya noma kusan hekta 600 a shekara.
Ana sa ran shirin zai taimaka wa manoma sama da miliyan 1.2 a duk faɗin Nijeriya, tare da inganta samar da abinci da kuma bunƙasa tattalin arzikin karkara.
Haka zalika, ya ce gwamnatin ta samar da asusun tallafin noma na Niira biliyan 50 ta hannun Bankin Masana’antu domin sauƙaƙa harkokin zuba jari a fannin noma, yayin da aka kuma tanadi Naira biliyan 250 domin tallafa wa ƙananan manoma miliyan ɗaya a daminar shekarar 2026.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta shirya samar da motocin gyaran taraktoci guda 36, da kuma gina cibiyoyin kula da injinan noma guda bakwai a sassan ƙasar nan, tare da shirin kafa babbar masana’antar haɗa taraktoci da za ta riƙa samar da tsakanin guda 2,000 zuwa 4,000 a duk shekara.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage wahalar aikin noma, da kuma kara yawan amfanin gona domin tabbatar da wadatar abinci a ƙasar nan.







