Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Olayemi Cardoso, ya ce a shekaru uku da yake kan shugabancin bankin ya yi abin a yaba wajen gudanar da aikin sa na tabbatar da daidaiton harkokin kuɗi da kuma farashin kayayyaki.
Cardoso ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, bayan gabatar da sanarwar sakamakon taron Kwamitin Tsarin Kuɗi (MPC) karo na 307.
Ya ce: “Abu na farko shi ne mun sami damar mayar da bankin kan muhimmin aikin sa na asali.
“Yanzu mun shafe watanni 36, wato shekaru uku kenan, tun lokacin da muka karɓi ragamar jagorancin CBN. Kuma kamar yadda yake ga kowane abu, wannan lokaci ne mai kyau da za mu waiwaya baya mu yi nazari.
“Idan muka yi la’akari da halin da muka tsinci kan mu a lokacin, ya kamata mu tuna daga ina muka fito. Mun fito ne daga wani yanayi da aka shiga na rashin amincewa da bankin da kuma ƙasar.
“Hakan ya bayyan a fili musamman ta yadda aka daina yin amanna ko amincewa da kuɗin ƙasar mu.
“A wannan lokaci ne da kuɗin ƙasar mu ke ci gaba da faɗuwa akai-akai. Ba za ka iya tsara komai ba, mutane suka shiga firgici, sannan da yawa suka fitar da duk abin da za su iya daga ƙasar domin kare kuɗaɗen da suka tara cikin wahala,” inji shi.
Cardoso ya ce wancan lokaci ne hatta hukumomin tantance darajar tattalin arzikin ƙasashe suka rage darajar Nijeriya, kuma ba su ga wata babbar dama ga makomar ƙasar ba, har sai an aiwatar da sauye-sauye masu tsauri.
Ya ce a yanzu jami’an da suke jagorantar CBN tun daga shekarar 2023 sun taimaka matuƙa wajen gudanar da ayyukan MPC da kuma bada damar sauke nauyin da ke kan sa a matsayin Gwamnan CBN.
“Abu na farko, bisa la’akari da yanayin da na bayyana a nan a yau, shi ne mun sami damar mayar da CBN kan muhimmin aikin sa na asali.
“A wancan lokaci Bashin Rufa wa Gwamnati Asiri (Ways and Means) da gwamnatin tarayya ta riƙa karɓa daga CBN ya jefa tattalin arzikin cikin wani mummunan hali.
“Mun samu bashin ‘Ways and Means’ da ya kai naira tiriliyan 23.7, wanda ya ƙara rura wutar matsalar hauhawar farashi da muke ciki. Haka kuma, akwai tsare-tsaren tallafi da suka haura naira tiriliyan 10.
“Mun samu kasuwar canjin kuɗin waje a lokacin ta samu matsala sosai, inda ake samun farashin canjin kuɗi iri-iri.
“Aikin mu shi ne dawo da daidaito da kuma tabbatar da daidaiton farashin kayayyaki da kuma zaman lafiyar tsarin kuɗi. Abubuwan da muke alfahari da su sosai a cikin waɗannan shekaru su ne yadda muka iya ɗaukar matakan da suka dace waɗanda suka taimaka wajen dawo da mu wannan matsayi.”






