Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da naɗa Olayemi Cardoso matsayin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, inda ya nemi Majalisar Tattawa ta amince da shi, a matsayin madadin Godwin Emefile da aka cire.
Bayan sati biyu sai Majalisar Dattawa ta amince da naɗin Cardoso, tare da amincewa da sunayen wasu mutum huɗu da za su kasance mataimaka ga gare shi a tsawon wa’adin shekara biyar da zai yi a CBN. Duk da dai Shugaba Tinubu zai iya ƙara masa wa’adin wasu shekaru biyar ɗin idan ya gamsu da tasirin ayyukan sa a CBN.
Cikin shekaru uku bayan da Cardoso ya zama Gwamnan CBN, yanayin harkokin kuɗi na ƙasar nan ya sauya sosai. Bankuna sun ƙara ƙarfi ta fuskar jari, kasuwar canjin kuɗin waje ta ƙara zama mai gaskiya da bayyana, biyan kuɗi ta hanyar fasahar zamani ya ƙara samun tsaro, yayin da ajiyar kuɗin ƙasar waje ta kai matakin da ba a taɓa gani ba kusan tsawon shekaru 17.
Yayin da Olayemi Cardoso ke cika shekaru uku a matsayin shugaban CBN, an aiwatar da manyan sauye-sauyen manufofin kuɗi, tsauraran matakan daidaita harkokin kuɗi, tare da muhawara mai ƙarfi a tsakanin jama’a. Daga ƙarshen shekarar 2023 zuwa 2026 ya sauya alƙiblar tattalin arziki zuwa manufofin kuɗi na gargajiya da suka fi dacewa da ƙa’idojin tattalin arziki, duk da cewa ra’ayoyi sun rabu matuƙa kan tsadar da waɗannan sauye-sauye suka jawo wa al’umma da tattalin arziki. Amma dai an haƙƙaƙe cewa hakan shi ne mafi alfanu.
Jadawalin nasarorin da CBN ya fitar ya nuna waɗannan sauye-sauye sun sa Shugaba Bola Tinubu ya yaba da aikin Cardoso, sannan ya samu karramawa daga ƙasashen waje da cikin gida.
Karramawar baya-bayan nan ita ce lambar yabo ta Gwarzon Bankin Shekara daga Babban Bankin Landan. Cardoso ya kuma samu lambar yabo a taron shekara-shekara jaridar Blueprint, wanda aka gudanar a ranar 18 ga Agusta, 2026, a Cibiyar Taro ta Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Abubuwan da CBN ya ce ya cimma a ƙarƙashin jagorancin sa ya isa ya nuna irin sauye-sauyen da aka samu.
Ƙarfafa Jari Da Inganta Tsarin Bankuna:
Babban ginshiƙin sauye-sauyen bankuna shi ne kammala shirin ƙara jari a ranar 31 ga Maris, 2026. Bankuna 33 sun cika sabbin ƙa’idojin mafi ƙarancin jari, inda suka tara kusan naira tiriliyan 4.65 a matsayin sabon jari. Kimanin kashi 72.55 cikin 100 na wannan kuɗi ya fito ne daga cikin gida, abin da ke nuna amincewar masu zuba jari na cikin gida ga harkar banki. CBN ya ce wannan shiri ya ƙara wa bankunan Nijeriya ƙarfin jure wa matsaloli tare da ba su damar samar da kuɗin da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
An kuma mayar da hankali kan shugabanci. A watan Satumba na 2025, CBN ya gabatar da tsarin sauyin shugabannin manyan bankunan da ake kira DSIBs, wato bankunan da gazawar su za ta iya jefa tsarin kuɗin ƙasa baki ɗaya cikin haɗari. Manufar hakan ita ce tabbatar da cewa sauyin shugabanci a manyan bankunan ba zai kawo cikas ga zaman lafiyar tsarin kuɗi ba.
A watan Fabrairu na 2026, CBN ya amince da kafa tsarin bada lamuni babu ruwa ga Bankin Masana’antu na Nijeriya, domin faɗaɗa damar samun wasu nau’o’in kuɗaɗen tallafi da kuma inganta harkokin samar da kuɗi ga masu ƙaramin ƙarfi.
