• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Ƙasashen Duniya

Ganawa da Guterres: Nijeriya ta jaddada neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 26, 2025
in Ƙasashen Duniya
A A
0
Ganawa da Guterres: Nijeriya ta jaddada neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana gaisawa da Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, a zauren majalisar a New York

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana gaisawa da Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, a zauren majalisar a New York

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya gana da Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, a zauren majalisar da ke birnin New York, inda batun neman kujerar dindindin a kwamitin tsaro ya kasance kan gaba a tattaunawar.

Ganawar ta gudana ne bayan taron babban zauren majalisar karo na 80 (UNGA80), inda Shettima ya gabatar da jawabin ƙasa a madadin Shugaba Bola Tinubu.

Shettima ya jaddada buƙatar majalisar ta ƙara tallafa wa Nijeriya don cimma burin ta, musamman yadda ƙasar ke sha’awar samun kujerar dindindin a kwamitin tsaro.

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya shaida wa manema labarai cewa an tattauna kan cigaban da ake son samu wajen aiwatar da muradun cigaba masu ɗorewa (SDGs), batun sauyin yanayi, da kuma haɗin kai don ƙarfafa dimokiraɗiyya a Nijeriya da yankin Afrika.

Ya ce Guterres ya yaba da rawar da Shettima ya taka wajen jaddada buƙatar Nijeriya ta kujerar dindindin, tare da bayyana irin muhimmancin majalisar a Nijeriya, kasancewar dama ofisoshi da hukumomin majalisar da dama suna aiki a ƙasar.

Batun fasahar zamani da walwalar jama’a:

Ministan Sadarwa da Ƙirƙire-ƙirƙire, Bosun Tijani, ya bayyana cewa Guterres ya nuna farin ciki da nasarar Nijeriya wajen ƙaddamar da samfurin Ƙirƙirar Fasaha mai harsuna da dama (multilingual AI model) na farko a nahiyar Afrika, wanda gwamnati ta tallafa.

A cewar sa, Guterres ya buƙaci Nijeriya ta taimaka wa sauran ƙasashen Afrika don kada a bar nahiyar baya a fannin na’urorin Ƙirƙirarriyar Fasaha.

Shettima yana rubuta sunan sa a littafin maziyartan ofishin Sakatare-Janar Antonio Gutierres

A nasa ɓangaren, Ministan Walwala, Jinƙai da Rage Talauci, Yusuf Sununu, ya ce Shettima ya bayyana ƙoƙarin gwamnatin Tinubu wajen rage talauci da tallafa wa jama’a.

Ya ce gwamnati na da jadawalin al’umma da ta ƙunshi gidaje miliyan 18.9, inda aka riga aka tallafa wa sama da mutane miliyan 8.1 ta hanyar shirin bayar da kuɗin tallafi.

Sununu ya ce an kuma bayyana damuwa kan raguwar tallafin kuɗi daga wasu ƙungiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya, ciki har da shirin WFP wanda ya tallafa wa sama da mutane miliyan 1.3 da kayan abinci.

Tabbacin goyon bayan Majalisa:

Sakataren-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tabbatar wa Nijeriya cewa za ta ci gaba da samun goyon baya wajen ƙara ƙarfin ma’aikatun gwamnati, tabbatar da sahihancin bayanan al’umma, da kuma samun karin tallafi don rage talauci da inganta jin dadin jama’a.

A cewar sa, Guterres ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da gwamnatin Najeriya baki ɗaya kan irin haɗin kai da suke bai wa majalisar.

Tags: António GuterresKashim ShettimaKwamitin TsaroMajalisar Ɗinkin DuniyaUNGA
Previous Post

Nijeriya na so a yafe wa ƙasashen da ake bi bashi tare da ba su damar yin kasuwanci domin samun cigaba mai ɗorewa

Next Post

Tinubu na so jama’a su ƙara haɗa kai yayin da Nijeriya ke cika shekara 65 da zama ’yantacciya

Related Posts

Ƙasashen Duniya

July 3, 2026
Isra’ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran – CNN
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran – CNN

June 5, 2026
Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce
Ƙasashen Duniya

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

April 24, 2026
Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

April 20, 2026
Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa
Ƙasashen Duniya

Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa

April 20, 2026
Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran
Ƙasashen Duniya

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

April 18, 2026
Next Post
Tinubu na so jama’a su ƙara haɗa kai yayin da Nijeriya ke cika shekara 65 da zama ’yantacciya

Tinubu na so jama'a su ƙara haɗa kai yayin da Nijeriya ke cika shekara 65 da zama ’yantacciya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!