• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnati ta yi kira a riƙa amfani da ilimin hulɗa da jama’a wajen ƙaryata zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
October 20, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnati ta yi kira a riƙa amfani da ilimin hulɗa da jama’a wajen ƙaryata zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya
Minista Idris yana jawabi a babban taron Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a na Duniya (World Public Relations Forum, WPRF Abuja 2026) a Abuja a yau

Minista Idris yana jawabi a babban taron Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a na Duniya (World Public Relations Forum, WPRF Abuja 2026) a Abuja a yau

 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga masana harkokin sadarwa da su yi amfani da fayyace gaskiya tare da kafa hujjoji wajen ƙaryata iƙirarin da wasu ke yaɗawa cewa wai ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya.

Idris ya yi wannan kiran ne a Abuja a wajen babban taron ƙaddamar da reshen ƙasar nan na Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a na Duniya (World Public Relations Forum, WPRF Abuja 2026), inda ya yi gargaɗin cewa martabar ƙasar nan tana fuskantar barazana daga mutanen wasu ƙasashe da ke ƙoƙarin gurɓata gaskiya da raunana haɗin kan ‘yan ƙasa.

Ya ce: “Ya kamata mu fahimci irin barazanar da ke fuskantar martabar ƙasar mu daga wasu maƙaryata da ke ƙoƙarin ɓata sunan Nijeriya, suna yaɗa cewa wai ana yi wa wasu mutane kisan ƙare dangi saboda addinin su. Wannan farfaganda ce da masu ganin haɗin kan mu ya raunana suka kitsa ta daga ƙasar waje.

Minista tare da shugabannin taron

“Na sha faɗa cewa babu ko ɗigon gaskiya a zancen cewa ana ‘yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi’ a Nijeriya.”

Ministan ya jaddada cewa manufar irin waɗannan labaran ƙaryar ita ce a haifar da rarrabuwar kai, don haka wajibi ne a riƙa mayar da martani ta hanyar sadarwa cikin gaskiya da bin ƙa’idar aikin jarida.

Ya ƙara da cewa, “Ina kira a gare mu da mu yi amfani da dabarun hulɗa da jama’a bisa gaskiya da hujjoji domin mu ƙaryata waɗannan muggan labaran game da Nijeriya.”

Ministan ya ce a wannan zamani na dijital, bayanai suna yaɗuwa cikin sauri fiye da yadda mutane ke nazari, don haka masana harkokin sadarwa su kasance masu gaskiya, tausayi, da sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.

Ya danganta wannan kira da Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda, a cewar sa, yake ƙoƙarin sake gina aminci tsakanin gwamnati da jama’a ta hanyar fayyace gaskiya da hulɗa da jama’a.

A cewar sa, damar da Nijeriya ta samu ta gudanar da Taron Hulɗa da Jama’a na Duniya na 2026 alama ce ta jagorancin Nijeriya wajen sadarwa bisa ƙa’ida da fayyace gaskiya a duniya.

Alhaji Mohammed Idris a wurin taron

Ya ce: “Wannan taro wata hujja ce cewa ƙarƙashin jagoranci mai hangen nesa na Mai Girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Nijeriya ta zama mai murya mafi ƙarfi, mafi haske, kuma mafi ƙarfin hali wajen samar da ingantacciyar sadarwa a Afrika da ma duniya baki ɗaya.”

Idris ya yaba wa Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a da Gudanar da Sadarwa ta Duniya, ƙarƙashin Farfesa Justin Green, da kuma Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), ƙarƙashin Dakta Ike Neliaku, saboda jawo hankalin duniya zuwa ga Nijeriya ta hanyar babban taron na WPRF.

A cikin kira mai cike da bada ƙwarin gwiwa, ministan ya roƙi masana harkokin sadarwa, da ‘yan jarida, da jami’an gwamnati da su rungumi hanyar sadarwa mai ɗauke da fayyace gaskiya da amana.

Ya ce: “Ya dace wannan buɗe taron ya kasance kira ga zukatan mu.

Saƙo ga ƙwararru shi ne: ku tsaya ƙyam kan gaskiya. Saƙo ga ‘yan jarida: ku bayar da rahoto cikin gaskiya da mutunci. Saƙo ga jami’an gwamnati: ku bayyana gaskiya ba tare da ɓoye komai ba. Saƙo ga jama’ar ƙasa: ku yi magana da tunani.”

Ya bayyana tabbacin cewa za a riƙa taron WPRF Abuja 2026 a matsayin muhimmin zango wajen sake gina martabar Nijeriya a idon duniya.

Ya ce: “A ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya na sake fasalta yadda ake kallon ta a idon duniya. Ya dace wannan Taro ya zama abin tunawa a matsayin lokacin da babbar dimokiraɗiyyar Afrika ta jagoranci duniya wajen bayyana ma’anar aikin sadarwa na gaskiya da gaskiya.”

Jigon taron WPRF na bana dai shi ne: “Sadarwa da Gaskiya: Muryar Duniya”.

Tags: Mohammed IdrisNIPRWPRFAbuja2026
Previous Post

Kotun KAROTA ta hukunta mutum 87 da suka karya dokar zirga-zirga a Kano

Next Post

Tinubu ya taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwar sa

Related Posts

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Tsaro

Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro

May 9, 2026
Next Post
Tinubu ya taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwar sa

Tinubu ya taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwar sa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!