• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka sun haɗa gwiwa don wayar da kan ‘yan Nijeriya kan sababbin ƙa’idojin samun biza

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 8, 2025
in Labarai
A A
0

 

GWAMNATIN Tarayya ta haɗa gwiwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya domin wayar da kan ‘yan Nijeriya kan sababbin ƙa’idojin neman bizar Amurka tare da tabbatar da bin ƙa’ida yayin neman.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudana tare da Jakaden Amurka a Nijeriya, Richard M. Mills Jr., a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce wannan yekuwar wayar da kan ta zama dole saboda Amurka tana ci gaba da zama ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suke yawan ziyarta.

Idris ya ce a tsawon shekaru ‘yan Nijeriya suna tafiya Amurka saboda dalilai daban-daban, ciki har da yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu, da kuma neman magani.

Ya ce: “An san Nijeriya a duniya a matsayin ƙasar da ‘yan ƙasar ta suke yawan yin tafiya zuwa ƙasashe daban-daban, suna hulɗa da ƙasashen duniya ta fuskar harkar kasuwanci, ilimi, yawon buɗe ido, da sauran muhimman fannoni. Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suka fi ziyarta, abin da ke nuna zurfin dangantaka mai tsawo tsakanin ƙasashen biyu.

“Yawancin ‘yan Nijeriya suna zuwa Amurka ne domin karatu, aiki, neman magani, ziyartar ‘yan’uwa, yawon buɗe ido, da damar zuba jari.

“Wannan mu’amala mai ƙarfi tana ci gaba da bunƙasa al’ummomin biyu.

“Sababbin abubuwan da Ofishin Jakadancin Amurka ya bayyana game da sauye-sauye a ayyukan ofishin jakadancin da hanyoyin neman bizar sun jima suna cikin labarai kwanan nan.

“Waɗannan sauye-sauyen, kamar yadda Ofishin Jakadancin Amurka ya bayyana, wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta bayar da sabis, ƙara saurin aiki, da mayar da martani ga sauye-sauyen buƙatun ayyukan jakadanci.”

Ministan ya yaba wa gwamnatin Amurka bisa ƙoƙarin yin bayani kai-tsaye ga ‘yan Nijeriya a wannan taro tare da tabbatar da samun sahihan bayanai na zamani ga kowa.

Haka kuma ya jaddada girmamawa da haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Amurka da kuma jajircewar Ofishin Jakadancin wajen sanar da matafiya ‘yan Nijeriya.

A nasa jawabin, Jakaden Amurka, Ambasada Mills, ya ce bin ƙa’idojin neman biza da dokokin Amurka na ‘yan Nijeriya abu ne mai muhimmanci wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

“Bin dokokin neman biza na Amurka ba kawai wani nauyi ba ne, amma ginshiƙi ne na amincewa da girmama juna tsakanin ƙasashen biyu,” inji Ambasada Millis.

Ya ƙara da cewa: “Kamar yadda Minista ya bayyana, ni da shi mun yi tattaunawa mai amfani game da dokokin biza na Amurka da kuma yadda za mu isar wa ‘yan Nijeriya muhimmancin bin waɗannan dokokin.

“Bari in fayyace cewa Amurka tana daraja ƙarfaffar dangantakar ta da Nijeriya da kuma nau’o’in hulɗa da yawa da ke tsakanin ƙasashen biyu.

“Bizar Amurka na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da riƙe waɗannan lamurran dangantaka da ƙarfafa su, ko ta hanyar bai wa mutane damar tafiya domin ilimi, kasuwanci, yawon buɗe ido, ko musayar al’adu.”

Jakaden ya jaddada cewa ya zama dole a yi amfani da biza bisa ga dokoki da ƙa’idojin Amurka.

Ya ce: “Tabbas, muna maraba da baƙi ‘yan Nijeriya a Amurka kamar yadda Nijeriya take maraba da ‘yan Amurka masu zuwa wannan ƙasa. Dukkan gwamnatoci suna son baƙi su girmama dokokin ƙasashen mu da ƙa’idojin mu.”

Ya gargaɗi masu neman biza cewa yin amfani da ita ba bisa ƙa’ida ba ko bayar da bayanan ƙarya yayin neman ta yana iya rage amincewar juna a tsakanin ƙasashen biyu.

Ya ce: “Muna kira ga dukkan masu neman biza da su bayar da sahihan bayanai kuma su bi sharuɗɗan biza ɗin su, domin na sani, mafi yawan ‘yan Nijeriya suna yin hakan. Ta yin haka, za mu ƙarfafa ɗorewar zumunci tsakanin ƙasashen mu.”

Ambasada Mills ya kuma yaba wa Idris bisa jajircewar sa wajen kare ‘yancin faɗar albarkacin baki a Nijeriya, yana mai jaddada cewa wannan ɗabi’a ce da ta yi daidai da manufofin Amurka.

Ya kuma yaba wa haɗin kai da ake samu daga hukumomin Nijeriya, ciki har da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, Hukumar Kwastan ta Nijeriya, da Fadar Shugaban Ƙasa, wajen wayar da kan jama’a kan ƙa’idojin biza.

Haka kuma ya shawarci ‘yan Nijeriya da su nemi sahihan bayanai daga shafin soshiyal midiya na Ofishin Jakadancin Amurka kuma su tabbatar da cewa duk wata tambaya da suke da ita za su samu amsa cikin lokaci.

Tags: AmurkabizaMohammed Idris
Previous Post

Matar Tinubu ta ƙaddamar da na’urorin musamman don gano cutar tarin fuka da magance ta

Next Post

Gwamnan Bauchi kuma Shugaban Gwamnonin PDP ya roƙi Peter Obi ya dawo domin takarar 2027

Related Posts

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Tsaro

Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro

May 9, 2026
Next Post
Gwamnan Bauchi kuma Shugaban Gwamnonin PDP ya roƙi Peter Obi ya dawo domin takarar 2027

Gwamnan Bauchi kuma Shugaban Gwamnonin PDP ya roƙi Peter Obi ya dawo domin takarar 2027

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!