Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunan tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (ritaya), ga Majalisar Dattawa domin tabbatar da shi a matsayin sabon Ministan Tsaro.
Shi ne ya maye gurbin bayan Alhaji Mohammed Badaru Abubakar wanda ya yi murabus a jiya Litinin.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya faɗi a wata sanarwa cewa Tinubu ya aika da wasiƙa zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, inda ya sanar da shi cewa naɗin Janar Musa ya biyo bayan ajiye aikin da Badaru ya yi a ne a ranar Litinin saboda matsalolin lafiya.
Janar Musa, wanda zai cika shekaru 58 da haihuwa a ranar 25 ga Disamba, ya kasance ɗaya daga cikin manyan hafsoshin soja da suka yi fice a ayyukan soja tun bayan shiga rundunar a shekarar 1991.
Ya riƙe muƙamin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 zuwa Oktoba 2025, tare da samun kyaututtuka da dama, ciki har da Colin Powell Award for Soldiering a 2012.
An haife shi a Sakkwato a 1967, inda ya yi karatun sa na firamare da sakandare, kafin ya tafi Kwalejin Ilimi ta Zariya.
Daga nan ya shiga Makarantar Horar da Sojoji ta NDA a 1986, ya kammala digirin sa a 1991.
Tun daga lokacin, Musa ya riƙe muƙamai da dama a rundunar soja, ciki har da Babban Jami’i mai lura da horo da ayyuka a Hedikwatar Runduna ta 81, Kwamandan Bataliya ta 73, da Mataimakin Darakta a Sashen Tsare-tsaren Runduna.
A 2019 ya jagoranci Sector 3 na Operation Lafiya Dole da kuma Multinational Joint Task Force a yankin Tafkin Chadi.
Daga bisani, a 2021, aka naɗa shi Kwamandan Operation Haɗin Kai, sannan ya jagoranci Rundunar Infantry kafin Shugaba Tinubu ya naɗa shi Babban Hafsan Tsaro a 2023.
A wasiƙar da ya aika majalisar, Tinubu ya bayyana gamsuwar sa da cewa Musa zai ƙara ƙarfafa wa Ma’aikatar Tsaro gwiwa tare da taimaka wa gwamnati wajen inganta tsaron ƙasa.







