• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, October 2, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar gama-gari kan matsalar tsaro – NLC

ALI KANO by ALI KANO
December 14, 2025
in Tsaro
A A
0
Ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar gama-gari kan matsalar tsaro – NLC
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) na Ƙasa, Mista Joe Ajaero, a wurin wata zanga-zanga

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) na Ƙasa, Mista Joe Ajaero, a wurin wata zanga-zanga

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) na Ƙasa, Mista Joe Ajaero, ya ce za su yi zanga-zangar ƙasa kamar yadda ƙungiyar ta shirya gudanarwa a ranar 17 ga Disamba, ba su janye ba.

Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa 19 kuma Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, a birnin Gombe, babban birnin jihar.

Ajaero ya ce zanga-zangar za ta nemi matakin gaggawa da ƙarfi daga gwamnati kan matsalar rashin tsaro, yana mai jaddada cewa lamarin yanzu ya shafi kowane ɗan Nijeriya, ba tare da la’akari da matsayi ko sana’a ba.

Ya ce ayyukan ’yan bindiga da laifukan tashin hankali ba su dace da al’adar Nijeriya ba, kuma dole ne a haɗa kai wajen yin Allah-wadai da su domin sauya abin da ya kira abu mai hatsari ga ƙasa.

A cewar sa, rashin tsaro na lalata tattalin arziki tare da raunana ikon Nijeriya na jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje.

Ƙungiyar ta NLC ta ba da sanarwa a ranar 8 ga Disamba cewa tana shirin gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya kan matsalar rashin tsaro a ƙasar.

Ta yi Allah-wadai da sacewa da kisan wani ma’aikacin makaranta a harin da aka kai wata makaranta a Jihar Kebbi, tare da sukar janye jami’an tsaro daga makarantar kafin faruwar harin.

NLC ta bayyana ƙaruwar hare-haren da ake kai wa makarantu a matsayin abin tayar da hankali, tare da kiran Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da tsaron dukkan makarantu, musamman waɗanda ke yankuna masu nisa da kuma masu rauni.

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan rikicin da ke addabar ɓangaren manyan makarantu, yajin aikin da ƙungiyar haɗin gwiwar ma’aikatan lafiya (JOHESU) ke yi, da kuma farfaɗo da Haɗin Gwiwar Ƙwadago da Ƙungiyoyin Farar Hula (LASCO).

Haka kuma, NLC ta yi tsokaci kan halin da Jam’iyyar Labour take ciki, inda ta shawarci membobin ta da su sake daidaita jam’iyyar da ƙa’idoji, aƙida da mutuncin ma’aikata.

Tags: Joe AjaeroNLCzanga-zanga
Previous Post

Ziyarar Messi a Indiya ta rikiɗe zuwa hargitsi yayin da masoyan sa suka lalata filin wasa saboda ficewar sa ba zato ba tsammani

Next Post

Shirin ƙarfafa noma: Gwamnan CBN ya ƙaddamar da Kwamitin Asusun Bada Bashi ga Manoma

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Shirin ƙarfafa noma: Gwamnan CBN ya ƙaddamar da Kwamitin Asusun Bada Bashi ga Manoma

Shirin ƙarfafa noma: Gwamnan CBN ya ƙaddamar da Kwamitin Asusun Bada Bashi ga Manoma

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!