Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa saƙon taya tsohon gwamnan Jihar Kano kuma shahararren ɗan siyasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, murnar zagayowar ranar haihuwar sa a yau, 21 ga Oktoba, 2025.
Shugaban ya taya ‘yan’uwa da abokan arzikin Kwankwaso da ma tawagar siyasar sa murna a yayin da suke bikin wannan rana mai muhimmanci.
Shugaban ya ce idan an duba da irin gagarumar gudunmawar da Kwankwaso ya bai wa ƙasar nan a dukkan muƙaman shugabanci daban-daban da ya rike, kama daga matsayin sa na tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a Jamhuriya ta Uku, sannan Gwamnan Jihar Kano na wa’adi biyu, kana Ministan Tsaro, da kuma Sanata mai wakiltar Yankin Kano ta Tsakiya, za a ga lallai Kwankwaso ya bayar da gagarumar gudunmawa ga cigaban ƙasa.
Tinubu ya tabbatar da cewa ƙarin haɓakar tasirin Sanatan a arewacin Nijeriya, musamman a Jihar Kano, na da nasaba da irin salon siyasar sa da ke bai wa muradun al’umma fifiko, wanda ya yi kama da salon siyasar Malam Aminu Kano da Alhaji Abubakar Rimi.
Ya ce: “Sanata Kwankwaso yana nan a matsayin aboki kuma takwaran aiki na tun muna ‘yan Majalisar Tarayya a 1992 sannan a matsayin gwamnoni a 1999.
“Har ila yau, mun yi aiki tare a yayin gwagwarmayar kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Duk da cewa daga baya ya bar APC don kafa tasa jam’iyyar ta New Nigeria People’s Party (NNPP), amma abu mafi muhimmanci shine kasancewar sa jagora a sahun gaba a ɓangaren siyasa.”
Shugaban ya yi wa Kwankwaso fatar alheri, ɗorewar lafiya, da kuma ƙarin shekaru masu amfani cikin hidimar al’umma.







