• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Kiwon Lafiya

Matar Tinubu ta ƙaddamar da na’urorin musamman don gano cutar tarin fuka da magance ta

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 7, 2025
in Kiwon Lafiya
A A
0

 

UWARGIDAN Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana aniyar ta na ganin an kawar da cutar tarin fuka (TB) a Najeriya kafin shekarar 2030. Ta bayyana haka ne a wurin kaddamar da sabbin na’urorin gano cutar TB da aka samar domin inganta ganowa da magance cutar a faɗin ƙasar nan.

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a Bwari, Abuja, inda aka bayyana cewa na’urorin an samar da su ne ta karkashin shirin Renewed Hope Initiative (RHI) da Sanata Oluremi Tinubu ke jagoranta, wanda ya cika alkawarin naira biliyan daya da aka yi a lokacin bikin ranar ciwon Tarin Fuka ta duniya a Sauka dake birnin tarayya.

A jawabin da ta gabatar ta bakin matar Gwamnan Jihar Kwara, Ambasada Olufolake Abdulrazaq, Sanata Tinubu ta ce da wannan cigaba, za a iya gane cutar cikin gaggawa a sassa da dama na ƙasar nan, musamman inda mutane ba su da isassun kayan gwaji.

Ta ce cutar TB na da magani, amma mutane da dama a Najeriya na mutuwa sanadiyyar rashin na’urorin tantance cutar da wuri.

Ta kuma jaddada buƙatar ƙara saka hannun jari daga cikin gida, samar da kuɗi, da ƙwarewa.

Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya yaba wa Sanata Tinubu bisa jagoranci da jajircewar da ta nuna wajen yaƙi da cutar TB.

Ya ce Gwamnatin Tarayya na ci gaba da ɗaukar matakai don haɗa ayyukan yaki da TB cikin tsarin kula da lafiyar matakin farko da kuma ƙarfafa ɗaukar ma’aikatan lafiya.

Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci a kwantar da hankali kan dakatar da gidan rediyon Badeggi FM

Next Post

Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka sun haɗa gwiwa don wayar da kan ‘yan Nijeriya kan sababbin ƙa’idojin samun biza

Related Posts

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA
Kiwon Lafiya

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA

April 20, 2026
Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata
Kiwon Lafiya

Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata

April 5, 2026
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500
Kiwon Lafiya

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500

April 3, 2026
Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya – Minista
Kiwon Lafiya

Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya – Minista

March 3, 2026
Nijeriya ta rattaba hannu kan babbar yarjejeniyar zuba jari a fannin kiwon lafiya
Kiwon Lafiya

Nijeriya ta rattaba hannu kan babbar yarjejeniyar zuba jari a fannin kiwon lafiya

February 5, 2026
Amurka za ta kashe dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da asibitoci 900 na mabiya addinin Kirista a Nijeriya
Kiwon Lafiya

Amurka za ta kashe dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da asibitoci 900 na mabiya addinin Kirista a Nijeriya

December 21, 2025
Next Post

Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka sun haɗa gwiwa don wayar da kan ‘yan Nijeriya kan sababbin ƙa’idojin samun biza

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!