• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, May 15, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Allah zai bi mana haƙƙi kan yafewar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inji iyalan marigayi Bilyaminu

ALI KANO by ALI KANO
October 13, 2025
in Labarai
A A
0
Allah zai bi mana haƙƙi kan yafewar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inji iyalan marigayi Bilyaminu

 

Iyalan Bilyaminu Ahmed Bello, wanda matar sa Maryam Sanda ta yi wa kisan gillar a cikin 2017, sun ce ba su aminta da yafewar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam ɗin ba.

A takardar bayani da ya fitar a madadin iyalan, Dakta Bello Haliru Mohammed, OFR (Ɗangaladiman Gwandu), ya bayyana matakin da Tinubu ya ɗauka a matsayin tsantsar mugunta tare da fama ciwon da ke cikin zuciyar su, tare da wargaza nasarar da suka samu a kotu a tsawon shekaru.

Dakta Bello, wanda ya taɓa zama Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, ya ce iyalan Bilyaminu sun yi shiru ne kan ibtila’in da ya faɗa masu a ranar Lahadi, 19 ga Nuwamba, 2017, wato ranar da Maryam ta kashe mijin ta, a bisa tunanin kotu za ta yi masu adalci.

Suka ce sun ji daɗin yadda Babbar Kotun Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa a ranar 27 ga Janairu, 2020, kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara da Kotun Ƙoli suka tabbatar da shi a 2020 da 2023.

“Mun gamsu da cewa a ƙarshe an yi adalci a shari’ar, hukuncin da ya kawo ƙarshen maganar…

“Duk da yake wadda ta aikata laifin ba ta nuna wata nadama ba a duk tsawon lokacin da ake lamarin, iyalan mamacin sun haƙura bisa hukuncin da kotuna suka yanke, suka ci gaba da rayuwar su, tare da rungumar ƙaddarar da ta faɗa wa ɗan su.”

Amma iyalan suka ce yafiyar Shugaban Ƙasa, wadda ta haɗa da mutum 175 da aka yafe wa, ciki har da wasu da aka yanke wa hukuncin kisa, ta ragargaza hanyar warkewar da suke a kai kuma ta gurɓata darajar shari’a.

“A ce Wai an bar Maryam Sanda tana yawon ta ba tare da wata tsangwama ba saboda ta’asar da ta tafka, kamar ta kashe kiyashi ne, abu ne mafi ƙasƙanci da za a iya aikata wa kowane iyali saboda wani abin ƙaunar su.”

Iyalin suka ce an nuna masu bambanci a Yafiyar Shugaban Ƙasa, kuma ba komai ba ce illa siyasa ba tare da kula da ƙuncin da aka jefa su a ciki ba.

Sun zargi magoya bayan Maryam Sanda da cewa sun riƙa yaɗa maganganun ƙarya tun lokacin da aka yi kisan, ba tare da kula da rayuwar ‘ya’yan da Maryam da Bilyaminu ba, “don kawai su samu goyon bayan jama’a.”

“Maryam, kada mu manta, da farko ta ƙi amincewa da ‘ya’yan da yanzu kuma take amfani da su don neman a sake ta.”

Suka ce shari’a tana wajen Allah Maɗaukakin Sarki “wanda zai yanke hukunci kan wannan lamari a ranar Gobe Kiyama.”

Tags: Bilyaminu Ahmed BelloDakta Bello Haliru Mohammedkisan gillaMaryam SandaYafiyar Shugaban Ƙasa
Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya taya Ɗanlami Nmodu murnar zama Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Onlayin

Next Post

Cewar Minista: Gwamnati ta saki da naira biliyan 32.9 don inganta kiwon lafiya

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da motocin gas da na lantarki don rage kuɗin sufuri a Kano
Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da motocin gas da na lantarki don rage kuɗin sufuri a Kano

May 15, 2026
Kotu a Amurka ta ɗaure farfesa ‘yar Nijeriya watanni 70 kan satar dala miliyan 1.4
Labarai

Kotu a Amurka ta ɗaure farfesa ‘yar Nijeriya watanni 70 kan satar dala miliyan 1.4

May 14, 2026
EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
Next Post
Cewar Minista: Gwamnati ta saki da naira biliyan 32.9 don inganta kiwon lafiya

Cewar Minista: Gwamnati ta saki da naira biliyan 32.9 don inganta kiwon lafiya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!