Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da sakin naira biliyan 32.9 don gudanar da shirin Basic Health Care Provision Fund (BHCPF), wanda zai tallafa wa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin ƙasa baki ɗaya.
Wannan shi ne zagaye na uku na wannan shirin a bana.
Ministan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken Jar Wasiƙa, “The Red Letter”, inda ya jaddada cewa kuɗaɗen sun riga sun fara shiga asusun ajiyar kuɗi na cibiyoyin kiwon lafiya na gundumomi a duk faɗin ƙasar nan.
Pate ya ce wannan mataki yana nufin bai wa al’ummomi ikon tsara yadda za su kashe kuɗaɗen domin tabbatar da cewa kuɗin sun samar da ingantaccen sakamako ga jama’a.
Ya ce gwamnatin ta cika nata alƙawari wajen samar da kuɗaɗen, yanzu al’umma ne ke da haƙƙin tabbatar da cewa an yi amfani da su yadda ya dace.
Ministan ya yi kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya tashi tsaye wajen kare lafiyar jama’a ta hanyar shiga cikin kwamitocin kula da asibitoci, idan an duba yadda ake kashe kuɗaɗen, da kuma tabbatar da gaskiya da bayyananniyar hanya wajen amfani da su.
Ya ƙara da cewa gwamnati tana son ganin wannan saƙo ya isa kowace unguwa, gunduma da gida, don tunatar da ‘yan ƙasa cewa inganta lafiyar Nijeriya abu ne da yake hannun ‘yan Nijeriya.







