• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya umurci bankuna su mayar wa waɗanda aka yi wa zambar APP kuɗin da suka yi asara cikin sa’o’i 48

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
December 3, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya tashi haiƙan: Malejin farashin kayayyaki ya ƙara yin ƙasa zuwa kashi 16.05, yayin da asusun kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 46.7
Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

A wani sabon tsarin ƙara kare haƙƙin kwastomomi masu hulɗa da bankuna da kuma kare su daga ɗibga asara, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da wani sabon umarni da ke wajabta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi su mayar wa waɗanda suka faɗa cikin zambar Authorised Push Payment (APP) kuɗin su cikin awanni 48.

Wannan dai wani muhimmin mataki ne da ke nufin ƙara kare masu gudanar da harkokin kuɗi daga yawaitar zambar da ake yi masu ta hanyar kafofin hadahadar na zamani.

Wato zambar APP ita ce salon damfara da ake yi idan mutum ya tura kuɗi da kan sa zuwa asusun masu damfara bisa yaudarar sa ta hanyar yin sojan gona, yaudara ko yin alƙawarin bogi.

Sai dai kuma shi wannan ba kamar zambar da ‘yan dandatsa ke wa mutum kutse cikin asusun ajiyar ba ce, ba tare da sanin mai shi ba.

Masu aikata zamba da damfara ta APP na amfani da dabarun yaudarar jama’a ne domin samun amincewar su har su tura masu kuɗaɗe.

CBN ya bayar da wannan ne umurni ne da aka bayar mai ɗauke da sa hannun Rita I. Sike, wadda ita ce Daraktar Sashen Tsare-tsare da Ƙa’idojin Hadahadar Kuɗi ta CBN, ta sanya wa hannu a ranar Talata.

Umurnin dai ya fayyace yadda bankuna da cibiyoyin kuɗi za su gudanar da bincike, warware matsaloli, da kuma mayar da kuɗaɗen ga mutanen da suka shiga cikin taskun zambar APP.

CBN ya ce za a mayar wa mutum kuɗin sa ne bayan an kammala bincike tare da tantancewa, kuma dole ne a yi hakan cikin sa’o’i 48.

Sanarwar ta ci gaba da jaddada cewa binciken da mayar da kuɗin tilas a gudanar da su cikin adalci, kan lokaci a bisa gaskiya.

Haka nan kuma dokokin sun fayyace yadda za a yi idan abin ya shafi cibiyoyi fiye da ɗaya. A irin wannan yanayi, bankin da aka fara tura kuɗin daga gare shi dole ne ya sanar da bankin da ya karɓa cikin minti 30 bayan samun ƙorafi.

Sannan dukkan su za su yi bincike tare, su gano kurakuran da suka faru, su tantance adadin asarar, sannan su amince kan mayar da kuɗi da matakan kariya.

Umarnin na ɗauke da cewa a irin waɗannan lokuta, dole ne a kammala mayar da kuɗin wanda aka zambata cikin kwanakin aiki 16 daga ranar da aka fara bayar da rahoton lamarin.

Wannan matakin CBN ya ɗauka na daga cikin yunƙurin sa na ƙarfafa tsarin kuɗi da dawo da amincewar jama’a ga hanyoyin hadahadar kuɗi ta zamani a Nijeriya.

A ƙarƙashin waɗannan ka’idoji, mutanen da abin ya shafa dole ne su bada rahoton zambar da aka yi masu ta ‘APP’ cikin awa 24, ko kuma awa 48 idan akwai buƙata.

Rahoton zai ƙunshi bayanan ma’amala, bayanan wanda aka tura wa kuɗi, da wasu takardun da ke nuna cewa tabbas an damfari mutum.

Da zarar an kai ƙorafi, to dole ne su kuma cibiyoyin kuɗi su tabbatar da karɓa cikin awanni 24, su ba da lambar shaidar karɓar ƙorafi, sannan su bayyana lokacin kammala bincike.

CBN ya kuma gargaɗi bankuna cewa rashin gudanar da bincike cikin lokaci ba tare da uzuri ba na iya zama karya dokar kare masu amfani da bankuna, wanda ka iya jawo hukuncin a kan bankunan kan su.

Sai dai kuma CBN ya ce duk wanda aka yi wa zamba, to kada ya yi jinkirin bayar da rahoto fiye da awa 72, ba tare da wani ƙwaƙƙwaran uziri ba, kamar rashin lafiya ko kuma sai daga bayan wasu kwanaki sannan ya gane ashe zamba ce aka yi masa.

Tags: bankunaCBNumurni
Previous Post

Ba za mu musguna wa ’yan jarida a mulkin Tinubu ba – Gwamnatin Tarayya

Next Post

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Janar Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaro

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa sabon Ministan Tsaro

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Janar Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaro

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!