Bayanan baya-bayan nan da suka fito daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), sun tabbatar da cewa bankunan ajiya na kasuwanci a Nijeriya sun rufe jimillar rassa da cibiyoyin hadahadar kuɗi guda 476 cikin shekaru uku.
Binciken ya tabbatar da cewa an rufe rassan ne daga shekarar 2022 zuwa 2025 a jihohi daban-daban na ƙasar nan, har da yankunan gundumomin FCT Abuja, lamarin da ya rage yawan wuraren da bankunan ke gudanar da ayyukan su kai tsaye da kashi 8.8 cikin 100, bisa CBN.
Sai dai kuma wannan za a iya cewa yana da nasaba ne da ci gaban harkoki, hadahada da mu’amalolin kuɗi ta hanyoyin zamani, wato digital, waɗanda suka haɗa da amfani da wayoyin hannu, hanyar aika kuɗi ko cira ta P.O.S da sauran hanyoyin zamani a komfuta da sauran.
A shekarun baya wanda ke kasuwanci kan riƙa gaganiyar zuwa banki a kowace rana domin shigar da kuɗaɗen cinikin da ya yi a kasuwa. A yanzu kuwa ɗan kasuwa da yawa kan shafe watanni ba su je banki ba, saboda kowa akwai na’urar P.O.S a hannun sa.
Juyin zamani ya haifar da sabbin dabarun aikawa da kuɗi daban-daban na tare da zuwa banki ba. Kuma hakan ya kusa kawar da wahalhalun jigilar tulin kuɗi ana ɗaukar su niƙi-niƙi zuwa kasuwanni ko bankuna.
Tuni CBN ke zagayen karaɗe jihohin ƙasar nan domin wayar da jama’a dangane da muhimmancin rungumar tsarin hadahadar banki na zamani. Haka kuma shigowar manhajojin hadahadar kuɗi na ‘fintech’ sun taka muhimmiyar rawa wajen yadda mutane ke gudanar da mu’amalar kuɗaɗe ba tare da sai an yi takakkiya har zuwa cikin banki ba.
Rufe wasu rassa na bankuna ba ya na nufin duk reshen da aka rufe, wai ana sallamar ma’aikatan cikin sa ba ne, sai dai a yi masu canjin wurin aiki zuwa reshen da ake da matuƙar buƙatar su.
A nazarin da na yi, matsawar banki zai samu riba a wuri, to zai yi hanzarin buɗe reshe a wurin. To amma ba zai yiwu banki ya buɗe reshe a wurin da babu yawaitar kwastomomi ba. Saboda yin haka zai haifar masa da asarar kuɗin wuta, nauyin ɗaukar jami’an tsaro da sauran kuɗin ɗawainiyar kula da bankin.
Tabbas akwai wasu wuraren da za a iya cewa rufe rassan na da alaƙa da matsalar tsaro. Hakan kuwa ya nuna kenan banki ba zai iya gudanar da harkokin kuɗin kwastomomin a yankin da ake fama da barazanar rashin tsaro ba.
Alƙaluman da ke cikin Rahoton CBN CBN na Hadahadar Kuɗi a Shekarar 2025, sun nuna cewa adadin rassan bankuna da cibiyoyin hadahadar kuɗi a faɗin ƙasar ya ragu daga 5,410 a shekarar 2022 zuwa 4,934 a shekarar 2025.
Raguwar ta faru ne duk da cewa adadin bankunan da ke gudanar da ayyuka a ƙasar ya ƙaru a wannan lokaci, lamarin da ke nuna cewa a hankali bankuna na rage yawan wuraren da suke gudanar da ayyukan su.
CBN ya bayyana cewa waɗannan alƙaluma sun haɗa da rassan bankuna da cibiyoyin hadahadar kuɗi da bankunan kasuwanci, bankunan ‘yan kasuwa da bankunan da ba su karɓar riba ke gudanarwa. An samo bayanan daga CBN da Hukumar Inshorar Kuɗaɗen Bankuna ta Nijeriya (NDIC).
Raguwar wuraren gudanar da harkokin banki ta zo ne duk da cewa adadin bankuna ya ƙaru daga 32 a shekarar 2022 zuwa 33 a 2023, sannan ya kai 35 a 2024, kafin ya ɗan ragu zuwa 34 a 2025.
A Kano, adadin wuraren gudanar da harkokin banki bai ragu ba, sai ma ƙaruwa da ya yi daga 164 a shekarar 2022 zuwa 175 a 2023, sannan ya kai 183 a 2024.
Sai dai adadin ya ragu sosai zuwa 157 a shekarar 2025, wanda ya bar jihar da wurare bakwai ƙasa da adadin da take da su shekaru uku da suka gabata.
Kaduna ma ta bi irin wannan tsarin.
Adadin rassan da cibiyoyin hadahadar kuɗi ya ƙaru daga 148 a shekarar 2022 zuwa 156 a 2023, sannan ya kai 164 a 2024, kafin ya ragu zuwa 146 a shekarar 2025.






