Ministocin Yaɗa Labarai na ƙasashen Afirka sun yi kira da a samar da tsarin sadarwa na bai-ɗaya domin yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya, sake gina amincewar jama’a da kuma ƙarfafa muryar Afirka a duniya.
An yi kiran ne a yau Laraba a Abuja, yayin Taron Hulɗar Jama’a na Duniya na shekarar 2026 (World Public Relations Forum, WPRF).
Ministocin sun kuma ba da shawarar farfaɗo da Taron Shekara-shekara na Ministocin Yaɗa Labarai na Afirka domin inganta haɗin kai da daidaita manufofin sadarwa a faɗin nahiyar.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya ce yawaitar amfani da kafafen sadarwa na zamani da ƙirƙirarrar basira (AI) ya sa ingantacciyar sadarwa ta zama wajibi wajen gudanar da mulki.
Ya yi gargaɗin cewa labaran ƙarya suna iya sauya gaskiyar al’amura, haddasa firgici da raunana amincewar jama’a.
Ya ce: “Fasaha ta zo ta zauna. AI yana nan domin taimaka mana idan muka yi amfani da shi yadda ya kamata. Babban ƙalubalen shi ne tabbatar da cewa labaran da muke yaɗawa sahihai ne kuma gaskiya ne.”
Ya yi kira da a sabunta haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin Afirka, yana mai cewa, “Idan muka haɗa kai, za mu fi ƙarfi. Akwai buƙatar samar da ingantaccen tsari da zai ba mu damar kallon Afirka a matsayin abu guda, tare da sake magana da murya ɗaya.”
Idris ya kuma buƙaci ƙasashen Afirka da su mara wa Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta UNESCO mai mataki na biyu kan Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai da Bayanai (IMILI) da ke Abuja baya, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai na gwamnati domin musayar shirye-shirye da inganta yadda ake bayyana Afirka.
Sakataren Majalisar Ministocin Kenya mai kula da Yaɗa Labarai, Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, William Kabogo Gitau, ya yi kira da a ƙarfafa ƙa’idojin sana’a a fannin hulɗar jama’a da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe domin yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya.
Ya jaddada cewa daidaito a saƙonnin gwamnati yana da muhimmanci wajen gina amincewar jama’a.
“Ana gina amincewa tsakanin gwamnati da ’yan ƙasar ta ne ta hanyar hulɗar yau da kullum: amsa tambaya da sahihin bayani, isar da hidima kamar yadda aka yi alƙawari, da kuma isar da saƙo iri ɗaya daga kowane ɓangare na ƙasa. Gwamnati ɗaya, saƙo ɗaya,” inji Kabogo.
Ministan Sadarwa da Kafafen Yaɗa Labarai na Jamhuriyar Kongo, Thierry Lézin Moungalla, ya ba da shawarar gudanar da shawarwari tsakanin ministoci a kai a kai, horas da ma’aikata, haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai na gwamnati da masu zaman kan su, da kuma samar da shirye-shirye tare.
Ya ce dole ne a shigar da sadarwar gwamnati cikin tsarin gudanar da mulki.
“Sadarwar gwamnati ba ta tsaya kawai ga aikin hulɗa da jama’a ba. Dole ne ta kasance wani muhimmin ɓangare na dabarun gwamnati da tsarin gudanar da harkokin ta,” inji Moungalla.
Mataimakin Ministan Yaɗa Labarai, Wayar da Kai da Ayyukan Gidajen Rediyo da Talbijin na ƙasar Zimbabwe, Omphile Marupi, ya jaddada muhimmancin ilimin kafafen yaɗa labarai, aikin jarida bisa ƙa’idojin sana’a da kuma sadarwa a matakin al’umma.
Ya buƙaci gwamnatoci da su riƙa sauraron jama’a tare da amsa buƙatun su.
“Dole ne mu yi sadarwa ba don a ji mu kawai ba, har ma don a fahimce mu. Bai kamata mu tsaya kawai ga yaɗa labarai ba; dole ne mu saurari al’ummar mu, mu yi hulɗa da su, sannan mu amsa abubuwan da ke damun su,” inji Marupi.
Ɗan majalisar dokokin Ghana kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Sadarwa na majalisar, Abed-Nego Lamangin Bandim, ya yi kira da a ƙara kuɗaɗen da ake ware wa fannin sadarwar gwamnati tare da inganta tallafin da ake bai wa ’yan jarida.
Ya bayyana cewa Ghana ta ware cedi miliyan 10 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2027 domin horas da ’yan jarida, bunƙasa ƙwarewar su da inganta walwalar su.
An kammala taron ne da ƙudirin ƙarfafa haɗin gwiwar sadarwa a faɗin Afirka, inda Nijeriya ta bayyana shirin ta na karɓar baƙuncin taro na gaba na Ministocin Yaɗa Labarai na Afirka.






