• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da motocin gas da na lantarki don rage kuɗin sufuri a Kano

Wakilin Mu by Wakilin Mu
May 15, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da motocin gas da na lantarki don rage kuɗin sufuri a Kano
Motocin safa-safa masu aiki da gas

Motocin safa-safa masu aiki da gas

Gwamnatin Tarayya, ta hannun Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Amfani da Iskar Gas (CNG) da Motocin Lantarki (Pi-CNG & EV), ta ƙaddamar da shirin na shiyyar Arewa a Jihar Kano.

Wannan mataki yana daga ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na samar da sauƙin sufuri ga al’umma da kuma farfaɗo da tattalin arziki.

Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana a taron cewa sauya ababen hawa zuwa masu amfani da iskar gas da motocin lantarki zai taimaka ƙwarai wajen rage kuɗin sufuri, samar da isasshen makamashi, da kuma tabbatar da cigaban tattalin arziki mai ɗorewa.

“Kuɗin sufuri yana shafar komai, farashin abinci, masana’antu, zirga-zirgar kayayyaki, da kuma rayuwar talakan Nijeriya.

“Wannan shiri ba kawai manufar makamashi ba ce; tsari ne na tattalin arziki don bunƙasar ƙasa,” inji shi.

Shettima, wanda Mataimakin Babban Jami’in Ma’aikatan sa (Deputy Chief of Staff), Ibrahim Hassan Haɗeja, ya wakilta a wurin taron, ya ƙara da cewa an zaɓi Kano don ƙaddamar da shirin a Arewa ne saboda matsayin ta na dabarun kasuwanci, kasancewar ta babbar ƙofa ta kasuwanci tsakanin amfanin shiyyar Arewa da maƙwabtan ƙasashe.

Haka kuma ya yaba wa kamfanoni masu zaman kan su kamar Greenville LNG da NIPCO Gas da suka zuba biliyoyin naira a fannin gas, sannan ya bayyana zuba jarin Aliko Ɗangote na sayen dubun-dubatar motocin dakon kaya masu amfani da CNG a matsayin abin a yaba.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana ƙaddamar da shirin a matsayin babban alheri da zai rage kuɗin sufuri kai-tsaye tare da buɗe ƙofofin haɓaka tattalin arziki a jihar.

Yusuf ya jaddada cewa tuni gwamnatin jihar ta haɗa gwiwa da masu zuba jari don faɗaɗa ayyukan samar da ababen hawa na lantarki da na gas, inda aka ba da filaye ga kamfanonin da ke son kafa rassa a Kano.

Ya kuma bayyana cewa shirin zai samar da ayyukan yi ga matasa ta hanyar horar da su fasahar sauya injina zuwa na CNG, gyare-gyare, da harkokin sufuri.

A nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Shirin, Barr. Ismaeel Ahmed, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi umurni na musamman don ya sauya fasalin makamashin gas a arewacin Nijeriya tare da mayar da Kano babbar cibiyar shirin.

Ya ce: “Shugaban Ƙasa ya shaida mini cewa ba ya son a tuna da shi kawai a matsayin shugaban da ya cire tallafin man fetur, a’a, yana son a tuna da shi a matsayin Shugaban Ƙasa da ya samar da madadin mafita mai ɗorewa ga ‘yan Nijeriya.”

Ahmed ya bayyana cewa a cikin watanni takwas kacal, shirin ya kafa tashoshin CNG guda biyar da na LNG guda biyu a Kano, sannan an riga an fito da motoci 40 da babura masu ƙafa uku (daidaita sahu) guda 200.

Ya ƙara da cewa ana shirin tura ƙarin motoci 5,000 da manyan motoci guda 200 zuwa Kano nan ba da daɗewa ba.

A gefen taron, Ahmed ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU) da Bankin Lotus domin samar da tallafin kuɗi na biliyoyin naira don ‘yan kasuwa, masu zuba jari, da masu ababen hawa da ke cikin tsarin CNG.

Previous Post

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi

Next Post

Tinubu ya isa Legas bayan balaguro a ƙasar waje, zai halarci taron fidda gwani na APC ranar Asabar

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Tinubu ya isa Legas bayan balaguro a ƙasar waje, zai halarci taron fidda gwani na APC ranar Asabar

Tinubu ya isa Legas bayan balaguro a ƙasar waje, zai halarci taron fidda gwani na APC ranar Asabar

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!