• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ba za mu musguna wa ’yan jarida a mulkin Tinubu ba – Gwamnatin Tarayya

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
December 2, 2025
in Labarai
A A
0
Ba za mu musguna wa ’yan jarida a mulkin Tinubu ba – Gwamnatin Tarayya
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a Taron Shekara-shekara na Cibiyar 'Yan Jarida ta Duniya (IPI) da aka gudanar a yau a otal ɗin NICON Luxury da ke Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a Taron Shekara-shekara na Cibiyar 'Yan Jarida ta Duniya (IPI) da aka gudanar a yau a otal ɗin NICON Luxury da ke Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a Taron Shekara-shekara na Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya (IPI) da aka gudanar a yau a otal ɗin NICON Luxury da ke Abuja

Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida, kare dimokiraɗiyya, da tabbatar da tsaro a fagen yaɗa labarai a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a Taron Shekara-shekara na Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya (IPI) da aka gudanar a yau Talata a otal ɗin NICON Luxury da ke Abuja.

Idris ya bayyana kafofin watsa labarai a matsayin “hanyar sadarwa mafi muhimmanci ta kowace dimokiraɗiyya, kuma mai ƙara ƙarfafa muryar ’yan ƙasa.”

Ya ce halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wajen buɗe taron ya nuna yadda gwamnati take buɗe ƙofa ga tattaunawa da manema labarai.

Da yake magana kan taken taron, wato “Magance Musguna Wa Kafofin Watsa Labarai a Nijeriya,” Ministan ya ce dole ne a bambanta abubuwan da suka faru a baya da kuma yanayin da ake ciki a yau.

Ya bayyana cewa, “Babu wata manufa ta gwamnati da ke neman takura kafofin watsa labarai a yau,” yana mai cewa hujjoji suna nuna kamewa da haɗin kai, ba ƙiyayya ba.

Ya ce: “Tattaunawa kan ’yanci dole ta ta’allaƙa ne a kan gaskiya. Idan wani ya yi iƙirarin cewa akwai wata manufa ta musgunawa a yau, ya kamata mu auna wannan iƙirari da hujjoji.”

Idris ya ce hukumomin tsaro yanzu suna aiki ne ƙarƙashin ƙa’idoji masu tsauri domin tabbatar da amincin ’yan jarida, musamman a lokutan zanga-zanga ko wuraren da ake ganin rikice-rikice.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da sauran manyan mahalarta Taron Shekara-shekara na Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya (IPI) da aka gudanar a yau a yau a Abuja

Ya kuma bayyana cewa hukumomin da ke kula da yadda kafafen yaɗa labarai ke aiki suna ci gaba da samar da muhallin da ya dace, mai tsari da gaskiya.

Ya ce: “’Yantar da kafofin watsa labarai abu ne da ba za a iya watsar da shi ba. Dole ne ’yan jarida su iya yin aikin su ba tare da tsoratarwa ko tsoma baki ba, kuma wannan gwamnati ta kasance a ko da yaushe a kan wannan matsayi.”

Ya kuma ambaci wani rahoto da wata jarida ta wallafa rahoto mara kyau da ya yi iƙirarin cewa wai Nijeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ke tilasta karɓar haƙƙin ‘yan luwaɗi da maɗigo.

Ya ce duk da cewa rahoton na iya tayar da rikicin addini da al’ada, gwamnati ta zaɓi gaskiya maimakon husuma.

Idris ya ce: “Gwamnatin Tarayya ta buga cikakken rubutun yarjejeniyar, ta fitar da bayanai na gaskiya, ta tattauna da jama’a a fili, sannan ta kai ƙorafi ta hanyar mai duba aikin jaridu mai zaman kan sa. Ba mu yi amfani da matsin lamba ko tilastawa ba. Mun zaɓi gaskiya.”

Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya za ta karɓi baƙuncin Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai (IMIL) na Afrika, wadda za ta riƙa horar da ’yan jarida, malamai, da al’umma kan yadda ake yin aikin jarida cikin gaskiya, tantance bayanai, da yaƙi da yaɗa ƙarya bisa tsarin al’adu na Afrika.

Ya ce cibiyar za ta kasance mai zaman kan ta, wadda ke dogaro da ilimi ba tare da zama mai magana da yawun gwamnati ba.

Ya ce za a ƙaddamar da ita a farkon watannin 2026.

Haka kuma, Idris ya tabbatar da shirye-shiryen gwamnati na yin aiki tare da IPI reshen Nijeriya, Ƙungiyar Editocin Nijeriya, da Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya domin sabunta tsarin dokokin kafafen yaɗa labarai bisa ƙa’idojin duniya, tare da kiyaye ’yancin magana da muradun jama’a.

Ya ce: “Haƙƙin mu mu duka ba wai kawai ƙalubalantar musgunawa ba ne, har ma da faɗaɗa ‘yanci. Mu ƙarfafa ginshiƙan dimokiraɗiyyar mu ta hanyar kare ‘yancin da ke tabbatar da dorewar ta.”

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda shi ne ya jagoranci buɗe taron.

Tags: aikin jaridaBolaTinubuIMILIIPIMohammedIdris
Previous Post

Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa sabon Ministan Tsaro

Next Post

CBN ya umurci bankuna su mayar wa waɗanda aka yi wa zambar APP kuɗin da suka yi asara cikin sa’o’i 48

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
CBN ya tashi haiƙan: Malejin farashin kayayyaki ya ƙara yin ƙasa zuwa kashi 16.05, yayin da asusun kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 46.7

CBN ya umurci bankuna su mayar wa waɗanda aka yi wa zambar APP kuɗin da suka yi asara cikin sa'o'i 48

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!