A ci gaba da ƙoƙarin saisaita tattalin arzikin Nijeriya da Babban Bankin Nijeriya ke yi, Membobin Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗi na CBN sun tashi daga taron su na 307 da aka gudanar a ranar 22 ga Satumba, inda suka yanke shawarar rage kuɗin ruwa na lamuni, daga kashi 26.5 zuwa kashi 23 bisa 100.
Ana sa ran wannan sabon sauyin manufofin zai yi tasiri ga karɓar rance, shawarwarin zuba jari da kuma harkokin kuɗin gidaje, yayin da ’yan kasuwa da masu amfani da kayayyaki ke sa ido kan tasirin ragewar ga tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.
CBN ya kuma yanke shawarar cewa bankunan kasuwanci za su ci gaba da ajiye kashi 45 cikin 100 na kuɗaɗen ajiyar abokan cinikin su a CBN, yayin da bankunan ‘yan kasuwa (merchant banks) za su ajiye kashi 16 cikin 100.
Tuni dai Ƙungiyar Masu Ba da Aiki ta Nijeriya (NECA) da Cibiyar Inganta Kamfanoni Masu Zaman Kan su (CPPE) suka nuna gamuwa kan wannan matakin da CBN ya ɗauka.
Sai dai sun yi gargaɗin cewa nasarar rage kuɗin ruwan za ta dogara matuƙa ne kan yadda bankunan kasuwanci za su gaggauta mayar da raguwar kuɗin ruwa na manufofin CBN zuwa raguwar kuɗin rancen da suke bayarwa.
Shawarwarin CBN sun nuna sabon yunƙuri na inganta yadda manufofin kuɗi ke shafar tattalin arziki.
Yayin da matakin ke sauya tsarin iyakar gejin kuɗin ruwa na manufofin kuɗi, CBN ya dage cewa hakan ba yana nufin an sauya ainihin alƙiblar manufofin kuɗi ba ce.
Maimakon haka, CBN na neman ƙarfafa yadda shawarwarin sa ke ratsawa zuwa kasuwar kuɗi, inganta tasirin tsarin manufofin sa da kuma tallafa wa ƙoƙarin Nijeriya zuwa tsarin saita manufofin hauhawar farashi.
An ɗauki wannan mataki ne a daidai lokacin da hauhawar farashi ke raguwa, ajiyar kuɗin waje ke ƙaruwa, tattalin arziki ke samun ci gaba kuma ake samun ƙarin ƙwarin gwiwa kan ɓangaren tattalin arzikin ƙasar bisa tsarin hulɗa da ƙasashen waje.
Sai dai matakin ya kuma zo a lokacin da rashin tabbas a tattalin arzikin duniya, rikice-rikicen siyasa da tsaro a duniya da kuma yiwuwar ƙarin kashe kuɗi da ya shafi zaɓe ke ci gaba da haifar da ƙalubale ga makomar tattalin arziki.
Kwamitin Manufofin Kuɗi MPC na ba da haske kan yadda CBN ke daidaita buƙatar ci gaba da rage hauhawar farashi da kuma babban burin tallafa wa ayyukan tattalin arziki.
Abin da sabon tsarin manufofin ke nufi ga tattalin arziki:
Sabuwar shawarar MPC ta mayar da hankali ne kan inganta tsarin da ake amfani da shi wajen gudanar da manufofin kuɗi.
Maimakon sanar da wani sabon sauyi a cikin kuɗin ruwa, CBN ya fi mayar da hankali ne kan sake tsara iyakar kuɗin ruwa da kuma ƙarfafa matsayin MPR a matsayin babban siginar manufofin kuɗi.
Sakamakon zai dogara ne kan yadda wannan gyara zai inganta alaƙar da ke tsakanin shawarwarin CBN da kuɗin ruwa na kasuwa.
Ga bankuna da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwar kuɗi, wannan iyaka tana samar da tsarin kula da yawan kuɗaɗen da ake samu a ɗan gajeren lokaci.
Ga ’yan kasuwa da gidaje, babban tasirin zai dogara ne kan yadda sauye-sauyen kuɗin ruwa a kasuwar kuɗi za su shafi yanayin bayar da lamuni, shawarwarin zuba jari da samun damar karɓar rance.
Alƙawarin CBN na duba tasirin sabon gejin kuɗin ruwa ya nuna cewa za a ci gaba da sa-ido kan sabon tsarin na tsawon lokaci.
Kwamitin ya ce shawarwarin da za a ɗauka nan gaba za su ci gaba da dogara kan bayanan tattalin arziki, da nufin ci gaba da tsarin rage hauhawar farashi.
Wannan tsari na nufin cewa shawarwarin manufofin da za a ɗauka daga baya za su kasance bisa la’akari da sauye-sauyen hauhawar farashi, ci gaban tattalin arziki, farashin canjin kuɗi, yawan kuɗaɗen da ke yawo da sauran muhimman alamomin tattalin arziki.
A wurin CBN, raguwar hauhawar farashi na bada shaida cewa tsauraran matakan manufofin kuɗi da aka ɗauka a baya da kuma daidaiton farashin canjin kuɗi suna taimakawa wajen rage saurin hauhawar farashi.
Haka kuma raguwar saurin hauhawar farashi, na nufin farashin kayayyaki ba lallai ne su ragu ba; a maimakon haka, suna ƙaruwa ne da sauri ƙasa da yadda suke ƙaruwa a baya.
Ci gaban tattalin arziki ya ƙara wa CBN ƙwarin gwiwa:
Tattalin arzikin Nijeriya ya samu ƙarin ci gaba a zango na biyu na shekarar 2026, domin gejin ƙarfin tattalin arzikin cikin gida (GDP) ya ƙaru da kashi 4.43, idan aka kwatanta da kashi 3.89 a zangon da ya gabata.
An samu wannan ci gaba ne sakamakon ƙarin ayyuka a ɓangarorin man fetur da waɗanda ba na man fetur ba.
CBN ya danganta wannan ci gaba musamman da ƙarin ayyuka a fasahar sadarwa da bayanai, amfanin gona, gidaje da kadarori, kiwon dabbobi, ayyukan kuɗi da kasuwanci.
Kwamitin ya danganta wannan ci gaba da ƙarin hako ɗanyen mai da kuma zuba jari a ɓangaren. Kwamitin ya kuma yi nuni da nasarar shirin ƙarfafa jarin bankuna.
A cewar MPC, shirin ya ƙarfafa ajiyar jarin bankuna, juriyar su da kuma damar ba da kuɗin gudanar da manyan ayyuka a muhimman ɓangarorin tattalin arziki.
Bankunan da suka ƙara ƙarfafa jarin su na iya samun ƙarin damar tallafa wa ’yan kasuwa da ayyukan more rayuwa, duk da cewa ainihin sakamakon bayar da lamuni zai dogara ne kan haɗarin rashin biyan bashi, ƙarfin masu karɓar rance, kuɗin ruwa da sauran yanayin tattalin arziki.







