• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
September 9, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

A ƙoƙarin sa na kare darajar tsarin harkokin kuɗi a Nijeriya, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara ƙarfafa sa-ido wajen kula da harkokin kuɗi, domin daƙile duk wasu hanyoyi da kafofin da masu ɗaukar nauyin ta’addanci ke bi.

CBN ya jaddada cewa ya mayar da wannan batu a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da yake bai wa fifiko a halin yanzu, domin hana miyagun mutane amfani da tsarin kuɗin ƙasar nan wajen aikata ayyukan da ba su dace ba.

CBN ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Daraktar Riƙo a Sashen Hulɗa da Jama’a da Hulɗa da Masu Zuba Jari, Hajiya Hakama Sidi-Ali, wadda aka raba wa manema labarai a ranar Talata.

A ƙarƙashin wannan sabon matakin ƙara tsaurara sa-ido, CBN ya ce zai mayar da hankali sosai musamman kan yadda cibiyoyin kuɗi ke tafiyar da haɗarin da ke tattare da samar da kuɗaɗen tallafa wa ta’addanci, sa-ido kan hada-hadar kuɗi, aiwatar da takamaiman takunkuman hadahadar kuɗi, da kuma bayar da rahoton duk wata mu’amala mai cike da shakku da ake dangantawa da tallafa wa ta’addanci.

Bankin ya ce zai ci gaba da amfani da tsarin sa-ido bisa la’akari da girman haɗari, ciki har da bincike kai tsaye a cibiyoyin kuɗi da kuma sa-ido daga nesa, domin ƙarfafa matakan yaƙi da masu halatta kuɗaɗen haram (AML), yaƙi da masu samar da kuɗaɗen ta’addanci (CFT), da kuma hana hadahadar samar da kuɗaɗen yaɗuwar makamai masu haɗari (CPF) a faɗin ɓangaren harkokin kuɗi.

A cewar CBN, za a aiwatar da waɗannan matakai ne bisa ga dokoki da ƙa’idojin da ake da su a halin yanzu.

Babban bankin ya kuma bayyana cewa matakin yana tallafa wa haɗin gwiwar Nijeriya a gida da kuma ƙasashen duniya wajen yaƙi da samar da kuɗaɗen ta’addanci, hana samar da kuɗaɗen yaɗuwar makamai masu haɗari, da kuma faɗaɗa ƙoƙarin ƙarfafa mutuncin tsarin kuɗi da kare tsarin kuɗin ƙasar nan.

CBN ya ƙara da cewa, “za a ci gaba da gudanar da ƙarin sa-ido da tuntuɓa idan buƙatar hakan ta taso.”

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan mataki yana nuna ci gaba da jajircewar CBN wajen kare tsarin kuɗi na Nijeriya daga ayyukan da ba bisa ƙa’ida ba, tare da bayar da gagarumar gudunmawa a fannin ƙoƙarin ƙarfafa mutunci da amincin tsarin kuɗi, a matakin cikin gida da kuma na ƙasa da ƙasa.

Previous Post

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

Next Post

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Asusun IMF ya jinjina wa manufofin kuɗi na CBN, ya yaba da shirin ƙarfafa jarin bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Asusun ajiyar kuɗaɗen wajen Nijeriya ya cika maƙil da dala biliyan 54, cika mafi yawa cikin shekaru 18 – CBN

September 7, 2026
Next Post
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!