A YAU Juma’a Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP kuma Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, ya yi kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi, da ya dawo jam’iyyar PDP kafin babban zaɓen 2027.
Ya bayyana hakan ne lokacin da Obi ya kai ziyara a Gidan Gwamnatin Bauchi.
A jawabin sa ga manema labarai, Bala ya nanata muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyar PDP, ADC, da sauran su domin yin aiki tare don samar da adawa mai ƙarfi.
A cewar sa, duk da yake ba a gaba da gwamnati mai ci yanzu, “amma babu kasafin kuɗi, babu tsari, komai sai dai maganar siyasa tun daga ranar farko.”
Ya ƙara da cewa, “Akwai yunwa da kuma fushi sosai, ba mu so mu jawo tarzoma. Saboda haka don Allah ka dawo. Inda ya kamata a same ka kenan. Kada ta tafi wani waje inda ake ta hayaniya.”
A nasa jawabin, Peter Obi ya bayyana cewa ya kai ziyara Bauchi ne domin ya sadu da matasa a kwalejojin kiwon lafiya da makarantun allo.
Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed saboda nasarorin da ya samu ɓangaren ba da ilimi.
Ya ce duk wani haɗin gwiwar siyasa da za a yi domin zaɓen 2027, to a yi shi domin cigaba ƙasa, nagarta, da tausayin jama’a — ba kawai don a samu mulki ba.
A yayin ziyarar, Obi ya ba da gudunmawar naira miliyan 15 don taimaka wa bayar da ilimi a jihar — da naira miliyan 10 ga Kwalejin Kimiyyar Aikin Nas ta Malikiya da naira miliyan 5 ga naira miliyan 5 Makarantar Islamiyya da Haddar Alƙur’ani ta Intisharu.

A jawabin sa ga ɗaliban, ya faɗa masu cewa, “Ita ma’aikaciyar jinya ta ma fi likita. Ma’aikaciyar jinya ce ta san majinyaci, ita nas ce take tare da majinyaci, ita nas ita ce ta san komai da komai.”







