Ziyarar da Lionel Messi ya kai ƙasar Indiya ta rikiɗe zuwa hargitsi a ranar Asabar lokacin da wasu fusatattun masoyan sa suka lalata filin wasa, sakamakon barin filin da fitaccen ɗan ƙwallon ya yi ba zato ba tsammani.
‘Yan kallo da suka fusata sun rushe shingaye tare da kutsa kai cikin wani filin wasa da ke Indiya.
Shahararren ɗan ƙwallon yana rangadin kwanaki uku ne a ƙasar a matsayin wani ɓangare na abin da ake kira GOAT Tour.
Tauraron na ƙungiyoyin Ajantina da Inter Miami mai shekaru 38 ya sauka a jihar West Bengal da ke gabashin ƙasar da sassafe a ranar Asabar, inda magoya baya cike da farin ciki suka tarbe shi suna rera sunan sa.
Awanni kaɗan bayan haka, dubban magoya baya sanye da rigunan Messi suna ɗaga tutar Ajantina suka cika filin wasan Salt Lake da ke babban birnin jihar, Kolkata. Sai dai tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka a kusa da ɗan wasan sun hana masoya samun damar ganin sa sosai.
Messi ya zagaya cikin filin wasan yana gaisawa da magoya baya, sannan ya bar filin da wuri ba kamar yadda aka tsara ba.
Masoyan sa da suka ji takaici—da dama daga cikin su sun biya fiye da dala 100 na tikitin shiga—sun cire ɓaɓɓalle kujerun filin wasa tare da wurga kwalaben ruwa zuwa cikin filin.
Wasu da dama kuma sun kutsa kai cikin filin, suka lalata tutoci da tantuna.
“Ni a wuri na, kallon Messi abin jin daɗi ne, mafarki ne. Amma na rasa damar ko da ganin sa kaɗan ne saboda rashin tsari a filin wasan,” inji ɗan kasuwa mai shekaru 37, Nabin Chatterjee.
Kafin rikicin ya ɓarke, Messi ya ƙaddamar da wani mutum-mutumi mai tsawon mita 21 (ƙafa 70) da ke nuna shi yana ɗaga Kofin Duniya.
Haka kuma an yi tsammanin zai buga ɗan gajeren wasa a filin.
Wani masoyi da ke cikin fushi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Press Trust of India (PTI) cewa mutane sun kashe “albashin wata ɗaya” domin su ga Messi.
“Na biya rupiya 5,000 (dala 55) don tikiti, na zo da ɗa na domin mu kalli Messi, ba ’yan siyasa ba. Sai ga shi ’yan sanda da sojoji suna ɗaukar hotunan kai-tsaye (selfies) da shi, kuma laifin yana kan masu shirya taron,” inji Ajay Shah ga PTI.
Babbar ministar jihar, Mamata Banerjee, ta ce ta “damu” kuma ta “ɗimauce” da rashin kyakkyawan tsari.
“Ina ba Lionel Messi haƙuri ƙwarai, haka nan ga duk masoya wasanni da magoya bayan sa, kan wannan mummunan lamari,” ta ce a wani saƙo da ta wallafa a X, inda ta ƙara da cewa ta bayar da umarnin a gudanar da bincike kan abin da ya faru.
Zaman Messi a Indiya na iya haɗawa da yiwuwar ganawa da Firayim Minista Narendra Modi.
A wannan makon, Messi ya lashe lambar Ɗan Wasa Mafi Tsada (Most Valuable Player, MVP) ta Major League Soccer a karo na biyu a jere, bayan ya jagoranci ƙungiyar Inter Miami zuwa kambin MLS tare da zama wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a gasar.
Messi, wanda tsohon ɗan wasan Barcelona da Paris Saint-Germain ne, zai jagoranci ƙoƙarin ƙasar Ajantina na kare kambin Kofin Duniya a watan Yuni–Yuli a Arewacin Amurka.