Faɗaɗawa Da Ƙara Bayyana Ingancin Kasuwar Canjin Kuɗin Waje:
Gyaran kasuwar canjin kuɗin waje ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da aka fi sa-ido a kan su yanzu a zamanin Cardoso, kuma CBN ya ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a shekarar 2026.
A ranar 15 ga Mayu, 2026, ya ƙaddamar da bugu na huɗu na Kundin Bayanan Canjin Kuɗi, wato kundin ƙa’idojin canjin kuɗin waje, wanda aka tsara domin inganta gaskiya, inganci, amana da kuma gudanar da harkokin canjin kuɗin waje bisa yanayin kasuwa.
An kuma ƙara shigar da masu gudanar da harkokin canji, wato ‘Bureau de Change’ (BDC) cikin tsarin hukuma. Yanzu kamfanonin BDC masu lasisi suna samun kuɗin waje ta hannun bankuna masu izini, tare da amfani da BDC ‘Purchase Tracker’, wannan kuwa wani tsari da ke ƙara bayyana gaskiya, bin ƙa’idoji da sa ido kan harkokin sayen kuɗin waje a lokaci guda.
A ranar 25 ga Maris, 2026, an bai wa kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa damar mayar da kashi 100 cikin 100 na kuɗaɗen da suka samu daga fitar da mai zuwa ƙasashen su ta hannun bankunan da ke da izini.
CBN ya ce wannan mataki ya ƙara sassauta kasuwar canjin kuɗin waje.
Haka nan kuma CBN mayar da hankali kan kuɗaɗen da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ke turowa cikin gida Nijeriya.
A ranar 24 ga Maris, 2026, ya gabatar da buƙatar da za ta tilasta masu hadahadar masayar kuɗaɗen waje daga wannan ƙasa zuwa waccan, wato ‘International Money Transfer Operators’ (IMTOs) yin sulhu da biyan kuɗaɗen da suka karɓa da kuɗin naira, domin ƙara bayyana gaskiya da kuma sauƙaƙa bin diddigin kuɗaɗen da ake turawa daga ƙasashen waje.
Domin ƙarfafa sa-ido kan fitar da man fetur da iskar gas zuwa ƙasashen waje, an ware wasu ƙarin tashoshin fitar da ɗanyen mai a shekarar 2026, abin da ke taimakawa wajen inganta bin ƙa’idoji a dukkan matakan harkar.
Sauya Tsarin Biyan Kuɗi Ta ta Hanyar Fasahar Zamani:
Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi amfani da tsarin biyan kuɗi ta hanyar fasahar zamani, kuma CBN ya yi ƙoƙarin sanya wannan tsarin ya ƙara zama mai tsaro da kuma isa ga mutane da dama.
An kafa Kwamitin ‘PSV 2028’ a ranar 9 ga Satumba 2025, sannan aka ƙaddamar da shi dai wannan tsari da ake kira ‘Payments System Vision’ 2028 a ranar 1 ga Yuni, 2026. Tsarin ya ginu ne kan ginshiƙai shida: haɗin kai tsakanin tsarin biyan kuɗi, tsaro, samar da damar shiga tsarin, ƙirkire-ƙirkire, amana da haɗin gwiwa.
Manufar sa ita ce mayar da tsarin biyan kuɗin Nijeriya ya zama mafi tsaro kuma ya haɗu sosai da tattalin arzikin dijital na duniya.
An kuma ɗauki matakai kan mu’amalolin Point-of-Sale (PoS) a shekarar 2026, ta hanyar ƙara amfani da tsarin tantance wurin gudanar da mu’amala da kuma buƙatar na’urorin su kasance da hanyoyin sadarwa guda biyu. Manufar ita ce inganta iya bin diddigin mu’amaloli, juriya da kuma ingancin tsarin.
Waɗannan duk kaɗan ne daga cikin ayyukan ci gaban tattalin arziki da Cardoso ya samar a shekarun sa yana Gwamnan CBN, akwai wasu da yawa da aka bayyana a shekarar 2025 da 2026 ɗin nan, waɗanda an sha karanta su a baya.







