• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
September 13, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Olayemi Cardoso, ya bayyana lambar yabo ta musamman Ƙungiyar Tattalin Arzikin Nijeriya (NES) ta bai wa CBN a matsayin tabbaci na ingancin manufofin da bankin ya aiwatar, da kuma ƙoƙarin sa na tabbatar da daidaiton tattalin arzikin ƙasa.

NES ta damƙa kyautar ga CBN ne a taron shekara-shekara na 67 na NES, wanda aka gudanar a Abuja daga ranar 7 zuwa 10 ga Satumba, 2026.

Daraktan Sashen Manufofin Kuɗi na CBN, Dakta Victor Oboh, shi ne ya karɓi kyautar a madadin CBN.

Karramawar dai ta zo a daidai lokacin da CBN ke aiwatar da jerin sauye-sauye a fannoni da suka haɗa da manufofin kuɗi, kasuwar musayar kuɗaɗen waje da kuma harkokin kuɗi a cikin shekaru uku da suka gabata.

Daga cikin matakan da NES ta yaba da su akwai sauye-sauyen da aka yi a kasuwar musayar kuɗaɗen waje, biyan tsoffin basussukan da suka shafi kuɗaɗen waje na biliyoyin daloli, dakatar da amfani da tsarin da CBN ya riƙa ɗirka wa gwamnatin tarayya bashi, wato ‘Ways and Means’, aiwatar da Burin Tsarin Biyan Kuɗi na 2028 (PSV 2028) da kuma nasarar ƙarfafa jarin bankuna.

A cewar ƙungiyar, waɗannan matakai na nufin samar da ingantaccen tsarin kuɗi mai ƙarfi, juriya ga matsaloli da kuma iya yin gogayya a matakin tsarin kuɗi ko ƙalubale a duniya.

NES ta kuma lura da samun ci gaba a wasu muhimman alamomin tattalin arziki, ciki har da raguwar matsin hauhawar farashi, ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasa da kuma ƙarin daidaito a kasuwar musayar kuɗaɗen waje.

Ƙungiyar ta ce tazarar da ke tsakanin farashin kuɗaɗen waje a kasuwar hukuma da ta bayan fage ta ragu zuwa ƙasa da kashi biyu cikin 100, yayin da aka samu ci gaba wajen shigowar kuɗaɗen da ’yan Nijeriya ke aikowa daga ƙasashen waje, ƙarin yawan zuba jari daga ƙasashen waje da kuma amincewar masu zuba jari ga tattalin arzikin ƙasar.

CBN ya danganta waɗannan sauye-sauye da matakan manufofin da yake ci gaba da aiwatarwa, waɗanda aka tsara domin dawo da amincewa da tattalin arzikin ƙasa tare da ƙarfafa tsarin kuɗi da na hadahadar kuɗaɗen Nijeriya.

Karramawar NES ta zo ne bayan CBN ya samu lambar yabo ta Gwarzon Banki na Duniya, shaidar da ke ƙara nuna yadda ake gane sauye-sauyen da bankin ke aiwatarwa da kuma manufofin sa.

Da yake magana kan kyautar, Cardoso ya bayyana ta a matsayin amincewa da jajircewar CBN wajen tabbatar da nagarta, ƙarfafa tsarin hukumomi da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.

Gwamnan ya ce: “Kyautar Girmamawa ta NES shaida ce kan jajircewar Babban Bankin Nijeriya wajen neman nagarta, ƙarfafa juriyar hukumar sa da kuma sadaukar da kai ga ci gaban ƙasa.”

Ya ƙara da cewa kyautar ta ƙara ƙarfafa aniyar bankin wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki, samar da ingantaccen tsarin kuɗi da kuma bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa.

Cardoso ya ce: “Yayin da yake ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da kuma samar da sabbin hanyoyi domin cika nauyin da aka ɗora masa, CBN zai ci gaba da jajircewa wajen gina tattalin arziki mai ƙarfi da kuma kyakkyawar makoma ga Nijeriya.”

Tags: Babban Bankin Nijeriya (CBN)lambar yaboMista Olayemi CardosoNES
Previous Post

Sarkin Lafiya ya yaba wa Bago kan nasarorin da yake samu a Neja

Next Post

Cewar Sarkin Zazzau: An yi wa rawar da El-Rufai ya taka wajen naɗa ni sarauta gurguwar fahimta

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Asusun IMF ya jinjina wa manufofin kuɗi na CBN, ya yaba da shirin ƙarfafa jarin bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Asusun ajiyar kuɗaɗen wajen Nijeriya ya cika maƙil da dala biliyan 54, cika mafi yawa cikin shekaru 18 – CBN

September 7, 2026
Next Post
Cewar Sarkin Zazzau: An yi wa rawar da El-Rufai ya taka wajen naɗa ni sarauta gurguwar fahimta

Cewar Sarkin Zazzau: An yi wa rawar da El-Rufai ya taka wajen naɗa ni sarauta gurguwar fahimta

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!