Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, a matsayin Jakadan “Renewed Hope” kuma mataimakin darakta-janar mai kula da yaɗa manufofin jam’iyya, hulɗa da jama’a da kuma tattara goyon baya.
Naɗin ya fara aiki nan take.
Bayo Onanuga, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, ya bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai cewa Shugaban Ƙasa, a matsayin sa na jagoran jam’iyyar APC, ya naɗa gwamnan ne bisa ƙwarewar sa ta jagoranci da kuma iyawar sa wajen tsara aiki.
Nauyin da ke kan sa zai haɗa da yin aiki tare da darakta-janar na shirin Renewed Hope da kuma manyan shugabannin jam’iyya, musamman shugaban ƙasa na APC, domin tabbatar da daidaito, haɗin kai da kuma tsara ayyuka cikin hikima a dukkan matakan tattara goyon baya da hulɗa da jama’a.
Ya ce: “Shugaban Ƙasa na sa ran Jakadan Renewed Hope da mataimakin darakta-janar zai ƙarfafa, ya inganta tare da yaɗa shirye-shirye da manufofin jam’iyyar, ciki har da nasarori da abubuwan da aka cimma, ta yadda za a ƙara amincewar jama’a tare da ƙarfafa saƙon Renewed Hope a faɗin ƙasa.”
A cikin wasiƙar da ya aike domin sanar da shi naɗin, Tinubu ya rubuta cewa: “Babbar manufar wannan naɗi naka ita ce tabbatar da cewa dukkan ‘yan ƙasa sun san, sun fahimta, kuma a ƙarshe su mara wa jam’iyyar mu da ‘yan takarar ta baya a dukkan matakai domin samun karɓuwa a faɗin ƙasa a zaɓen 2027.
Sannan ya ce: “Shiri yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma wannan buri, kuma jagorancin ka zai kasance muhimmi wajen tafiyar da wannan tsari cikin inganci da hikima.”







