• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran – CNN

ALI KANO by ALI KANO
June 5, 2026
in Ƙasashen Duniya
A A
0
Isra’ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran – CNN
Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yana jawabi yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) kan harkokin basirar  zamani (AI) tsakanin Isra’ila da Azerbaijan a ranar 3 ga Fabrairu, 2026.

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yana jawabi yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) kan harkokin basirar  zamani (AI) tsakanin Isra’ila da Azerbaijan a ranar 3 ga Fabrairu, 2026.

Wani rahoto da gidan talbijin na CNN ya watsa a yau Juma’a ya ce ashe Isra’ila ta tura dakarun kwamando da jami’an leƙen asiri zuwa ƙasar Azabaijan domin samun sauƙin kai wa Iran hare-haren a lokacin yaƙin kwanan baya da ta yi wa laƙabi da Operation Roaring Lion.

CNN ta ce wasu majiyoyi biyu sun shaida mata cewa dakarun Isra’ilar sun gudanar da ayyukan su ne daga kudancin Azabaijan, ƙasar da ke maƙwabtaka da arewa-maso-yammacin Iran.

A mafi kusancin da suka yi, an ce dakarun sun kai kusan kilomita 60 daga birnin Tabriz na Iran, wanda rundunar sojin saman Isra’ila ta kai wa hari yayin wannan yaƙi.

Wata majiya ta ce rundunar ta ƙunshi sojoji da dama, ciki har da membobin rundunonin musamman na Isra’ila, da rundunar ceto da ta yaƙi ta hanyar jirage masu saukar ungulu (wadda ake kyautata zaton ita ce Search and Rescue Unit 669), da kuma jami’an hukumar leƙen asiri ta Mossad.

Wasu majiyoyi biyu sun shaida wa CNN cewa waɗannan rundunoni sun gudanar da ayyukan tattara bayanan sirri da kuma sarrafa jirage marasa matuƙa (drones).

Rahoton ya ce tun farko an tura su ne domin su kasance rundunonin ceto idan wani lamari na gaggawa ya taso a cikin Iran, amma daga baya ayyukan su suka faɗaɗa zuwa faɗa tare da tattara bayanan sirri.

Ana zargin su ma Iraƙi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Somaliland sun karɓi sansanonin sirrin Isra’ila

Majiyoyin sun shaida wa CNN cewa wuraren da ke Azabaijan suna daga cikin wasu sansanonin soja na sirri da Isra’ila take amfani da su a ƙasashe daban-daban. Sauran wuraren sun haɗa da ƙasashen Iraƙi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Somaliland.

A cewar rahoton, waɗannan wurare uku sun bai wa Isra’ila damar kasancewa a yankunan kudu, yamma da arewacin Iran a lokaci guda yayin yaƙin, tare da ƙara mata damar kai hare-haren soja daga nisan ɗaruruwan kilomita.

Hakan ya taimaka wa Isra’ila wajen samun sauƙin gudanar da hare-haren soja a zurfin cikin Iran, wadda ita ce ƙasa ta biyu mafi girman faɗin ƙasa a Gabas ta Tsakiya bayan Saudiyya.

Da CNN ta nemi jin ta bakin su, sai kakakin ofishin jakadancin Azabaijan da ke Washington ya yi watsi da rahoton, yana mai cewa suna “ƙin amincewa gaba ɗaya da waɗannan zarge-zargen marasa tushe na cewa an yi amfani da yankin Azabaijan wajen kai hare-hare kan wasu ƙasashe.”

CNN ta kuma nemi ƙarin bayani daga ofishin Firayim Ministan Isra’ila da kuma rundunar soji ta IDF.

Dakarun sashen jirage marasa matuƙa na rundunar Isra’ila (IDF) suna atisaye kusa da iyakar Siriya a yankin Golan Heights na arewa a ranar 26 ga Yuni, 2025.

Mossad, Shin Bet da IDF sun bayyana wata “cibiyar ta’addanci” ta Iran

A ranar 20 ga Afrilu, lokacin da yaƙin ya yi zafi, hukumomin leƙen asiri ta Isra’ila, wato Mossad, da hukumar tsaron cikin gida ta Isra’ila (Shin Bet) da kuma rundunar sojin ƙasar (IDF) sun bayyana cewa sun gano wata “cibiyar ta’addanci” ta Iran da ke aiki a sassa daban-daban na duniya, tana kai hari ga jami’an Isra’ila da kadarorin ta, ciki har da a Azabaijan.

A cewar sanarwar haɗin gwiwar hukumomin tsaron Isra’ila, masu shirya “wannan makirci” daga Iran sun shigar da jirage marasa matuƙa masu ɗauke da abubuwan fashewa zuwa Azabaijan tare da tattara bayanan sirri kan wasu wuraren da ake niyyar kai wa hari.

Rahotannin kafofin watsa labarai na ƙasashen waje sun daɗe suna nuna cewa Isra’ila da Mossad suna da alaƙa mai ƙarfi da Azabaijan, wadda ke da doguwar iyaka da Iran mai sauƙin ƙetarawa. An kuma taɓa zargin cewa wannan iyaka tana daga cikin hanyoyin da jami’an leƙen asirin Isra’ila suke amfani da su wajen shiga Iran.

Kama waɗanda ake zargi da ayyukan ta’addanci a Azabaijan ya taimaka wajen gano sauran membobin cibiyar da kuma masu ba su umurni daga cikin Iran.

(Tare da rahoton The Jerusalem Post)

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yana jawabi yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) kan harkokin basirar  zamani (AI) tsakanin Isra’ila da Azabaijan a ranar 3 ga Fabrairu, 2026.

Dakarun sashen jirage marasa matuƙa na IDF suna atisaye kusa da iyakar Siriya a yankin Golan Heights na arewa a ranar 26 ga Yuni, 2025.

Tags: AzabaijanAzerbaijanIranIsra'ilaleƙen asiriyaƙi
Previous Post

An kusa kammala dokar kafa ’yan sandan jihohi a bisa tsarin mulki — Fadar Shugaban Ƙasa

Next Post

Sabon Kundin Dokokin Canjin Kuɗi: Yadda CBN ke ƙoƙarin hana naira tambotsai a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya 

Related Posts

Ƙasashen Duniya

July 3, 2026
Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce
Ƙasashen Duniya

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

April 24, 2026
Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

April 20, 2026
Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa
Ƙasashen Duniya

Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa

April 20, 2026
Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran
Ƙasashen Duniya

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

April 18, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Ƙasashen Duniya

CBN na shirin kafa kwamitin sulhu don warware rikice-rikicen masu taurin bashi

April 17, 2026
Next Post
Sabon Kundin Dokokin Canjin Kuɗi: Yadda CBN ke ƙoƙarin hana naira tambotsai a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya 

Sabon Kundin Dokokin Canjin Kuɗi: Yadda CBN ke ƙoƙarin hana naira tambotsai a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!